← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 241 OF 267

Sashe 241

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har suka kwanta Humaira na lura da yanayinsa dukda yanda yake ta qoqarin kawar da komai amma seda ta fahimci wani abu tayi kwanciyarta ta barshi a zaune yana danne dannen laptop data tabbatar babu abinda yakeyi kawai dan ya dauke hankalinta ta zata aiki yakeyi ne dan haka tayi baccinta ta barshi.
Khalil kuwa tambaya ce baya so tayi masa dan besan amsar da ze bata ba gaba daya ganin Umaiman ya haifar masa da wani yanayi mara dadi, juyi yayi tayi akan Gadon tunani kala kala suna yawo a kwakwalwarsa daya gaji gashi ya kasa bacci ya tashi ya dauro Alwala ya fara sallah har seda yaji ya fara jin bacci kafin ya sallame yayi addu'a ya kwanta. Abinda be tabayi ba tsahon lokacin rabuwarsu se gashi daren yayi mafarki da ita cikin wani yanayi me firgitarwa dan tana daure da sarqoqi wani mutum yana janta tana miqa masa hannu tana kuka akan yazo ya ceceta yayi yunqurin miqa mata nasa hannu wani haske me tsananin kaifi ya kashe masa ido har ya hanashi sake hangota se amsa kuwwar Kukanta yake ji a kunnensa tana fadin
"Khalil ka taimakamun ka gaya musu ban aikata ba".

A gigice ya farka daga baccin yana salati ya kalli Humaira data miqe zaune itama tana kallon cikin wani yanayi, tana bacci taji ya kama hannunta da matuqar qarfi yana kiran Umaimah da har seda ta farka sedai yanayin data ganshi ta tabbatar koda mafarkin Umaiman yayi tofa bame dadi bane. Addu'a ta ringa tofa masa kamar yanda shima yake tayi zufa na keto masa kamar babu Sanyin Ac a dakin ga jikinsa na rawa yanda kasanwanda aka rutsa da wuqa a mafarkin. Seda suka kwashi wasu mintuna a haka kafin ya daidaita nutsuwarsa ya koma ya kwanta tareda janta jikinsa ta zame be takura mata ba ya saketa dan har sannan bawai jikinsa ya gama daidaita bane

Humaira ko tsaki taja a zuciyarta ta juya masa baya babu bata lokaci kuwa bacci yayi awon gaba da ita shi kuwa haka ya ringa juyi ya gagara komawa baccin har aka kira sallar Asuba kafin ya tashi yayi wanka ya fita masallaci. Kwanaki biyu da suka biyo baya duk haka yayi su sukuku shi kansa bazece ga abinda yake damunsa ba amma jikinsa gaba daya babu qarfi, da Hajiya ta matsa masa da tambayar me yake damunsa ne dole ya qarfafa jikinsa ya koma sabgoginsa daman Humaira koda wasa bata ma nuna masa ma tasan abinda yakeyi ba, daya ware dinma shareshi ta ringayo seda yayi ta rara gefe yana lallashinta kafin ta sakko suka koma daidai amma qasan ranta danuwa ce fal akan abubuwan da taga suna faruwa. Haka rayuwa taci gaba da gangarawa, seda cikinta ya shiga wata shida kafin mutane suka farga dashi.

Ranar da Hajiya ta gama tabbatar da cewar cikine har kuka tayi tasa aka dafa abinci me yawa aka fita dashi akayi sadaka, Khalil kp kasa hada ido yayi da ita a dole kunya yake ji ita kuwa ko a jikinta ta ringa bige bigen waya tana shaidawa yan uwanta da abokanan Arziqi matar Khalil nada ciki yanda kasan be taba haihuwa ba sedai duk wanda ta gayawa yasan me take nufi, shaida musu takeyi Khalil din ya samu lafiya sun kuwa taya su murna tareda fatan Alkhairi kafin tofin Alatsine ya biyo baya akan Umaimah datayi masa sanin wannan tonon silili. Hajiya Hauwa kanta barka suka ringayiwa Juna ita da Hajiyan, tace mata
'Kinsan ta da zurfin ciki, tun kwanaki nale hasashen cikin amma tace na haka ba to tunda kasan ga yanda abu yake kinga ba zaka matsanta ba ashe iyashege ne kawai irin nata yanzu da baze boyu ba ai kowa ya sani Allah ya inganta shi kuma ya bashi lafiya me dorewa".

Jalilah kuwa ta samu abin yi, daga shi har Humairan bata bari ba dukda yanda take bala'in jin kunyarta amma idan ta tasata a gaba da tsokana seta kusa kuka take qylaeta, saboda ta samu iya shege ma cewa tayi ta haqura ita ce Hussaina yanzu shi ya zama Hassan din dan haka yanzu a qanwar Miji take dole ta tsonaketa
"Haba nidai nace ashe su Khalil anji garau an shiyasa ko gidan nan aka zo ba'a jinku kunyi muqus a daki ana biyan bashi, dan Allah tun yaushe ka koma duty?" A gaban Hajiya tayi masa tambayar yanda kasan qasa ta tsage ya shige cikinta Hajiyar kanta seda ta dafa kai tana jinjina hali irin na Jalilah, bata haqura ba taci gaba da zaro zance dayaga babu sarki se Allah dole ya shafawa idonsa toka ya mata ta yan barikin shima yace mata
"Kedai ki bari shekara uku ai ba nan bace nida ita duk munji jiki yanzu kuwa da lafiya ta samu ai dole mu biya bashi " Hajiya dai se tashi tayi ta barsu dan ba zata iya da wannan fitsara ta tagwayen nata ba.

BAYAN WANI LOKACI
Misalin qarfe goma na safe suka fito shida Humairan da ze sauke a Asibiti zataje Awo, dakyar take daga qafarta saboda yanda cikin me watanni takwas a sannan yayi girma sosai dan yafi na Aryaan, fuskarta a hade ta shiga motar haka shima tashi dukda shi yana qoqarin hadiye bacin ransa dayi mata uzuri akan abinda take masa. Tagiya sukeyi babu me tanka dan uwansa ta juyar da fuska tana kallon waje lokaci lokaci yake waiwayawa ya kalleta Ya rasa abinda yake damun Humairan kusan wata biyu kenan ta canza gaba daya daga yanda ya santa a kullum cikin takalar rigimarsa takeyi abu kadan kuma zeyi mata ta hau fushi da koke koke ya rasa inda ze tsoma ransa ta kasa yi masa uzuri akan abinda shi kansa yana damunsa, a yanzu data rigada tasan dadin jikinta a kullum cikin zuwar masa da buqata takeyi wadda yake gaza biya mata, ya lura ta raina qoqarinsa dukda cewar Abubuwa sun qara daidaitar masa dan a yanzu yana iya takarta amma bayayin dogon zango, abinda ya lura dashi ita kuma halittarta me zurfi ce tana daukan lokaci kafin ta samu gamsuwa duk kuma yanda ya sabayi mata yanzun baya wadatarta tafi so yayi mu'amala ta gaske da ita duk kuma da qoqarin da yakeyi dan lokaci da yawa bayan sun gama hala zeyi ta murqususun ciwon Mara a maimakon ta yaba masa sedai tayi ta bata rai yinin ranar kuwa zir haka zasuyi cikin qunci daga shi har ita dan baya taba iya walwala idan batayi ba.

Sau da yawa yakan zaunar da ita yayi qoqarin fahimtar da ita amma setaqi qarshe ko tasa masa kuka ko tayi shiru har ya gaji da magana yayi shiru, be san me take tunani ba gani takeyi shine baya so yayi mata yanda take ko yaya sam shi be fahimta ba yanzu da safen ma rigimar da suka tashi da ita kenan, har yayi wanka yana shiryawa ta shige masa jiki, yasan me take so a lokacin kuma bashi da sha'awar hakan a tattare dashi amma gudun shiga haqqi dole yayi mata yanda take so, haka kawai yama jikinta ta tureshi, cikin fushi take ce masa
"Daman an fada idan Namiji baya son mace ko burgeshi batayi, inda wacce kake so ce ba rashin lafiya ba koma menene zakayi mata yanda take so ai" ta shige bandaki ta barshi cikin tsananin mamakinta. Ransa ya ringa baci zuciya tana harzuqo masa, ba yau din ta fara fada masa haka ba duk ranar da Yara suka ambaci Mamansu taga wani sauyin yanayi a tattare dashi ta ringa yada masa da magana kenan akan saboda an tuna masa da wadda yake so zeyita daure fuska yana fushi a gidanamma be taba daga kai ya kalleta ba shine yau zata kafa hujja akan abinda ba haka yake ba shi yaushe rabonsa da ko a tunani ya tuna da wata Umaimah?

Idan ba Bibi ta tada rigimar zata gurinta ba wlh shi mantawa yakeyi da ita amma ota Humairan ya fahimci ta tsaya mata a zuciya tana yawan son kawo zancenta ya kuma zaunar da ita ya nuna mata baya so amma ya lura duk in tana so ta bata masa rai ne take ambato Umaiman. Haka yayi wanka suka fito, yana yai mata uzuri ne da cikin jikinta shi kansa yana iya qara mata fitina da neman rigimar da takeyi yana kuma fatan idan Allah ya sauketa lafiya ta canza karta ce zasu ci gaba da rayuwa hakan dan zaman baze musu dadi ba idan har zata cigaba da quntata zuciyarta tana quntata shi. Tun farkon daya gamu da ibtila'in irin abubuwan daya ringa hangowa kenan har yayi tunanin sawwaqe mata amma tace taji ta gani zata zauna dashi se yanzu kuma data gama mamaye zuciyarsa sannan zata tsiro da wasu baqin halaye na daban gaskiya baze dauka ba.

Seda ya jirata ta gama abinda zatayi a Asibitin saboda ya Driver yara ya tafi kai Hajiya Gaya gaisuwar rasuwa, sun fito daga office din Dr Al'amin suka wuce pharmacy zasu karbi magungunan Awo, yana gaban me bada maganin tana daga can bayansa ya juya da niyyar ya tambayeta idan tana da sauran Paracetamol ko a hada musu dashi idonsa yayi kyakykyawan ganinta da wani Dogon saurayi fari suna dariya. Kallon saurayin ya ringayi yana qoqarin tuna inda ya sanshi take ya gano wanene wani kalar tashin hankali ya rufto masa daga inda yake yana jin muryarta tana fadin
"Nuru kaine ka zama haka?" Ta sake fada cikin madaukakin farin ciki tamkar yanda Noor din dake tsaye gabanta da rigar Lab coat shima fuskar sa ta nuna farin cikin ganinta.
"Nine, Ashanty, oh my God look at you kin zama wata big Mama dake, but wait ya naganki heavenly pregnant While naji ance Mijinki ya zama mace? Ina ta neman contact dinki nayi miki jaje duk wanda na tambaya seya hanani bayan kuma dai ai ko babu SO yanzu tsakaninmu akwai zumunchi dukda ni har abada bazab dena sonki ba" Noor ya sake fada yana qarashewa da wata kalar dariyar shaqiyanci take murmushin kan fuskarta ya dauke ta kalli bangaren da Khalil yake tsaye suka hada ido ya saki ledar magungunan hannunsa saboda yanda qirjinsa ya shiga bugawa da qarfi cikin dabarbarcewa ta kalli Noor din tace
Chapter 241 · 0% Book details