Sashe 130
Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Qarar horn da suka jiyo ya saka shi shiga dakinsa da sauri ya fito da pistol guda biyu yana soke su a jikinsa.
"Abban Nu'aima wai aikin me zaku fita ne kace mun yanzu zaka dawo ammana ganka harda bindiga" Anty Mami ta fada cikin tashin hankali dan a duniya babu abinda ke tsorata ta irin taga ze fita operation da bindiga tasan gurin da ze shiga me hatsarine hankalin kuma baya kwanciya se taga ya dawo gida.
"Yanzu zan dawo in sha Allah Mamy ki kula da yara ki gaya musu Dady na sonsu" ya fada yana rungumeta lokacin da aka sake danna horn din da qarfi ya saketa yana cewa su Khalil
"Dare yayi ku tafi gida kunsan fa yanzu garin se a hankali ba'a son kaiwa dare a waje".
Tare suka fito har ya shiga mota Umaimah ta tuna da saqon mama ta zura dagudu tana tsayar dasu, wayar ya zaro ya duba yana ce mata zan kirata ina shiryawa sanda ta kira shiyasa banji ba" Driver yaja mota suka bar gurin da sauri dan sun kusa missing target din an sanar musu yana shirin barin gurin.
Umaimah shiru tayi batacewa Khalil komai ba ganin ba hanyar gida ya dauka ba. A laundry din da yake kai wanki suka tsayaya shiga, be jima sosai ba ya fito yaran gurin na binsa da ledojin da aka sako masa kayan wankinsa ya bude musu back sit suka zuba kafin ya zaro dubu biyu ya basu su biyun suka karba suna masa godiya ya shiga motar.
Sesa suka kusa shiga gida shi ya tuna basu da bread dan haka ya nemi wani gurin da ake siyarwa ya tsaya.
Wayar Khalil din daya bari a mota ce ta dauki qara, kamar ita aka kira tayi zuruf ta daga tana fatan wata me tsautsayin ce ta kirashi sedai ganin sunan 'Dr Sagir' data tabbata Mijij Nuratu ne ya bata mamaki kiran me zeyiwa Khalil a daren nan?
Wayar ta katse ya sake kira ganin Khalil din ya tsaya dan da akwai me siyar da Nama a gefe da alama shi ya tsaya karba yasa ta daga
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Khalil kun koma gida kaji abinda ya faru ko? Ance kune baqinsa na qarshe Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Dr Sagir ya fada a rikice
"Meya faru, meya samu Yaya Aminu?" Umaimah ta fada cikin wani yanayi dan dai a kalaman Sagir tasan shi yake nufi, gidansa kadai sukaje se Lundary da suka tsaya karban wanki kuma sune na qarshe da ya gani a gabansu ya fita ta tabbata akansa yake magana.
Qit Sagir ya kashe wayar jin muryar Umaimah, qoqarin kira ta shiyayi rawar da hannunta yake ya sa ta kasa bude wayar daidai nan Khalil ya bude motar da sauri saboda hango wayarsa a hannun Umaimah da yayi, baya son wani sabon tashin hankalin shiyasa ko kayan be karba ba ya taho seta miqa masa wayar tana cewa
"Ka kira Sagir ya gaya maka waye ya Mutu, wayyo Allah na shiga uku" ta qarasa tana dora hannu biyu a kai da fasa ihu.
"Ke meye haka? Wazan kira?" Ya fada yana duba wayar ganin Sagir ne kiran qarshe yasa yabi bayansa. Salati ya ringa ja yana maimaitawa jikinsa yayi wani mugun sanyi haka yazare wayar daga kunnensa ya kasa juyawa ya kalli Umaimah da yanayinsa ya tabbatar mata dagske Yaya Aminun ya mutu. Ihu ta shiga rusa masa ya yi shiru dan besan yanda ze rarrashe taba, shi kansa mutuwar ta dake shi yanzu fa, yanzun nan ko minti Ashirin cikakku basuyi da rabuwa ba ashe fitar Ajalice, saurinda yakeyi na ya taradda Ajalinsa ne.
Komawa yayi gurin masu bread da nama yace suyi sadaka dashi kafin yaja motar suka wuce gidan su Umaiman.
Fadar kalar tashin hankalin da suka tarar bata baki ne, yanda gidan ya cika da Mata ba zakace dare bane har mamakine ya kama Khalil na yanda akayi labarin mutuwar tasa ya bazu cikin dan lokaci idan ya duba taqin rabuwarsu to yaushe har ya rasun?
A bakin Baba Abdullahi da suke shirin tafiya Asibiti karbo gawar yake jin wai ashe wanda sukaje kamawa sun samu labarin zuwansu, a cikinsu aka samu wani ya ha'incesu ya sanar masa dan haka sukayi musu qofar rago suna shiga gurin sukayi surrender suna qoqarin saka musu Handcuffs akayi attacking nasu se jin harbi kawai sukayi ta ko ina, su takwas uku sun rasu a take harda Yaya Aminun Biyar suna Asibiti.
Allah sarki rayuwa mai rai na tafe Ajalinsa na binsa a baya be sani ba haka a daren nan aka kawo gawar Yaya Aminu daya fita daga gida cike da burika kala kala ba tareda yasan yayi fitar da baze dawo bane. Fadar irin tashin hankalin da Iyalan gidan suka shiga bata bakine, Daga dare zuwa safiya Suman Mama biyu, Mamy matarsa ko tunda ta zube ba'a sake jij bakinta ba har seda safe da aka zo fita da gawarsa sannan ta sake fasa wani ihu ta zube sumammiya a gurin dole aka hada ita da Mama da Jininta ya haye akayi Asibiti dasu Abba kansa daga maqabarta Asibitin aka wuce dashi saboda yanda Numfashinsa keta hawa da sauka har ana ganin dagawar qirjinsa gashi ya kasa magana toh ya za'ayi? Allahn daya fisu son Aminu ya karbi abinsa ba tareda yayi shawara da kowa ba sedai a bishi da fatan samun dacewa kamar yansa ya samu kykykyawar shaida daga bakin jama'ar unguwa da Abokan aikinsa. Sun bada shaidar mutum ne me Amana ba kuma ya karbar cin hanci haka mai laigi duk daurin gindinsa idan aka sakashi akan case seya tsaya iya yinsa yayi ansha kaiwa rayuwar sa Hari Ubangiji na tseratar dashi se yanzu da tafiyar tazo babu wanda kuma ya isa ya dakatar da ita.
Rasuwar Yaya Aminu ta sake maida kowa na gidan cikin hayyacinsa musamman Umaimah da wasiyyar da yayi mata ta qarshe ta samu guri radam ta zauna a kwakwalwarta, damanya fada wata rana baya nan bare akai masa qararta gashi kuwa ashe abinbada nisa bane yanzu sedai su tunashi su sakashi a Addu'a Allah sarki Anty Mamy ta shiga sahun su Anty Hafsa Allah ya daga musu. Wannan rasuwa ta sakata watsar da makaman yaqi sabon gidanma gaba daya ji tayi ya fita a ranta qila ma duk haqilon da takeyi ta mutu kafin a tare ko idan an shiga ba zata dade ba zata mutu. Ranar da tayi tunanin idan ta mutu Khalil wata ze auro kwana tayi tana kuka har abin ya bashi tsoro ya rinfa tofa mata Addu'a da farko duk a zatonsa Yaya Aminu ta tuno amma se yaga ta kalle shi seta rushe da kuka se kuma ya fara tunanin ko shima mutuwar zeyi ne ta fara Alhini?
Alwala ya dauro ya fara jera salloli, idan ma mutuwar zeyi ya mutu yana sallah haka suka kwana ita kuka shi sallah.
Bayan wasu watanni
Yaya Khalil, bari naje na kaiwa Hajiya abin nan" Umaimah dake tsaye akansa ta sako wani uban zumbulelen Hijabi ta fada. Khalil ya zare Glass din dake idonsa kafin ya ture takarddun gabansa ya nuna mata kan cinyarsa yana cewa
"Bazaki dena cemun Yaya Khalil bako? Gashi nan kin koyawa su Bibi sun deba Dady se wani Yaya zan saba miki fa" ya qarasa yana jan hancinta daya fara budewa. Yar qara ta saki kafin tace
"Toh za'a dena, suma zan hanasu fada"
"Yawwa ko kefa, me zaki kaiwa Hajiyar?" Ya fada yana qoqarin bude kwanan hannunta ta qanqame tana cewa
"Bazaka gani ba"
"Wai dagaske kike matar nan rowa zaki mun ko kadan bazaki sammun ba?" Ya fada sanda yayi nasarar bude kwanon ya debi dambun naman dake ciki ya zuba a baki yana taunawa yana lumshe ido. Bubbuga qafa ta shigayi da kuka qarya wai seya biyata, kwanon ya karbe ya sake dibar wani ya watsa kafin ya ajiye gefe yana cewa
"Zo na biyaki toh, ai abun bana rigima bane".
Bakinsu ya hade ya shiga kissing nata passionately, seda suka kwashi kusan minti goma kafin Umaimah tayi saurin janye jikinta jin Alamun ana hawowa saman da gudu. Tana zama kusadashi kuwa Mu'ayyad ya fado da gudu yana sallama Bibi a bayansa tana kuka da yar tsanarta a hannu babu kai"
Jikin Umaimah ya fada ita kuma ta wuce gurin Khalil ya riqeta yana cewa
"Meye haka, me kayiwa Mamana take kuka?" se ta sake fashewa da kuka cikin magarta da bata gama nuna ba ta nunawa Khalil din kan yar babynta tana cewa
"Yaya ya kace ta, ya ciye mata kai".
"Lalala baka kyauta ba Yaya, ya zaka kashe mata Babynta ka cire mata kai? Kyaleshi kinji Mamana an jima zamuje mu siyo wata babba maza share hawayenki" saurin goge fuskarta ta shigayi jin za'a siya mata wata ta dane cinyar Khalil din tana qoqarin taba takaddun zanen dake gabansa ya janye su yana cewa Umaimah
"Kije dasu dan Allah na samu na qarasa aikin nan yau"
"Uhm kafi sati kullum haka kake cewa yau zaka gama, ni na fara gajiya da wannan aikin me cinyewa mutane lokacinsu" ta fada tana zumbura baki, seya daga wata takadda ya nuna mata yana cikin tsokana yake cewa
"1 Billion contract ake gaya miki yarinya, kedai kiyita salati kina mana addu'a idan harkar nan ta fada ai ke kanki zaki sha mai Hajiyata"
"Toh Allah yasa" ta fada tana miqewa ta bawa Mu'ayyad kwanon ita kuma ta kama hannun Bibi suka fita ya bita da kallo yana wa tafiyarta data fara canzawa kallo. Watanninsu Shida da tarewa a Sabon gida kuma watannin cikinta tsarabar Sabon gida. An tare lafiya kuma tun sannan zaman lafiya ya sake jaddaduwa a gidan idan ka cire qananan sabani da kowanne gidan aure ake samun su musamman ma da akayi katari da Khalil din me dauke kaine abinda yake qarawa zaman nasu Armashi kenan dan ko tsiyatakunta sonso motsawa baya kulata yanzu.