← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 267

Sashe 66

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wallahi Mama qawata ce ta ara kuma sun tafi America da Mijinta se qarshen watan nan zasu dawo nasan idan na gaya miki fada zakiyi amma akwai tata a gurina kuma tafi tawa tsada na sani" Umaimah ta fada tana janyo qaramin Kit din kayansu ta bude, Sarqar Maman Nihal ta dakko ta miqawa Mama ta karba tana cewa
"Wace qawar taki, Rumasa'u ko Halima?"

Seda ta kalli Khalil da mamakinta ya hanashi magana kafin cikin rashin gaskiya tace
"Maman Nihal, baki santa ba"
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, wace shegiyar barauniyar kika bawa sarqarki ta baki ajiyar wannan?" Mama ta fada cikin jimami tana daga barawon gwal din da Maman Nihal ta bawa Umaimah a matsayin zinaren gaske.

"Barauniya kuma Mama, baki ga girmansa ba yafi nawa ko? Tace nawan yana nan gidanta a Janbulo ta barwa Driversu ya kawo mun, idan ma baki yarda ba kawai ko siyar dashi ma za'a iyayi in dauki kudin nawa in tura mata sauran idan yaso ta riqe wancan dan inata nemanta a waya bana samunta har a WhatsApp kamar ma ta canza lamba ne ban sani ba" Umaimah ta fada, se Mama ta wullo mata qwandalelen kwadon sarqar ya same ta kuwa a goshi ta dafe tana cewa

"Kai Mama daya sameni a ido fa?"
"Ai gara ya sameki a idon yar banza mara hankali, banda kwakwalwar kifi ce dake wannan yayi miki kama da zinare? In banda hauka da rashin sanin ciwon kai a ina kika hadu da matar dan ni ban taba jin sunanta ma a gidan nan ba shine zaki dauki sarqar kusan miliyan biyu ki bata tunda bada guminki aka siyo ba, to zaku ci ubanku daga ke har ita ba America ba ko bangon duniya ta tafi seta fito dashi, ina kinsan gidanta tashi maza maza yanzu zamuje duk wadda za'ayi ayita a daren nan tashi muje" Mama ta fada tana miqewa se a sannan Khalil ya iya bude baki yace

"Mama ayi haquri yanzu dare yayi zuwa da safe idan Allah ya kaimu se aje tunda tace ta san gidan matar, ni daman tun asali mu'amalar su batayi mun ba saboda yanda matar sam bata da sirri komai ya seta fada"
Umaimah ta harareshi Mama tace

"Khalil gara muje tun yanzu dan jikina ma baya bani za'a samu sarqar nan amma dukda haka muje mu kama barauniyar zaune dan kwandala bazatayi ciwo ba idan babu sarqa seta bada kudinta"

"Wai dan Allah waya ce guduwa tayi matar da tafi qarfin dan wannan abin shine duk za'a ringa wani tashin hankali kuma wannan Mama idan baki yadda me kyau bane a kaiwa Bashir mana ya auna a gani" Umaimah ta fada tana zumbura baki Mama ta kai mata mari tana gocewa tace

"Wallahi sena bata miki rai idan baki rufemun baki ba sakarya da bata da tunani, idan rashin mutunci ne da tsiya kala kala babu wadda baki iya ba amma kwakwalwarki sam bata aiki balle tayi tsinkaye, yanzu zamuje idan kuma qarya kikeyi mata dan ubanki duk idan munje maji yanda akayi".

Mama ta dage akan adaren nan qarfe kusan goma za'a tafi idan Maman Nihal dakyar Anty da ta shiga itama suka hadu da Khalil suka lallabata ta bari seda safe, washe gari kuwa qarfe takwas bata cika ba Mama ta tasa Umaimah a gaba suka tafi gidan Maman Nihal Salman ya kaisu dan Mu'ayyad ma a gurin Anty suka barshi yana bacci.

A bakin babban Get din gidan salman ya faka mota, Megadin dake sanye da Uniform ya fito suka gaisa yana tambayarsa gurin wa suka zo haka Umaimah tace gurin Maman Nihal,
"Amma bakusan dokar gidan nan se Hajiya ta bada umarni daga ciki baqo yake shiga musamma ma ku da kuka dako wannan sammakon, ku kirata a waya, zata bamu unarni idan tace a barku ku shiga toh" Me gadi ya fada musu kafin ya koma can bakin qofa inda sauran yan uwansa masu gadi suke.

"Se ki kirata, gadai gida nan har gida amma matar ciki yar damfara" Mama ta fada tana hararar Get din kamar shine Maman Nihal, Umaimah ta kira layin kamar kullum dai a kashe ta kalli Mama kamar zatayi kuka tace
"A kashe take Mama, dan Allah kiyi haquri mu koma gida nasan ba guduwa tayi ba gadai gidanta kin gani idan lokacin da tace zasu dawo yayi bata dawo mun dashi ba sannan se a dauki kowanne mataki"

"Karki fita kisan yanda zakiyi su bude miki get din" Mama ta fada ba tareda ta kalleta ba, haka Umaimah ta fita daga motar kamar zata rusa kuka daidai sanda aka bude Get din mota ta fito, ta gane driver wanda Walid shine ya dakkota wancan karon da tazo ga su Nihal a baya da uniform ze kaisu makarantaya tsaya dan ya gane ta shima, Niihal ta leqo tana dagawa Umaimah hannu itama ta daga mata ta qarasa jikin motar Nihal din ta gaisheta

"Mamanku tana ciki?" Umaimah ta tambayeta ta daga mata kai, seta maida kallonta kan Driver tace
"Inata kiran wayar Mamansu bata shiga Me gadi kuma yace se na kira ta bada umarni ze barmu mu shiga". Shi yayiwa masu gadin magana suka bude musu shi kuma ya wuce kai yaran makaranta.

A palour na farko akayi iso, Mama tabi palour da kallo tana tabe baki kusan minti goma sha biyar sannan Maman Nihal ta shigo palour da sallama ciki ciki kamar wadda akayiwa dole jikinta sanye da kayan bacci alamar tashinta kenan.

Kallon Umaimah tayi da mamaki kamar yanda itama take kallo ta, cikin muryar isa tace
"Baiwar Allah lafiya, ko kinyi mantuwa ne a gidan nan?" Maman Nihal ta fada tana kallon Umaimh,
"Saqon na da Maman Nihal ta bari nazo karba" Umaimah ta bata amsa kai tsaye, seta kalleta irin kallon bangane abinda kike nufi ba Mama da gaba daya haushin matar ya cikata bama itace Maman Nihal din ba kenan ta harareta tace

"Sarqa da Maman Nihal ta ara a gurinta tace ta barta a nan ita muka zo karba"

"Ban gane me kuke magana ba akai Hajiya nice Maman Nihal ko wata daban kuke magana a kai, kedai na ganeki kece qawar Abu da kika zo kwanaki lokacin kamar kinada tsohon ciki koh" Matar ta fada tana kallon Umaimah, se Mama da Umaimah suka kalli juna jin wata sabuwa kuma,

Itace Maman Nihal, wace ce kuma Abu da take fada???

*SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS*

*Shin yar uwa kina da wata matsala ce data shafi zamantakewar aure da kika kasa gane kanta? Ko kuwa a bangaren megida ne Al'amura basa tafiyar miki daidai yanda kike so*

*Qaiqayin gaba, farin ruwa ko ruwa me qarni yana fitar miki kinje Asibiti kinsha magani har yanzu ba'a dace ba? Ko kuwa kin kasa gane kan mu'amalar auratayya bakyajin dadi ko kina jin zafi a lokacin saduwa*
*Aa damuwarki inda zaki samu ingantattun magungunan mata marasa illah wadanda masana ilimin suka hada ba yan taka haye to ki garzayo nan domin muna da maganin matsalolinki da yardar Allah*

*A Sumayyas_herbal_aprodiasics* *muna bada ingantattun magunguna wadanda masana sukayi bincike suka tabbatar da suna samar da waraka ga dukkan matsalolin da kuka zo dasu*
*Muna da maganin sanyi ko wanne iri da yardar Allah zamu baki bayan munyi miki tambayoyi domin sanin yanayin lakurarki*
*A bangaren kayan gyara muna da ingantattun tsumi, Gumba, Kaza/ciccibi, Sabaya na gyaran Nono, maganin qiba dana rage qiba ingantattu da babu kwaya a cikinsu*
*Sannan munada tsari na tattaunawa da mata domib musan matsalolinku mu kuma baku shawarar yanda zaku magance su da yardar Allah*
*Adreshin mu Zaria/Abuja muna kuma aika kaya ko ina a fadin qasarnan cikin Amincin Allah kutuntube mu akan*
*07031876677*
Ko a IG *sumayyas_herbal_aphrodisiacs*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

Page 30

Wayarta ta danna alamar kira bayan an daga tace
"Walid idan ka dawo ga baqi nan a palour ka kaisu gidan Abu" tana gama magana ta miqe ta kalle su tace

"Za'a raka ku gidanta yanzu"
"Ban gane za'a raka mu gidanta na ita wa kuma ke din wacece?" Mama ta fada tana miqewa tsaye itama ganin Maman Nihal din ta juya, seta kalli Mama tace
"Ita wadda kuke nema din nan ba gidanta bane, kuma ba wannan ne karo na farko da tayi qarya da sunana ko gidana ba amma wannan ne na qarshe, kuje can ku warware matsalarku ni ban san komai a kai ba" tana gama fadan haka ta juya ta barsu a palour.

Mama ta tafa hannaye tana salati Umaimah dai tagumi ta buga to idan Maman Nihal qarya take yi wanne irin kusanci ne da ita da wannan matar to da har ta bata damar shiga gidanta tayi abinda take so kamar matar gidan. Zuwan Walid ya sakasu tashi suka fita, a motar da suka zo suka dunguma gaba daya Walid na gaba yanayiwa Salman kwatance tiryen tiryen har suka isa Unguwar Hausawa ya nuna musu wani gida ginin bulo ne amma babu fulasta ta wajen yace musu nan ne daga nan yayi musu sallama ze juya Mama ta dakatar dashi tace

"Ina zakaje, ai se mun shiga mun tabbatar ita dince ka kawo mu gurinta kafin ka bar nan dan bangama yarda daku ba"
"Walid yayi murmushi ya qarasa soron gidan suna biye dashi daidai sannan wata yarinya da bazata haura shekaru goma ba ta fito daga gidan, cikin fara'a ta gaida Walid ya tambayeta Mamansu tana ciki tace eh ta juya tana cewa
"Bari na gaya mata kazo" ya dakatar da ita da cewa
"Aa wuce aikenki Amina baqi na rako zasu shiga ciki" seta wuce abinta. Umaimah ya kalla yace

"Yanzu kin yarda ko kuwa" ta daga masa kai alamar Eh saboda tun ganin yarinyar kamanninta da Maman Nihal din suka tabbatar mata dan haka yayi musu sallama ya tafi.
Chapter 66 · 0% Book details