← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 267

Sashe 131

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A bangaren Alaqarta da Hajiya kuwa se abinda ya qaru saboda qaruwar kusancinsu yasa ta sake siye zuciyar Hajiyan da mugun ladabi da biyayya. Kusan koda yaushe tana bangaren Hajiyar, da safiya tayi Khalil ya fita ta gama abinda zatayi zata wuce can. Habiba ta shiga jami'a dan haka yanzu itake duk wani abu daya shafi Hajiya harda Abinci dan sauda yawa can take girki seta debar musu dan dama yaran kusan ko yaushe suna can, Mu'ayyad ya fara zuwa makaranta se Bibi ce kawai a gida.

Da sallama ta shiga palour Hajiyar Jalilah da zuwanta kenan ta dago suka kalli juna kowacce ta watsar da yar uwarta. Tun case dinsu da Hadiza Jalilan ta fita a sabgarta. Haduwa seta zama dole gaisuwa ko se akan idon Hajiya in ba haka ba babu meyiwa wata kallon arziqi.

Ita Umaimah gani takeyi Jalilah ke zuga Khalil, ita kuwa abinda Umaiman tayi ne ya saka ta fitar mata akai ga kuma wannan rainin da tayi mata tunda ai ko banza ta girmeta tayi qanwa ta kusan nawa da ita bataga dalilin da ze saka ta fara kulata ba.
"Aa, Umaimah kin shigo yanzu yau Weekend dinma bazaki zauna ki huta ba ai Habiba tana gida" Hajiya data fito daga kitchen ta fada cikin fara'a, Umaimah ta zame qasa ta shiga gaisheta ta amsa tana tambayarta jiki jiki ta amsa harda satar kallon Jalilah data sakawa waya Ido kamar ma bata parlour. Kwanon hannunta ta ajiye Hajiyan tana cewa

"Dambun kaza na miki tun jiya Hajiya shi nace bari na kawo miki yanzu"
"Toh Madallah na gode kwarai Allah yayi miki albarka kamar kuwa kinsan bakin yana kwadayi, bana so na sakaki aiki ne ga nauyin jiki shi yasa na saka Habiba kin ganshi can na kasa ci duk ta qonashi ka shegeb qarni daga ji bata saka kayan qamshi a kazar ba"

"Kai Hajiya kawai dan kin saba cin na Anty Umaimah ne amma wallahi abuna yayi dadi, dan Allah Anty ci kiji" Habiba data taho da kwanon dambunta ta miqawa Jalilah. Ta dibi kadan ta saka a baki tace
"Aiko yayi dadi kuma ni banji wani qarni ba Hajiya se qamshin spices ma yakeyi"

"Oho duk ta zuba wasu abu masu warin kyankyaso ba ni nafi son abu na haka daga citta se Tafarnuwa ci kiji banbancinsa da wannan" Hajiyan ta fada tana miqa mata kwanon Umaimah seta miqe tana cewa
"Kedai kici abinki tunda ya fi miki dadi" Umaimah ta harareta qasa qasa yanda baza'a lura ba amma tsaf Jalilan ta gani a ranta tace
"Da haka kika shanye mana uwa kenan ai kuwa zamuyi maganinki".

Miqewa Umaimah tayi tana cewa
"Bari naje Hajiya, Anty Jalilah amma yai dai zaki shigo mana dan ina lissafe tun ranar tariyar mu baki sake leqa bangaren ba".
Yanda take murmushi seka rantse har zuciya tayi maganar, Jalilah ta mayar mata da martanin murmushinta tace
"Zan shigo, ki gayawa dan qanina ina nan zuwa" da haka ta juya ta bar sashen.

Ta tarar da Khalil ya tashi daga aikin da yakeyi, wayarsa dake ajiye akan centre Table ta dauka,seda ta leqa dakinsa, qarar zubar ruwa dataji yasa ta gane wanka yakeyi dan haka ta dawao palour ta bude wayar ta shiga yi masa binciken data mayar dabi'arta. A sabuwar Islamiyyar data chanza a nan cikin unguwar saboda tasu tada tayi mata nisa daga nan dukda yanzu tana jan mota babu inda bata shiga amma akwai tazara sosai to a Islamiyyar tayi wata sabuwar qawa wai ita Safina ana kiranta da Maman Halima.

Qawance suka qulla tamkar sanda suke da Rufaida, Rufaidanda saboda qin Allah yanzu take so ta dawo mata suci gaba da qawance saboda ganin cewa Allah ya sake dagata Mijinta ya samu budi sosai ga tangamemen gida na kerewa Sa'a tana ciki se gata ta debi zugar yan unguwa su Maman Hauwa wai sunje yi mata Allah sanya Alkhairi dukda bata fada musu zata tashi ba se a bakin Maman Hibban sukaji dan suna hulda da ita har yanzu ita kadaice bata ji hudubar Rufaida ta dena kulata ba se Ramatu kishiyar Maman Hauwa.

Ita Safina ita ta qara mata sabon course na binciken wayar Miji. Dukda daman sa'i da lokaci takanyi amma yanzun da Safina ta karanto mata wasu gurbatattun tunani ta dasa mata zargi a ranta ya sa ta maidashi sana'a a cewar Safina Maza yanzu gaba daya yan iska ne kawai wasu ne suka fi wasu iya taku shiyasa ba'a gane su amma in kika zurfafa bincike da wayo se kin gano duk abinda Mijinki yake aikatawa a boye. Ba iya binciken waya ta koya mata ba harda Mota.

Haka kawai zata ce ya bata Aron mota ta fita ta samu guri ta bincike masa mota tsaf tun Khalil baya lura har ya fara gane idan ya ajiye takaddu ana canza musu tsari ya fara zargin ko a office ne wani yake masa haka se daga baya wata rana ya kamata,ta ari motar ta fita can qasan ta tsaya tayi parking shi kuma fitar gaggawa ta same shi dan haka ya dauki motarta ya fita. Ya dade yana mamakin me take nema, be nuna ya ganta ba ya tafi sabgarsa bayan ya dawo ya duba motar tsaf dan a ranar akwai tsabar kudi naira miliyan biyar daya karbo daga banki ze kai wani guri ya barsu a motar zuciyarsa ta darsa masa ko kudin zata dauka amma ya qaryata hakan dan a zamansu naira biyar dinsa be taba nema ya rasa ba idan ze aje abu ya shekara ze dawo ya tarar dashi batta idan tana da buqata zata uzzura masa ya bata amma bazata taba taba masa kudi idan bashi ya dauka ya bata ba

Bayan ta ajiye motar ya koma ya duba kamar yanda ya tsammata komai yana nan inda yake ko tsinke bata dauka a ciki ba dan yana da lura haka idanya ajiye abu be fiya mantuwa ba kuma ko ya aka taba seya gane shiyasa yasan komai dake cikin motar da kuma yanda suke tanbayar da yake yawan yiwa kansa itace me take nema? Se daga baya ya samu amsarsa randa ya taba jinta tana waya take gayawa wadda besan ko wacece ba ita Mijinta Dabanne da sauran Maza kuma baya cin Amanarta dan babu inda bata bincika ba har dirar mikiya data tsiri yi masa a Office se yana tsaka da Aiki zataje kuma bata taba kamashi da wata alama ta rashin gaskiya ba. A nan ya gane ashe duk wannan binciken na neman hujjar yana cin Amanarta ne kai Mata se a barsu.

Tsaye Khalil yayi a bayanta yana kallon yanda take bincika masa waya kamar wani danta, messages ta gama dubawa ta bude WhatsApp kenan ya fuzge wayar dan akwai abinda baze so ta gani ba, badan yana tsoron komai ha sedan kawai yanzu yana da buqatar nutsuwa wata kwangila yake nema yana kan Tsara papee work din ne kafin yayi presenting idan yayi ayi awarding nasu yanzu idan ta shigar Masa WhatsApp sabuwar chapter bala'i zasu bude a gidan kuma be shirya asarar wannan kwangilar ba.

"Wai sau nawa zan miki magana akan ki dena yi mun bincike a waya ne?" Ya fada cikin fushi, Umaimah data zabura dan sam bata san yana wajen ba ta dauka wanka yakeyi ashe ruwa ya tara be shiga wankan ba, hade rai itama tayi tace
"Idan mutum yana da gaskiy ai baze damu ba in an duba masa wayar ammaji yanda ka wani zabura ka kwace da alama wani abun kake boyewa a ciki"

"Ni dan ki ne da zaki ringa mun bincike dukma abinda nake boyewa ina ruwanki? Ki shiga hankalinki wallahi bana son shirme kinsan sarai yanzu da da ba daya bane bazan dauki ko wanne rashin hankalinki ba" Khalil din ya fada a hasale se kuwa ta riqe qugu tana cewa

"Lallai Khalil, ni kake kira mara hankali ko saboda na kusa na bankado Asirin abinda kake aikatawa a waje ko? To mu zuba mu gani, ni din dai nice Umaimah ba janzawa nayi ba kuma zan tabbatar maka da hakan duk wadda ta shirya siyan tashin hankali da kudinta taci gaba da kulaka" tana gama fadar haka ta haye sama fuuuu ta barshi a tsaye.

Bayanta yabi da kallo, shikenan Aljannun da aka saka a batta tun mutuwar Yaya Aminu sun balle bala'i ya dawo kai wannan yarinya shaidan yana jinjinawa Umaimah. Zama yayi akan kujera ya shiga WhatsApp din nasa ya bude, kamar yanda yayi tunani kuwa message dinta ne a farko ga saqon data turo na qarshe ya fito ras I love you da manyan baqi harda Jajayen heart emoji. Beko bude ba yayi deleting chat din gaba daya yana zauke numfashi, Zahra nema take seta saka shi a bala'i, shidai Addu'arsa Allah ya taimake shi kwangilar nan ta samu daga nan ba kare bin damo kowa ya kama hanyar sa amma kafin nan dole ya lallaba wannan yar Tijarar ya samu ta barshi ya kammala abinda yake gabansa.

Umaimah ko kasa zama tayi sanda ta shiga dakinta, tabbas akwai abinda Khalil yake boyewa kuma ko menene seta bankadoshi idan ba haka ba me yasa ze fuzge wayar bayan a baya kota dauka ya kamata sedai ya mata fada kawai amma baya wannan rikicewar,to wallahi ya tarowa kansa abinda baze iya ba kuwa in har ta kamashi da laifin cin Amana ba zata saurara masa ba.

Kayanta ta cire ta shiga wanka, fita zatayi tanaso taje gida ta duba Anty ance tayi targade a hannu ta manta ma se yanzu abin ya fado mata daga nan ta biya gidan Safina ta bata wannan labari lallai ta yarda da tace Khalil ya iya taku ne kawai amma babu yanda za'ayi ace Matashi da kudi kamarsa ya rasa Yammata ko be nema ba dole su bishi ai.

Sanda ta gama shirinta bata tarar da Khalil ba ya rigata fita, tayi kwafa wato baze mata sallama bama waya sani ko gurin Matan ya tafi. Motarta ta hau ta fice, a babban Get suka hadu da Jalilah da Habiba da alama fita zasuyi suma amma ba nisa zasuyi ba dan slippers ne a qafar Habiban ko kallonsu batayiba ta bawa mota wuta ta fice a sittin.
Chapter 131 · 0% Book details