← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 201 OF 267

Sashe 201

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dagowa Hajiya tayi a sanyaye ta kalleta tace
"Umaimah kiyi haquri ki koma Asibitin kinji"
"Hajiya tambayarki nayi kawai ki bani amsa babu ruwanki da dukma inda zani daga nan nidai kawai buqatata ki qara mun bayani akan abinda kunnuwana sukaji" ta sake fada tana dagawa Hajiyar hannu se daya daga cikin Qawayen Hajiyar ta yunqura da niyyar Magana Hajiya tayi saurin dakatar da ita tana miqewa tsaye ta nufi Umaimah tace
"Muje ciki nayi miki bayani toh"

"Babu inda zanje daga nan gurin harse kin gaya mun abinda nake son naji" Umaiman ta fada cikin daga murya tamkar me yi da yar cikinta daidai nan aka sake bude qofar falon Jalilah da Jamila suka shigo cikin shiga ta alfarma sunyi anko na Lace haka fuskokinsu sunsha make-up.
"Meye haka? Ke wace fitsarar kikeyiwa mutane da ake jiyo muryarki tundaga tsakar gida?" Jalila ta fada tana kallon Umaimah swta juya a fusace ta kalleta tace
"Bada ke nake ba da uwar data haifeki nake dan haka ki sararamun" ta sake jutawa kan Hajiya da jikinta ya dauki rawar tsoro saboda hango kamar Iskokan Rashin mutunchin Umaiman zasu tashi da tayi cikin rawar baki tun kafin ta sake yi mata magana tace
"Kinga Umaimah kiyiwa Allah mu shiga ciki bari na kira Khalil din duk inda yake yazo yanzu se kiji komai a bakinsa ma"

"Wai Hajiya menene haka saboda Allah wannan mara mutunchin yarinyar kike bawa haquri me aka mata ba dole ma ta sake rainaki ta ringa miki duk cin kashin data ga dama ba, dallah Malama zo ki fita daga nan bakiji kashedin da nayi miki ba kenan akan Hajiya to wlh ko kishiga hankalinki ko yanzu jikinki ya gaya miki" Jalila ta fada a fusace

"Idan baki dakeni ba Aisha da Usman shegenki sukayi Jalilah, ni zaku rainawa hankali ni zaku yaudara? Ashe daman abinda Mama da yan uwana suka fada mun gaskiya ne ni zaku yiwa rufa rufa a cikin gidan nan ku cuceni ku daurawa Mijina aure da wata ba tare da na sani ba?" Umaimah ta fada cikin wani sauti jikinta ya dauki rawa take idanunta suka rine zuwa Jaaa kamar jini ya kwanta, da hannu ta shiga nunasu tana jan nufashi maganar ma ta gagara fitowa daga bakinta se ta juya kawai ta fice daga falon Jamila tabi bayanta Ita kanta Jalilah da take a hasale nan take jikinta yayi sanyi saboda ganin yanayin Umaiman Hajiya kuwa hannu ta dora a kai tana kiran
"Shikenan kun gani ko Jalilah kinga abinda nake gudu Allah gamu gareka ka karemu daga sharrin zuciyar wannan yarinyar".

"Hajiya Aisha Allahya sanya Alkhairi ya kuma rufa asiri nidai bari naje" Hajiya Uwani ta dauki jakarta ta maqala gaba daya sauran suka mara mata baya sunayiwa Hajiya sallama ganin wannan tashin hankali dake shirin ballewa a gidan kowacce ta fita da tambayar daman Uwargidan Khalil din bata san yayi aure ba kenan?

Umaimah kuwa tana fita a compound din daya raba bangaren nasu taci burki tabi motar yan jere da kallo Sammani ya bude Musu Get suka fice. Gurin da Sammani yake zama ta kalla, wata ajiyar zuciya ta sauke saboda hango zungureriyar Kokarar da yake ajiyewa a kusa saboda barayi, bata kulashi ba da yake tambayar me take buqata ta zari qaton sandan tayi cikin gida, Jalilah data biyota taja da baya a zatonta ita zata lodawa Umaimah kuwa ko kallonta batayi ba ta shige falonta kai tsaye ta haye sama ta murda qofar falon Amarya cikin Sa'a ta jishi a bude ta tuta qofar ta shiga, bata tsaya bata lokaci ba ta shiga dukan duk abinda hannunta ya kai kansa.

Sedata rugurguza mata kayan kallo tas da su Centre table, Showglass, frames, flower vase da duk wani abu da ze iya fashewa kafib ta wuce da niyyar shiga bedroom din nan qofar a kulle bata haqura ba ta ringa dukan handle din qofar a qoqarinta nason ta lalata shi ta samu ta bude qofar daidai nan Su Jalilah suka hawo saman gaba daya saka saka salati ganin irin barnar da tayi cikin Tashin hankali Hajiya take cewa
"Haba Umaimah ba se kinyi haka ba kiyi haquri a warware komai cikin nutsuwa wallahi muma ba'a son ranmu ba Allah ne ya qaddara faruwar hakan amma..."

"Kiyi mun shiru tsohuwar munafuka har kina da bakin cemun wani abu bayan duk abunda kika shirya yanzu zakice mun ba'a son ranku ba a son ran kutumar ubanki ne kenan kika aura masa yar qawarki sannan kice mun ba'a son ranki ba to idan kin cika ki qaraso nan ki gani na rantse da Allah sena rotsa miki kai ki mutu kowa ya huta na rage mugub irin Azzalumai macuta"

"Ke Umaimah baki da hankali ne Hajiyar kike gayawa haka?" Jalilah ta harzuqo zata qarasa inda take Hajiya ta riqeta tana girgiza mata kai tace
"Aa Jalilah karkije ba a hayyacinta take ba maza ki kira Khalil, Jamila dakko wayata ki duba lambar Hajiya Malika ki kirata dan Allah su taima suzo"

"Amma Hajiya.."
"Kiyi abinda kawai na sakaki Jalilah" Hajiya ta dakatar da ita, wani mugun kallo ta watsawa Umaimah data tsaya taja jiran wani cikinsu ya qarasa ta sauke masa kafada tayi kafin ta juya ta sauka qasa suka bar Hajiya tsaye dan tuni Jamila ta tafi dakko wayar Hajiyar itama.
"Ki bisu idan kina son ranki da lafiyarki" Umaimah ta fada mata cikin hargagi se Hajiyan ta juya da sauri ta bar saman, Umaimah kuwa dukan qofa taci gaba dayi so kawai takeyi ta bude ta qarasa aikin data fara kafin ta ragargaza Angon ta kumaje ta ragargaza Amaryar kamar yanda tayi mata alqawari, seda ta gaji da dukan qofar amma taqi buduwa ta haqura ta sauka, bazata iya misalta abinda take ji ba a taqaice ma zata iya cewa bata tantance komai ita dai tasan tana da rai kuma tana numfashi sauran abunda takeyi umarnin zuciyarta kawai take bi badan tasan abinda take aikatawa ba. Abu daya take ji a kunnenta kuma take gani Lokacin da Mama take gaya mata Khalil yayi aure se kuma hotonsa da waccen yarinyar da yake mata yawo a ido.

Qofar part dinsu ta dawo ta tsaya, Hajiya da yayanta na tsaye daga tasu qofar da alama jiran masu kawo dauki sukeyi akayi horn Sammani ya bude Get da gudu motar Khalil ta danno cikin gidan, kamar walqiya haka ta miqe tadurfafi motar da gudu, Khalil dabe lura da tahowarta ba dan waya yakeyi da Amaryarsa daya baro yanzu zuwan da yayi gidan kaya yazo ya canza danta kafa rigimar ko bazeje gurin Kamu ba to yazo suyi hotuna dan haka yazo ya saka babbar riga,duk uban kiran da Jalilah ta ringa masa be daga ba saboda zatonsa maganar Bikin zata masa yana qoqarinfaka mota se ganin mata yayi kamar an jefota Allah ya taimaka ya riqe motar yana salati kafin ya qarasa gane abinda yake faruwa qarar fashewar glass din gefen da yake zaune ta cika gurin cikin Azama ya durqusa dukda haka seda wani ya yanke shi a gefen fuska, ya balle murfin motar da bala'in sauri ya fice ganin ta sunkuya daukar kokarar data yi masa aika aikar da ita ta fadi.

Qoqari yakeyi ya gane me yake faruwa a gidan dan shi bema gane Umaimah bace so yake yaga wace mahaukaciya Sammani ya bari ta shigo musu saukar dutse yaji a goshinsa se a sannan kuma idonsa ya gane masa Umaimah datayi biji biji kamar wadda ta tsumu a cikin hauka ta sauke masa Kokarar a qeyarsa Dafe be ko tsaya takan Zugin Azabar daya ziyarceshi ba yayi baya ganin ta sake durfafoshi ido rufe, baya buqatar wani qarin bayani abin boyene ya fito fili qila se yanzu kwakwalwarta ta gama fassara mata duk maganganun da ake gaya mata ko kuma yanzu ne ta samu gamsashshiyar hujja data saka ta yarda da, amma ita daya baro a Asibiti meya kawota gida?

Ganin tana qoqarin qara loda masa itace a duk inda Allah ya bata sa'a ya saka qarfi ya murde hannunta ya kwace Kokarar ya jefata gefe Sammani yabi da gudu ya dauke, Umaimah kuwa ganin ya rabata da makamin ta cakumi kwalarsa ta shiga kai masa duka kota ita da hannayenta se a sannan ta fashe da matsanancin Kuka tana cewa
"Allah ya isa tsakanina dakai Khalil Dan iska macuci maci Amana Azzalumi mayaudari ma ha'inci wallahi Allah baze barka ba yanda ka cuceni ka yaudareni se Allah ya bimun haqqina akan ka kaida munafukar uwarka data tayaka kuka yaudareni wallahi se kunga sakayya akan abinda kukayi mun".

"Relax Umaimah relax" ya iya fada yana qoqarin riqe hannayenta amma ina qarfin data samu yau din ya zarce misali gashi shi kuma dukan datayi masa a qeya ba qaramin shigarsa yayi ba dan daga tsayen da yake jiri yake ji kamar ze kadashi, ya waiwaya ya kalli su Hajiya da sukayi cirko cirko aka rasa me kai masa agaji a cikinsu kowa ka kalla fuskarsa ta nuna zallar tashin hankali, kome ta tuna a sukwane Umaimahn ta saki kwalarsa tayi part dinsu tana ci gaba da kuka kamar ranta ze fita Khalil ya bita a baya yana kiran sunanta, a duniya bayan ranar da ze mutu wannan ce rana ta biyu da tun faruwar al'amarin yake taraddadin zuwanta domin be san a yanda zata zo masa ba. A tsakiyar falon yaci birki ganin ta fito daga kitchen da sharbebiyar wuqa a hannu ta se kyalli takeyi ya bude ido dakyau yana kallonta ganin shi ta durfafa da wuqar ai tuni ya manta da wani jiri da zafin da qeyar sa takeyi ya kwasa a dari da sittin ya fita waje Umaimah ta mara masa baya tana kuka tana fadin
Chapter 201 · 0% Book details