← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 267

Sashe 31

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kiji ki fa kamar waddaza'a kai saqo Niger ai da yardar Allah kafin Isha ma saqo yazo hannunki yanzun nan zanyi packaging na baya a saka miki a tasha, ki gayawa Amarya ta kwantar da hankalinta wannan matsakar an maganceta, idan da TULA-TULA, babu jin kunya" suka kwashe da dariya daga nan sukayi sallama.

"Allah ya kamaki matar nan, yanzu gashi a bagas munji sirrin yanda akayi abubuqa suke tsaye qyam kamar baki shayar ba" Yaya Hafsa ta fada, se da Anty Mamin tayi fari da ido kafin tace

"Toh ya ranki, yaya hudu na shayar yanzu waze kalleni yace sati na uku da yin Yaye?"

"Au wai kin Yaya Ni'ima amma kalli Nonon a cike koda yake tunda kike yaye ma ai ban taba ganin Nononki ya zube ba, tunda dai yau Allah ya matsi bakinki kin tona sirrin se ki gaya mana da kin gantalar damu da shan wata sabaya, sedai jiki yayi kyau amma abinda ake so ya tsaya din se a hankali, taimakamun kinji Surukata, nima na saka ranar Yaye wallahi har fargaba nake gaba daya nono ya zube ya koma kamar wanda qullin zobo ya fashe" Anty Ruqayya ta fada yanda tayi maganar dole ta baka dariya.

Seda suka dara kafin Anty Mamin tace "wani maganine na samo shi gurin Maman Ilham Sunansa *TULA TULA* Magani ne sadidan na gyaran nono kuma kowa yana iya sha Yan Mata da zawarawa masu Shirin yin aure, me shayarwa dukka kowa nasha Daga mambila Ake kawoshi kunsandai yanda Matan fulanin nan nasu suke qirji a tsaye kamar na babyn roba to TULA-TULA ne sirrin kuma yanayi sosai Bada wasaba koda yake ku zaku bada shedar haka.

Kinga kamar ke yanzu da zakiyi Yaye zaki fara Sha sati daya kafin yayen to In sha Allahu bazakiyi ciwon nono ba ko zubar ruwan nono lafiya lau zekiyi  yayenki Kuma nono baze kakkabeba".

"Amma matar nan anyi me baqin abun, yanzu da shine kika barmu muna ta bulayi kullum kyaji muna jimamnin neman maganin gyaran nan amma kinyi bulumbuqui idan anyi magana kice ku Natural ne toh kin wa kanki" Maman Asad ta fada tana kama baki, Se Anty Mamin tayi dariya tace

"Toh ai ku dangin miji ne ba'a iya muku haka kawai in bankada muku sirrina, Aa gara dai na adana abuna"

"Allah ya yafe miki matar nan, kinga sake kiranta yanzu a hado dashi ina son qulli goma nawane?" Anty Ruqayya ta fada,

"Sannu duk me zakiyi da har guda goma?" Mamin ta fada tana zare ido, Anty Ruqayya ta murguda baki cikin wasa tace "Ina ruwanki, kedai kirata kawai" sauran ma suka dauka gaba daya kowa tace a hado mata dashi tana so nan da nan kuwa ta Kira Maman Ilham ta gaya mata adadin da suke so, basu bar gidan ba se bayan Isha'i lokacin har saqon ya iso daga Kaduna sun aika an karbo musu a tasha kowa ta adana nata a jaka

(Indai matsalar ki Zubewar ko kwanciyar Nono ce tazo qarshe, ki nemi Maman Ilham akan 08135613021 ki siyi naki akan farashi me sauqi, tana Kaduna tana aikawa ko ina a fadin qasar nan da yardar Allah).

Kwanci tashi aka ce asarar me rai se gashi ana lissafin biki ya rage kwanaki biyar a fara, tuni Amare suka dauki harami jiki yayi mulmul fata tayi subul saboda ingantaccen gyara da suke samu daga gurin Anty, sal take sillesu da kurkum da dilka su shige cikin Hayaqin Dukan (wanda ba qaramin gyara mace yake ba, idan so samu ne kowannce mace ya zama tana da itacena gidan ta lokaci lokaci ki ringa turara jikinki yana maganin sanyi da sauran matsalolin mata ga matsi ciki da waje) idan suka gama wannan sukayi wanka kuma su sake mulke jiki da hadaddiyar kolakca sannan a shiga sabon turaren jiki shi yasa qamshi ya kama su duk inda suka gifta se sun bar mutane da bude hanci.

Idan kaga yanda Nuratu ta cicciko abin kamar almara dan Tula Tula ya karbeta, Umaimah me mata iskanci se gashi itama tana bin dare tana diba dan itafa duk ta inda za'a ce wani ya fita se tabi ta toshe qofar, Khalil yayi Namijin qoqari dan dubu dari biyar cis ya bata kudin hidimar biki, sanda ta gayawa Mama abinda ya turo din fada ta ringa yi mata akan me yasa zata takurashi ta karbi kudi masu yawa haka bayan babu abinda ba'a yi musu ba, har Khalil din ta kira, ya tabbatar mata da ba ita ta roqeshi ba. Kawai dai ya samu kudade ne shima dan sosai yake samun gudummawa tunda katin daurin auran ya fita Manyan mutane da ya tabayiwa aikin zanen gida kawai sedai yaga Alert ko yaji an kirashi a waya ance yaje ya karbi cash.

Allah kenan, a lokutan baya idan yana tunanin aure se ya ringa ganin kamar ba ze iya ba dan bashida abinda zeyi hidimomin se gashi yanzu ya yarda da abinda Hajiya take fada masa na cewar shi aure ba'a shirya masa shi yake shirya kansa, duk sanda mutum ya niyyata yinsa se kaga Allah ya buda masa gashi kuwa ya gani dan rufin asiri samun sa yake ta ko ina babu abinda ze ce sedai ya qara godewa Allah ya kuma tabbata Umaimah Alkhairi ce a rayuwarsa dan tunda ya hadu da ita yake samun budi ta hanyoyi daban daban, shi yasa bazeji qyashin kashe mata ko nawa bane a cikin dukiyarsa.

Ranar Alhamis ana gobe Kamu sukaje qunshi da gyaran gashi. Wani Hadadden Salon sukaje na mataasu Aji dan tundaga harabarsa zaka gane hakan saboda irin manyan motocin dake zube na matan da sukazo qunshi, gyaran gashi ko gyaran jiki.

Da yake sun rigada anyi musu booking basu bata lokaci ba nan da nan aka farayiwa Umaimah Jan Lalle wata kuma ta shiga wanke mata kai akayi steaming dan kitso zatayi Nuratu kuma aka saka mata Relaxer.

Cikin abinda be wuce awa uku ba se gata ta fito a Amaryarta fes, tayi kyau na gaske lallen da aka mata Jan yayi maroon sosai ya kwanta a fatarta da bata da haske sosai amma gyaran data samu ya taimaka gurin sake fito da ainihin kyan lallen ga qananan kitso an yarfa mata dole ka kalleta seta burgeka.

Tana zaune daga kan kujera ana zanawa Nuratu Baqin lalle bayan an gama mata jan dan ita Umaimah cewa tayi bata so duk yanda masu lallaen suka kada suka raya kuwa taqi dole suka haqura. Khalil ne ya kirata Video call, santin kitson da jan lallen ya ringayi dan ba qaramin kyau suka masa ba.

"Babe har an gama ne na taho na dauke ku? Dan bazan iya bari wani ya fara gane mun wannan gayun naki ba" ya fada bayan daya gama kodata, Murmushu tayi masa tace
"Aa Yaya Nuratu ake qarasa baqin lalle amma ana qarasawa zan kiraka kafin kazo yasha iska se mu tafi ta wanke a gida".

"Yauwa ke ba'ayi  miki wannan flower black ba da naga anayi yanayi mun kyau sosai, kice su rubuta miki sunana a nan" ya fada yana nuna mata gefen wuyanta, fuska ta dan bata tace

"Ni bana sonsa amma tunda kana so bari ayi mun"
"No ki barshi in bakya so wannan ma ya isa amma yanayin kyau sosai idan na ganshi a hannun mutane yana burgeni kuma musamman ma nasan idan akayi miki se yafi na kowa yin kyau" Khalil din ya fada, jin haka kuwa ba shiri ta bata fuska tace

"Wato kallon yammata kake yi har lallensu yana burge ka koh?"

"Ba haka nake nufi ba, idan su Habiba sunyi nefa nake gani. Ni ina naga lokacin kallon wasu yammata kullum ina site ina fama da sumunti da yashi" ya bata Amsa yana qunshe dariyarsa, ta maka masa harara kafin tace

"Se anjima idan mun gama i will call you"
"Ok ayi miki ke kyau kinji Babe, love you" ya fada tareda huro mata kiss, baki ta tura masa yayi dariya ya kashe wayar, seta kalli wadda ke zanawa Nuratun lallen sun gama saura qarashen hannu daya, murya a cukule tace

"Idan kin gama mata zakiyi mun, kuma yafi nata kyau"
"An gama Amarya" matar ta fada tana dan murmushi dan tun tana wayar suke kallonta daman kuma Nuratun ta fada tace su jira su gani zayi gashi kuwa.

Lalle me kyau matar ta zana mata na Amare dukda Umaimah nata noqewa a barshi yayi yawa amma ta shareta seda tayi mata yanda ya kamata ita da kanta kuma ta dawo tana Admiring lallen ganin yanda ya qawata hannunta sosai.

"Hajia Ango fa yace a rubuta miki sunansa a wuya" Me lallen ta fada bayan sun gama dataga Umaiman na shirin kishingida a kujerar da take, wani kallo ta watsa kafinta fara magana cikin fushin da bata gama saukowa ba na zancen lallen da Khalil yayi tace

"Daman samun ido kikayi har kina jin abinda mijina yake fada? Irin kune daman masuyiwa mutane labe kuna sauraran conversation dinsu ko? Toh bari kiji Mijina yafi qarfinki sedai ki qare a nan kina zana baqin lalle da baqar fuskar ki a gurin" sosai ta ringa spark tana bala'i ma'aikatan gurin na bata haquri dan a policy dinsu customers are always right, koda kuwa sune da rashin gaskiya.

Nuratu da ta shiga toilet wanko lallenta ta jiyo hayaniyar babu shiri ta fito
"Umaimah meye haka? Me yasa ke baki da mutunci daga abin arziqi shine zaki fara zaginta" Nuratu ta tareta se kuwa ta juya kanta tace

"Babu ruwanki saboda ba naki mijin tayiwa labe ba shi yasa zaki tare mata, akan me zata saka kunne harta ji muryar sa?"

"Da kika san bakya so aji muryar me yasa zakiyi waya a gaban mutane ko kin manta da video call kikayi kuma a speaker baki saka earpiece ba? Wallahi Umaimah ki shiga hankalin ki tun wuri kafin ki jawowa kanki baki" Nuratunta fada a fusace itama, Umaimah ta bude baki zata bata amsa wayarta tayi qara, Khalil ne.
Chapter 31 · 0% Book details