← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 267

Sashe 21

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Toh se kin dawo Allah ya raba, idanan gama abin karyawa a biyo ku dashi" Anty ta fada tayi hanyar kitchen tana ci gaba da cewa
"Bari toh na dora ruwan kunun kafin su kawo markaden, Allah ma ya taimaka ruwa be sauka ba jiya yanda aka baje itacen nan a waje da yau mun gayawa aya zaqinta".

Har Maman taje qaramar qofar fita daga gidan ta juyo tace " Saratu karki kama mata aikin nan, ita zatayi komai zuwa anjima idan ban dawo da wuri ba ki bata abinda za'a dafa na rana tayi" ta juya ta fice daga gidan.

Hawayen takaici ne suka zubowa Umaimah wato da wannan uban aikin za'a horata kenan? Ai wallahi gara kullum a yi mata bulala goma akan wannan uban shara da wanke wanken gidanga qarin girki da itace, ina zata tsoma ranta wai? Ba'a bar mutum yaji da abinda ya dame shi ba za'a rikito masa da wani bala'in.

"Halan wani laifin kika mata ko Umaimah?" Antyta fada taba kallo ta amma yanda kasan da dutse tayi magana haka tayi,bata damu ba ta shiga hada murhu ta dora ruwan zafi kafin ta dakko qullin kunun ta shiga damawa daidai sanda Almajiran suka kawo markadan qosan, Wanke wanken tace suyi, sega Abba ya fito daga dakinsa da waya a kunnensa.

"Kai kuje abinku idan an gama abinci ku dawo ku dauka, daga yau kun bar aikin nan har zuwa sanda za'a ce ku ci gaba" Ya fada yana kallon su Nazifin, suka tsame hannu daga kumfar da suka kada tareda daurayewa kafin suka fice daga gidan.

"Wai Alhaji ya haka ne? Ya zaka hana su yin wanke wanken bayan kasan aikinsu ne yanzu waye zeyi?" Anty ta fada bayan data dakata daga buga qullin qosan da takeyi.

Ba kiji Abinda Malika tace bane da zata fita? Ga wadda zatayi nan. Kema ki tashi daga wannan aikin kije ki hadamun ruwan wanka da wuri zan fita" yana gama fada ya juya cikin daki abinsa. Umaimah ta kalla da tayi mutuwar tsaye da tsintsiya a hann, ta fara murnar Allah ya kawo mata dauki dan sharar da takeyi kadai jin bayan ta take kamar ze cire inaga ta kama sauran ayyukan se ga Abba yazo da wannan zancen kuma.

Rau rau tayi da ido tana shirin fashewa da kuka Antyn tayi saurin dakatar da ita da cewa
"Karma kiyi asarar hawayenki bari naje na same shi wannan wane irin abu ne? Itama Maman banda abi ta ina ita ina saka Amarya aikin wahala ku da ya kamata yanzu ku qara hutawa kafin a fara gyaran jiki idan wani abin kikayi ai hanyoyin horo da yawa ba lallai seta wannan hanyar ba. Ina baze ma sabu na ace za'a sakar miki wannan uban aikin ke kadai dole da sake" ta goge hannu ta ta wuce dakin Abban tana ci gaba da mita.

Karon farko da Umaimah taji yau Antyn ta mata abin arziqi dan ko babu komai ta nuna tausayawa akan ta abinda uwa da uban da suka haifeta basu mata ba. Sharar taci gaba dayi tana share hawaye, a kan window ta ajiye wayarta yabda da Khalil ya kira zataji qara amma har sannan bataji ko qarar shigowar saqo ba ga wannan sabon bala'in da taje ciki kuma haka ta qarasa sharar ta kwashe,

Ruwan kunun ya tafasa har sannan kuma Antyn bata dawo ba, tasan halin Abban sarai dan haka sahunta a likafa gara tayi abinda zata iya kafin ya fito ya nemi abin kari, ruwan ta sauke a garin juyewa ya dan zubo mata a qafa saboda gaba daya hankalinta baya kan abinda take yi ta kuwa saki qara ta wancakalar da tukunyar a qasa tana yarfe hannu tareda sosa inda ruwanya zuba.

Daga cikin daki inda Anty da Abban suke dauki ba dadi suka leqo a tare, da sauri ta qaraso gurin tana cewa "meya faru? Badai qonewa kikayi ba?" Umaimah babu bakin magana se kuka take tana yarfe hannu, Anty ta dubi Abba daya ja ya kwafe a a tsaye tace

"Ka gani ko gashi nan haka kawai kun jawo ta qona qafarta, fisabilillahi Alhaji me yasa kake haka? Duk fa abinda Nasiha da Addu'a basuyi maganin sa ba duka ko aikin wahala bazeyi ba. Yanzu gashi nan tun baa je ko ina ba ta qona qafa ta yaya kake zaton zata iya da aikin gidan nan ita kadai? Ko mu din da muke yi ai muna da mataimaka ballantana" ta ci gaba da mita dan itama gwanace a fannin kafin ta debo qulli ta zuba mata akan qafar bayan data tofa mata Addu'a tace
"Tafi ki zauna haka kawai da safiyar nan an jawo miki"

"Ruwan bada yawa ya zuba ba ba? Ko zamuje a duba mata qafar?" Abba ya fada yana kallo ta, se Umaimah ta girgiza kai har sannan tana hawayen tace "Aa Abba baze tashi ba tunda Anty tayi mun tofi, anjima se naje gurin Ya'u me Chemist ya bani magani"

"Allah ya sawwaqe" ya fada tare da juyawa dakinsa.
Umaimah ta dingisa ta dauki wayarta ta shige daki, seda ta wanko qafar a Bandaki kafin ta zauna kan gadonta tana sauke ajiyar zuciya fa ruwan kadan ne ya dan zubar mata, yanda abin yazo mata a bazata ne ya sakata sakin tukunyar ta fake da hakan ne kawai saboda ta samu mafita gashi kuma Allah ya fiddata.

Number Khalil ta danna zata kira sega kiran sa ya shigo cikin azama ta daga tareda fashe wa da kuka kamar wadda aka cewa Mamanta ta mutu. Be ce mata qala ba ya barta tayi iya yinta, abinda ya ringa qarawa kukan nata qaimi shirun da yayi mata, ta saba idan tana so ta daga masa hankalo kawai zata kirashi ta fasa kuka shi kuma ya ringa lallashi da banbaki kenan har se tayi shiru amma yau yana jinta yai buris da ita dan kanta tayi shiru kafin tace

"Wai me nayi maka Khalil kake Azabtar dani haka? Kasan yanda nake ji kuwa? Ko so kake se zuciyata ta buga na mutu sannan zaka yarda da sonka ya gama yi mun illah?"

Daga bangaren Khalil dake zaune a office dinsa ya rufe ido ya dafe kansa da hannu daya, shi kadai yasan wahalar daya sha daga jiya zuwa yau saboda rashin magana da ita, gaza jure ganin tana kira baya dagawa yayi abinda ya saka ya kashe wayar gaba daya kenan daga baya kuma ya kunna ya sakata a cikin drawer kawai dan juriyarsa ta kusa qarewa.

Yanzun da take wannan kukan jinsa yake kamar ana masa yayyafin ruwan zafi, ita take kukan shi yake jin zafin abin a ransa amma yaya zeyi? Umaimah bata dace dashi ba. Dole ta qarfin tuwo ya yakiceta daga ransa in har yana neman zaman lafiya a rayuwarsa amma yaga abin da kamar wuya dan ji yakeyi wutar son ta tana qara ruruwa a zuciyar sa a maimakon tayi qasa.

"Khalil Khalil kana jina kayi shiru" Umaimah ta fada abinda ya dawo dashi daga tunanin daya tafi kenan, gyaran murya yayi yana jin wani na taso masa akan abinda yake shirin aikatawa amma yasan shine kadai gatan da zeyi musu daga shi har ita,

"Umaimah duk wannan drama da kike yi ta mecece wai? Kin manta irin zagin da kikayi mun jiya da irin kalaman da kika gaya mun? Kefa kika fada da bakinki babu ke babu ni na fita daga sabgarki to me kuma kike so nayi miki yanzu?"

"Duk abinda na fada maka bacin rai ne ya saka, kasan yanda nake sonka nake kishinka wallahi Khalil idan na ganka da wata mace ji nake yi kamar na kashe kaina tsabar baqin ciki kuma duk abinda na fada maka ba daga zuciyata bane kawai raina ne ya baci amma ba da gaske nake ba" Umaimah tayi saurin katse shi.

Se yayi wani dan murmushi kafin yace "Bacin rai se ya saka hankali ya gushe kuma? Sannan Kishi ya rufe miki ido kin kasa banbance yan uwana da sauran Mata, idan kinyi haka akan yar uwata ta jini da babu aure a tsakanina da ita Umaimah me ze faru kuma duk randa kika ganni da wata daban, kinga komai yana iya faruwa kenan.

Bazan iya saka rayuwata a cikin matsala ba, zan aureki ne saboda ki yi daidai da tsarina ina sonki ina kuma samun farin ciki a gurinki bansan wannan rashin hankali shi kike kira da kishin da kika ce kina dashi ba, a ban aureki ba kin zage ni saboda wata kinga kuwa idan mu kayi aure tsaf zaki iya neman rayuwata dalilin wannan baqin HALIN KISHIn,
Se yanzu na gano ainihin abinda ya saka sauran samarinki fasawa nima Allah ne ya soni da rahama ya kawo faruwar hakan da qila watarana ina bacvi sedai kawai na farka na ganni a lahira dalilin abinda bansan mafarinsa".

"Allah ya tsareni da kashe ka, ina sonla Khalil dana rasa ka gara na rasa raina, dagaske zanyi fito na fito da duk wadda tace zata shiga tsakanina da kai amma bazan taba bari wani abu ya shafi lafiyarka ba, zan kareka da iya kar kulawata, zan baka farin ciki har qarshen rayuwata saboda kai din kaine Rayuwata" Umaimah ta fada tana fashewa da wani sabon kukan daya ke jinsa har cikin ransa, so yake yace tayi haquri ta dena amma ya rigada yayi making mind di sa akan tarayyarsu ba kuma ya son wani abu da ze karya masa lago, ko wannan doguwar maganar da suke yi ji yake kamar ze rasa qarfin guiwarsa.
Chapter 21 · 0% Book details