← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 267

Sashe 139

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Umaimah" ya kira sunanta a tausashe bata amsaba kuma bata dago ta kalle shi ba dan haka ya qara matsarta yana qoqarin kama hannunta daya ga jini ya bata yana cewa
"Umaimah please..."
"Karka kuskura ka tabani Khalil idan ba haka ba wallahi sena baka mamaki" ta fada tana fizge hannunta tareda tashi tsaye sam ko nauyin cikin jikinta bataji, miqewa yayi shima da saurin ganin tana qoqarin taka kwalaben dake zube a qasa dan ko shi da yake sanye da takalmi da taka tsantsan ya tsalleke su, ruqota yayi ta fizge ta tafi baya saura qiris ta fadi ya sake tareta be bi takan dukan datake kai masa ba ya dagata cak suka fice daga dakin

"Ka ajiye ni Khalil ka ajiyeni dan kutumar ubanka" ta fada cikin wani irin sauti ai kafin ta kai qarshe ma ya direta a qasa yana bin bakinta data qunduma masa Ashar dashi da kallo.
"Ni kike zagi Umaimah?" Ya fada cikin mamaki yana nuna kansa, idon ta cikin nasa tace
"Na zageka maqaryaci maci Amana, taron da zakuyi da su Anwar din kenan ka tafi gidan su Budurwa a Yankaba, saboda ka mayar dani bansan abinda nakeyi ka dauka akwai wata qarya da zakayi mun ban gane ba? Wallahi kar nake kallonka Khalil, kuma tun ranar dana fahimci kana cin Amanata na dana maka tarko, duk wani motsinka akan ido na kakeyinsa ban kuma tabbatar daka cika qasurgumin maqaryaci ba se yau da har ka iya tsara zance ba tareda ka koji tsoron Allah ba ka yaudareni".

Kallonta kawai yakeyi har ta kai aya, jikinsa ya qarasa mutuwa, yanzu shi Umaimah ta zaga haka kai tsaye ba tareda shayin komai ba? Lallai abinta ci gaba yakeyi ba kuwa ze dauka ba, baze taba zama sakarai a gabansa mace ta zage shi ba dan haka nan take shima ya hade fuska yana kallonta yace
"Eh naje gurin budurwa se akayi yaya? Ajiyarki aka bani da zaki ringa bibiyar rayuwata ki daka mun ido ko kuwa? Sannan da izinin wa kika je, ba Salon na ajiyeki ba amma saboda baki dauki aure a bakin komai ba kina ganin zaki iya duk abinda kika ga dama shiyasa kika bini ai, kuma gashi nan a garin bin diddiginki ki tono abinda ze hana ki zaman lafiya dan da banyi niyyar sanar dake ba se komai ya kammala saboda kar hankalinki ya tashi amma yanzu tunda kin sani shikenan, auranta zanyi ita yarinyar da kika ganmu tare kuma baze dauki lokaci ba dan dakyar za'a ci wata daya nan gaba" ya fada da wani kalar expression akan fuskarsa.

Umaimah da tayi kasaqe tana kallon sa lokaci daya tayi kansa tana cewa
"Qarya kakeyi wallahi Khalil, baka isa kayi aure ba kai nawa ne ni kadai babu macen data isa ta shigo rayuwar mu. Idan kuma ka shirya ja mata bala'i shikenan karka manta da abinda ya samu Hadiza wallahi se nayi mata ninkinsa se ta zama mujiya a cikin mutane ba ita ba har iyayenta se sun zama abin tausayi".

Tsaki yayi ya wuce dakinsa ransa yana bala'in zafi, Ya rasa Umaimah wace irin mutum ce da idan ranta ya baci hankalinta yake gushewa. Ganin ta sauka qasa da sauri ya saka shi juyawa yabi bayanta amma kafin ya tarar da ita har ta fice daga palour seya qara sauri yana kiran sunanta ganin a yanayin da take kuma ta fita a hakan Umaimah kuwa ganin ya biyo ta ma se ta saka gudu, a parlour Hajiya ta zubr tana wani irin kuka ga numfashinta na qoqarin daukewa. Hajiya data idar da sallar Isha tana zaune a saqon kujera ta miqe a gigice tayi kanta tana tambayar lafiya? Koda yake babu alamarta a tattareda ita. Yanda take a hargitse ga jikinta duk jini ya bada amsar abinda yake faruwa.

"Khalil ne" ta fada cikin jan numfashi, Hajiya ta dafe qirji tace
"Dukanki yayi? Shaye shaye ya fara kome?" Daidai nan ya shigo shima kamar an jefo shi Hajiya ta miqe da sauri tana cewa
"Me kayiwa yar mutane Khalil, me tayi da zaka aikata mata wannan mugun abun?"

"Wallahi Hajiya babu abinda nayi mata nima dawowa nayi na tarar ta fasa komai na dakinta ni ban mata komai ba" ya fada da sauri ganin Hajiya na neman laqaba masa abinda beyi ba. Umaimah dake kwance lakadan saboda wani azababben ciwo da mararta ta dauka ta bude baki dakyar tace
"Qarya yakeyi Hajiya ya san me yayi mun, ki gaya masa ko ya fasa abinda yayi niyya ko na kashe kaina wallahi".

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Umaimah wace irin magana kike haka kamar ba musulma ba? Ki kashe kanki a saboda me saboda damuwar duniya? Kar na sake ji, kai kuma kamata mu tafi Asibiti kalli, innalillahi wainna ilaihi raji'un" Hajiyan ta sake fada tana zare ido ganin jinin na bin qafafun Umaiman. A rikice yayi kanta ya dagota, hankalinta ya fara nisa daga jikinta shiyasa ta gagara hanashi bata san yanda akayi ba se farkawa tayi ta ganta a Gadon Asibiti gefenta Khalil na zaune ya dora kansa akan gadon da take kwance.
Abinda ya faru ne suka fara dawo mata, murmushin da yakeyiwa Zahra ta hango bata san sanda ta saka hannunta da ba'a daura mata ruwa ba ta kwada masa mari a qeya.

A gigice Khalil ya farka yana zare ido, tun daren jiya da aka kawo ta be runtsa ba se yanzu da safe bayan su Hajiya sun tafi gida aka barshi shi kadai koda yake yace ze zauna da ita.
Kama hannunta yayi ganin tana qoqarin fizge qarin ruwan da aka saka mata ta juyo a fusace tace masa
"Ka sake ni karka sake tabani Khalil"
"Ki nutsu Umaimah ba'aso kiyi wani dogon motsi dan Allah saboda jijjiga jikinki da kikayi jiya seda akayi miki daurin bakin Mahaifa saboda babyn tana nema ta fito lokacinta baiyi ba ki koma ki kwanta" Khalil ya fada cikin muryarsa da bata fita dakyau saboda bacci da gajiya ga ciwon kai. Bata ko saurara na ta zare allurar, jini ya fara zuba daga hannun ko a jikinta ta dire qafarta qasa tana yunqurawa zafi da jiri suka ziyarci kwakwalwarta lokaci daya ta koma ta kwanta tana kwala ihu dan ji tayi kamar ganinya ya dauke saboda jiri ga wani ciwon Mara daya sake taso mata.

Nurse ce ta shigo dakin, take ta rufe Khalil da fada ta fita da gudu ta kira likita haka suka rufu kanta aka sake maida mata qarin ruwan tareda yi mata allurar bacci data rage radadi saboda yanda take ta faman juye juyen ciwo tana wayyo. Fada likita ya shiga yiwa Khalil, abin ya bashi haushi ya fice daga dakin ya barsu idan dai Umaimah ce gasu gata nan ai su da kansi zasu bada labarin halinta.

Gida ya wuce yana zuwa ya tarar da Hajiya cikin shirin sake komawa Asibiti, jiyan bata baro ba seda komai ya daidaita aka bawa Umaiman gado gurin daya na dare kafin Khalifa ya kaita gida ta bar Khalil ya kwana dan yace baza'a kira yan gidansu a cikin daren a tayar musu da hankali ba a musamman Mama bata da lafiya malaria ta kwantar da ita dan haka yace a bari seda safe tukunna a kirasu.

"Khalil, ya jikin nata ta farka kuwa?" Hajiya ta tsare shi da tambayoyi. A taqaice ya bata amsa ya wuce ciki dan gaba daya ji yake kamar kansa ze fashe tsabar bacci da ciwon da yake masa. Jin ana binsa a baya ya sakashi dakatawa ya juya, Hajiya ce se ya qarasa shiga parlour ta biyo ciki suka zauna akan kujera tana kallonsa tace
"Khalil meya hadaka da Yarinyar nan a wannan yanayin da take ciki zaka bigeta? Yaushe ma ka fara dukan Mace ban sani ba karfa giyar kudi tasa ka sauka daga layin da nasan ka aki Khalil?"

Dafe kansa yayi daya sara masa, shikam ya rasa wace irin makauniyar soyayya Hajiya takewa Umaimah da duk abinda ya hado da ita kawai bayanta take bi. Dakyar ya iya bude baki yace
"Haba Hajiya ko banida hankali dai ai kinsan bazan daki Umaimah ba, abune ya hadamu kuma taqi ta tsaya nayi mata bayani ta shiga haukanta da ta saba"

"Au mahaukaciya ma kake kiranta? Idan ma haukan ne ai a gidanka ta same shi kuma akanka takeyinsa" Hajiya ta fada tana harararsa seya bude baki kawai yana kallonta ya kasa cewa komai, gaskiya kuma son zuciyar Hajiya ya wuce misali, to ko Umaimah ta haifa bashi ba ai iyakarta kenan. Ganin idanma ya mata bayani ba fuskantar sa zatayi ba yasa ya miqe yana cewa
"Kishinta ne na banza ya tashi, kuma yarinyar da take haukan akanta ma data kwantar da hankalinta ba auranta zanyi ba" ya haye sama ya bar Hajiyar a zaune tana kallonsa.

Ajiyar zuciya ta sauke tareda miqewa, tunda take da Khalil baya iya ko kallon cikin idonta ya gaya mata magana sedai ya sadda kai amma yau shine ya tashi ya barta a zaune lallai dole akwai wani abu sata kasa fahimta anan. Miqewa tayi a sanyaye ta wuce inda Khalifa yake jiranta. Sun tarar da Anty, Nuratu se Anty Laure tareda ita wanda Khalil ya kira ya sanar dasu. Umaiman na barci har sannan tambayar Hajiya suke abinda ya sameta a taqaice tace musu itama bata sani ba, ta shigo gurinta a gigice shikenan kuma jini ya balle mata kuma shima Mijin yace haka yazo ya tarar da ita a qoqarin yayi calming nata ne ta fita da gudu zuwa gurin Hajiyar.
Chapter 139 · 0% Book details