← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 267

Sashe 49

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru yayi kawai yana kallonta, yanda take maganar har akan fuskarta yana iya karantar gaskiyar zuciyarta da kuma nadamar da tayi amma fa Umaimah ce, yanzu shi ai sedai ya bawa wani labarin halinta badai a bashi ba dukda haka yana fatan Allah yasa da gaske take ta gane gaskiya dan ya tabbatar da yafita Azabtuwa da wannan zaman da sukayi, kawai ya jure ne saboda ya nuna mata kuskurenta kuma Alhamdulillahi gashi nan yaci nasara amma dukda haka bazeyi saurin bada kai bori ya hau ba, dole ya sake shata mata wasu sharuddan in har Nadamar ta gaske ce kuma ta shirya suyi zaman lafiya zata bi.

Hannu biyu ya saka ya dagota daga durqushen har sannan bata dena tsiyayar hawaye ba, cikin palour ya qarasa shiga ya zaunar dasu akan kujera daya ya kama hannayenta duka biyu yana fuskantarta, kallon cikin ido yayi mata Umaimah dake kallonsa itama tayi saurin sadda kanta qasa, cikin kasalalliyar murya wadda halin da yake ciki da kuma Dramar Umaimah suka haddasa masa yace mata

"Look at me Umaimah, i want you to look in to my eyes while I'm talking. Bana so kice baki ji ba ko ki manta wani abu da zan fada".

Hannunta ta saka ta share hawayenta kafin ta dago idanunta da suka canza kala saboda kuka ta kalle shi itama, a tare suka sauke ajiyar zuciya, ya matsa hannunta dake cikin nasa yace

"Ina sonki Umaimah irin son da bazan iya misalta miki shiba amma a kullum halayyarki tana goge wani kaso daga cikin son da nake miki, Umaimah yazo Mana a cikin Hadisi Manzon Allah SAW yace 'Jublatul qulubi ala hubbi man ahsana ilaiha, wa bugudu man aasaha ialihi'. Ita zuciya da kike gani an halicceta akan son me kyautata mata haka kuma tana qin duk wanda yake munana mata ko dabba ki ka kalla yafi zuwa gurin wanda yake bashi abinci yake kyautata masa ballantana mutum.

Ina tsoron kar wata rana a waye gari tarin soyayyar da nake yi miki ta shafe gaba daya saboda a kulle halayenki marasa kyau suna rinjayar na kirkin akan sikelina.
Soyayya ita ce gadar da take kaiwa ga aure amma kyawawan dabi'u su suke zaunar dashi kuma girmamawa da mutunta juna dolene a cikin aure bawai zabi bane.

Idan ma wasu kike kwaikwayo ko suke doraki akan hanyar da bazata bulle ba qarshe zakiyi batan baqatantan babu nan babu can dan haka tun wuri ki farka dan nasan wannan ba tarbiyyar gidan ku bace, ba itace tarbiyyar da nayi sha'awa har ta kaini ga auranki ba ce wata ce daban kika aro a gurin wadanda suke zama irin zaman bariki, mace ta zagi mijinta idan ta kama ya daketa kuma gobe suci gaba da zama har suyi dariya toh ni bazanyi irin wannan zaman dake ba, idan kuma shi kika zaba kamar yanda kika gani a yanzu na fara zan fita daga sabgarki in barmi kiyi rayuwarki ke kadai nima nayi tawa saboda hakan ze fi samar mun da zaman lafiya da kwanciyar hankali".

Cikin nutsuwa da kwantar da murya yake maganarsa ta yanda duk taurin kan wanda akeyiwa seya saurara kafin ya gama kuwa jikin ta qaura yayi la'asar liqis ta sunkuyar da kai qasa kamar gaske tana matsar kwalla.

Qara kama hannunta yayi yaci gaba da cewa
"Dan Allah Umaimah ki kwantar da hankalinki mu zauna lafiya kamar kowanne ma'aurata. Wallahi banida burin sake sako wata mace a cikin rayuwata bayanke, inasonki, ina son komai naki yayi mun irin macen da nake so na qare rayuwata da ita idan kika cire Jidalinki shikadai ne fargabata a kullum na aure ki saboda ina sonki ina son zama dake amma sam kin gaza bani kwanciyar hankalin da nake kwadayi a tare dake.

Idan naji dadinki na kwana daya se nayi fama da tashin hankalinki na sati a haka kike so na zauna dake ke kadai?
Idan aka ci gaba a haka baki tunanin wata rana zan nemi inda zan ringa samun nutsuwa da kwanciyar hankalin dana rasa a tattare dake?
Umaimah kwalliya, girki, gyaran gida ko gamsuwa a gado ba su kadai ne jindadin aure ba da akwai Nutsuwar zuciya wadda duk irin jin dadin da kake ciki idan baka da ita bazaka taba samun yanda kake so ba daga ni har ke abinda muka rasa kenan kuma kece sila.

Kullum zuciyarki da tunaninki yana kan kar wata ta kulani karna kalli wata, idan akasi ya gifta wani abu ya faru kin ringa tashin hankali kenan kina bori duk akan me azatonki hakan ne ze hanani kula mata ko qara aure duk sanda naga dama? Toh ki sani wannan halin naki tamkar kina ingizani ne zuwa ga wasun kuma duk ranar da kika kaini qarshe sedai kiji ana cewa ki matsa za'a shigo da Amarya idan yaso ki kashe mu duka kamar yanda kika sha fada kinga munyi shahada ke kuma kinyi dakon zunubi dan babu wanda ze hanani qara aure idan na tashiyi hujjar tayar mun da hankali kadai da kikeyi kullum ta isheni in qara aure kuma kowa ze goyi bayana da babu wanda besan Halinki ba idan kika cire Hajiyata amma kowa yasan Umaimah danja ce duk abinda akace kinyi za'a yarda da wanda yafishi ma duk saboda me"

Kuka ta fashe dashi me sauti tana kallonsa, idan yasan irin wutar da take ruruwa a zuciyarta da be fara kawo zancen qarin aure ko makamancinsa a hirar su ba, amma ya zatayi ko wutar zata cinyeta yau dole ta hadiye kodan ta samu su sasanta dan ita da kanta bangaren kwakwalwarta me hankali ya mata karatun ta nutsu kuma ta yarda da duk abinda yake fada za kuma ta zage dantse in Allah ya yarda kwanciyar hankali ya samu gurin zama a gidansu tunda dai yace tijararta bazata hana ya mata kishiya ba toh kuwa zaman lafiya ze hana.

Cikin kuka tace masa
"Duk naji na kuma karbi laifina ina roqonka daka yafe mun bana so Allah ya kamani da laifin bata maka rai"

"Ni ban taba riqeki a zuciyata ba, a kullum ina miki addu'ar Allah ya shiryaki yasa ki gane abinda kikeyi ba daidai bane kuma duk abinda kikayi mun na yafe har wanda ma bakiyi ba kafin yazo na rigada nayi clearing nasu" ya fada yana dan murmushi da sake janyota jikinsa.

"Nagode, kuma ka gaya mun duk abinda kake so na dena zan bari indai hakan ze saka ka huce kuma kayi farinciki" ta sake fada tana shigewa jikinta, seya dora bakinsa akan kunnenta ya sakar mata kiss me qara da seda ta zabura ta kalleshi tana bata fuska, shima bata fuskar yayi yace

"Wannan Chatting din dayake dauke miki hankali bana sonsa, bance ki dena kwata kwata ba amma kisan yanda zaki raba lokacinki ya zamana kinada lokacina dana sauran ayyukan da suke a gabanki ba danna waya ba"

"Se kuma me?" Ta fada tana kallonsa, ya daga kai kamar me tunani sannan yace
"Shikenan".
Wayarta ta janyo ta bude, Khalil ya tsaya yana kallonta ta shiga cikin WhatsApp kai tsaye tayi deleting account din kafin tayi uninstalling nasa gaba daya daga kan wayar ta miqa masa tana cewa

"Gashinan na goge gaba daya ma saboda kar na barshi ya ringa dauke mun hankali"

"Nifa bance ki goge ba, idan kuma ina so muyi video call in bana nan fa ko zaki turamun da pictures.."

"Nidai bana so tunda dai baka sonsa, shikenan mun shirya ko?" ta fada cikin shawagwaba bata ida maganar ba Ya saka hannu biyu ya kama qugunta ya qara matsota jikinsa sosai kafin ya shiga aika mata da kiss cikin kwarewa, ya kwashe kusan minti goma yana kissing nata kafin ya saketa jikinta yayi mugun sanyi saboda wata fitinanniyar kewarsa data taso mata.

"Yunwa nakeji, tunda na shigo nake jin qamshin abinci me kika dafa" Khalil ya fada yana janyewa daga jikinta kamar beyi komai ba dukda shikansa qarfin haline kawai ba amma ba qaramin ruwa ya kunnowa kansa ba, kuma yana gudun ciwon daya ji mata kwanaki ya warke koda saura.

Kukan sangarta ta saka masa ta fada jikinsa tana qoqarin sake hade bakinsu ya riqeta yana cewa

"No Umaimah bakida lafiya kuma Dr tace se kinyi two months kina hutuwa" ya fada harga zuciyarsa dagaske ya dauka se tayi wata biyun kamar yanda likita tace dan ya tsorata da hukuncin nasa ya kuma yi nadama da alqawarin baze sake hakke mata yana cikin fushi ba.

Kamar zata shige masa ciki ta qanqameshi tana cewa
"Ni na warke ka duba ma ka gani, please Ibbah i miss you badly" ta qarsa tana hade bakinsu ta shiga bashi haddar karatun daya dade yana dora mata

"Innalillahi yarinyar nan zata kasheni" Khalil ya fada a zuciyarsa jin Umaiman tasa tana masa wasu abubuwa da ko a hasashe be taba zaton ta iya su ballantana tayi masa, ashedai ba Jidali kadai ta iya ba ita din ta kowanne fanni gwanace.

Dakyar suka rabu shima seda sukaji an kwada kiran sallar Magriba a masallatai. Kallonta kawai yake yana sakin murmushi kamar wani wawa dan kuwa yau din ta shayar dashi mamaki ba kadan ba. Ita ya sakarwa filin tayi sukuwa son ranta soyayya iri iri babu wacce be gani ba seda komai ya lafa kuma ta juya ta hade da kujera yanda kasan wadda Siriki ya rutsa.

"Wai dan Allah Babe course kika je kikayo ne ko yaya ni bangane wannan al'amari ba ya daliba take neman tafi Malamin hazaqa ne?" ya fada yana kama qugunta tareda leqa fuskarta data kife a kan kujera, seta zabura saboda yanda taji ruqon nasa har tsakiyar kanta ya kwanto ta jikinsa gaba daya yana shafata yace

"Kidena zabura haka fa kina mantawa bake kadai bace yanzu ko?"
Kwacewa tayi ta yayimi Rigar shaddar daya cire ta rufe jikinta, ta dai fi babu ta miqe tsaye Khalil kuwa qara kwanciya yayi yana qare mata kallo yanda Albarkatun jikinta suka qara cika taf gaba da bayan nan masha Allah a fuska ne kadai zaka ga ramar da tayi, tafiya tayi kamar zata kife yayi saurin ruqota ta sakar masa harara tana cewa
Chapter 49 · 0% Book details