← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 248 OF 267

Sashe 248

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta sunkuyar da kai qasa wai ita Mama ba zata bar wannan maganar ba se tonata takeyi sannan ita ba zata iya fada mata abinda ya hadasu ba, ai ta tababta seta gwammace fushin Khalil akan Mama taji wannan labari.
"Shikenan bari na kira Hajiya Aishar na gaya mata, ai baya koroki gida da tsohon ciki ba kuma tana gidan koma menene ai da gabanta ya kamata ku fara zuwa" Maman ta sake fada tana miqewa se Humaira ta marairaice mata danba zata manta ba yana yawan jaddada mata duk abinda ze hadasu komenene ta tunkareshi kai tsaye ta gaya masa, baya so takai qararsa gurin kowa musamman Hajiyarsa idanbata fada mata Alkhairinsa ba toh karta kuskura tayi masa lamba a gurinta dan shima baya kai qarar Mace gidansu danta masa abu, a ranta take ayyana qila Maman Mu'ayyad haka ta ringa masa shiyasa yake ja mata kashedi.

"Ayya Mama dan Allah kiyi haquri karki kira Hajiya, na gaya miki zezo daya huce wlh koba yau ha gobe da safe zaki ganshi inma kiran kike so to shi ki kirashi ai shiya koroni ba Hajiya ba" Ta fada tana riqe hannun Maman, seta maka mata harara tace
"Naqi na kirashin ita zan kira tu da ba zaki gaya mun abinda kika masa ba ai kinga seki fada a gabanta"
"Dan Allah Mama karki kiraya wlh fushi ze qarayi ya gaya mun baya so ina kao qarar sa gurin kowa shima baze kai tawa ba"
"Idan bekai qararki ba ai gashi ya koroki gida qarewar qara kenan ni raina ya baci ni kadai ko to sedai mu raba da uwarsa daga nan a tantance koma wacece me laifi a bashi yawwa" Mama ta fada tana ficewa daga dakin.

Tsaf ta tsarawa Hajiya zuwan Humairan da kuma yanda sukayi da ita, Hajiya ta ringa salallami tana cewa
"Shiyasa yau najita shiru kuma yanaji inata jajenta amma yayi muqus ya shigo tun Azahar yace mun baya jin dadi ko aiki be fita ba a bakin yara ma naji bata nan itana da suka dawo daga makaranta, dan Allah Hajita kiyi haquri yanzu kuma zan taso shi yazo ya maidota ai na gaya masa nice uwarta duk abinda tayi amsa kafin ya kaiwa kowa kukanta ya gaya mun shine ze turata gida saboda ya nuna mun ban isa ba zamu gamu duk baqin ran da yake ji dashi kwana biyu ina sane dashi zan kumayi maganinsa"

"Aa Hajiya ba'ayi haka ba be kamata ayi masa dole ba tunda bamu san me ta masa ba har ya turota gidan danita ma da kike ganinta ja'ira ce ta gaske kawai dai na sanar dake ne dan kisan abinda ake ciki tsakaninau kuma mu zuba ido harsu daidaita dan kansu ba shikenan ba" Mama Hauwa ta fada, Hajita ta dage se yazo Mama Hauwa ta dage akan kar a taso Khalil ta barshi dakansa idan yayi niyya zeje sannan ta qara da cewa
"Kuma dan Allah karkice zaki masa fada Hajiya tunda taqi fadar abinda ya hadasu na tabbata ita ce bata da gaskiya" daga haka sukayi sallama.

Jalilah dake maqale a gefen Hajiya tana jin abinda suke cewa ta tafa hannaye tana cewa
"Ahaf, ai wlh nasan se an rina. Wannan shige da ficen da yara suke tsakanin gidannan da nasu ni nasan swta qullo abinda ta saba ta aiko su dashi to kuwa tayi kadan dataga bayan Khalil da matarsa duk mugun abun da tayi ya koma mata wlh". Hajiya tayi sakato tana kallonta tace
"Ke kuma dawa?"
"Tsohuwar matarsa mana, ko kaffara bazanyi ba idan na rantse cewar ita ta saka musu hannu. Daman bana gaya miki ba ashe turo yarta takeyi ta sashi gabada tambayar wai yaushe ze maidata daman an tura masa yar azuciya kina kallo duk abinda ta fada ya zauna haka zeyi mata to wlh bata isa ba yanda ta bar gidan nan ta bar shi har abada alfarmar Annabi da Alqur'aniduk kuma wani qulumbotonta sedai ya koma mata" Jalilan ta fada tana hura hanci Hajiya ta saka ido tana kallonta kafin tace

"Kardai ki daukarwa kanki nauyin da ba zaki iya saukewa ba haka kawai zakiyi mata Qaharu kina da shaidar da zaki bayar akan ita tayi musu wani abu? Ko a baya da kike babatun zancenki idan ance ki bada shaida baki da ita zatone kawai kuma babu kyau dan haka bana so karna kuma sake jin kinyi magana makamanciyar haka, abinda ya rigada ya faru Allah ya tsara faruwarsa tilas seya kasance hakanan rabuwar Babana da Umaimah daga Allah ce yanda tazo ba a dadin rai ba kawai shine abinda ba'aji dadi ba".

Hangame baki Jalilan tayi itama tana kallon Hajiya kafin ta sauke ajiyar zuciya tace
"Yanzu Hajiya duk bayan abinda tayi miki tayi masa shima har zaki iya kare ta idan an fadi aibunta? Umaimah ce fa Hajiya kin manta tarin haqqoqin mutane da ita ta diba har kike cewa karna dauki haqqinta?"

"Ita dinfa Umaimah ina sane, bari kiji Jalilah har gaban Ubangiji na yafewa mata duk abinda tayi mun kuma ina mata fatan abinda ya faru ya zama darasi a rayuwarta ta gaba, meya ragu a jikina bayan abinda ya faru? Sannan shi dan uwan naki ya fasa rayuwa ne ko kuwa wata nakasa ta sameshi? Duk abinda ya faru babu laifin kowa qaddararmu ce a haka kuma mun karbeta bamu da ja akan hakan" Hajiyan ta sake fada se Jalilah ta miqe tana cewa
"Babu shakka Asirin data miki har yau he sake ki ba ko kuna an sake ninninkashi, to wlh ko da buzun baqin Jaki take tsafi tayi kasan a wannan karon kuma mu bamu yafe Tozarta mana Mahaifiya da lahantana mana Dan uwa da tayi ba Allah ya isan mu kuna se Munyi shari'a da ita a gaban Allah sannan wlh muddin wani abu ya sami auransa seta gane kurenta" tana gama fada ta fice daga falon a fusace Hajiya ta bita da kallo tana cewa

"Allah ya shiryaki Jalilah, Allah ya sanyaya miki zuciyarki ya azurtaki da yafiya ya yaye miki qullaci".

Jalilah kuwa na fita bangaren Khalil ta wuce suka ci karo a hanya yana fitowa ran nan a hade saboda tunda ya dawo da rana abinda ya gani yake damunsa. Gaba daya zuciyarsa ayyana masa takeyi da gangan ta fita saboda tana so su hadu dashi dukda be kawo wata Alfasha a tsakaninsu ba amma zuwan da tayi yayi bala'in yi masa ciwo akan me? Me take nufi da take so lallai seta ringa haduwa dashi? Tunda tasan baya so kuma tayi masa alqawari akan me zata bari harya kama hannunta yana shafawa har wani murmushin jin dadi yakeyi Allah kadai yasan abinda yake ayyanawa a zuciyarsa.

Jalilah ta girgizashi ganin ya zuba mata idonsa da suka kada sukayi jaa saboda tunanin daya tafi tana cewa
"Nema take ta zautar dakai ma kenan to wlh tayi kadan, idan tana taqama da Boka mu da Allah muka dogara kuma se munga qarshenta". Rintse idonsa yayi saboda yabda take maganar a sama kansa kuma yana sara masa, da muryarsa dake nuna bacin ran da yake ciki yace
"Ke kuma hayagagar me kikeyi haka keda nakya rabo da abin magana?"
"Zakace haka mana tunda ina shiga Al'amuranka muna murna mun rabu da kaska ashe tana can tana jiqo mana aiki, sake kayi da addu'a shiyasa har ta taradda kai kenan ka bari abin yayi tasiri a ranka ka kori matarka to wlh tayi kadan duk kuma shirinta nata dawo baze tabbata ba in zaka miqe da addy'a ka miqe dan wadda muke maka ba isa zatayi ba naga alamar hatsabibancin ta gaba ya sakeyi ba baya ba tunda har ka fara tafiya kana tunani ba tareda kana ganin hanya ba".

Tsaf ya fahimci inda maganarta ta dosa sharrin da kullum takewa Umaimah ne na cewar Asiri take masa shi kuma yace mata idan Umaimah batayi asiri ba ita ta tafi lahira da tulin laifin Qazafin da take mata ai. Yanzun ma Tsaki yaja me qarfi ya rabeta yana cewa
"Ki bar mutum yaji da abinda ya dameshi dan Allah ba wata Umaimah ba, ke take a gabanki shiyasa har kika kasa mantawa dacita shekara hudu kullum se kinyi zancenta" tayi sakare tana kallonsa harya shige part din Hajiya kafin ta juya tana cewa

"Maganina kenan danake shiga sabgar wanda besan mutunchin kansa ba, su Maza daman macen da zata tijara su taci musu mutunchi ita sukewa naci, me biyayya da kwantar da kai itace shararsu ai shikenan idan ta dawo ta qarasa abinda ta fara randa ka farka ka ganka a kabari ka kiyayi Umaimah" ta ringa sababi harta fita saga gidan Sammani na mata Allah ya tsare bata ma jishi ba.

Khalil kuwa yana shiga falon Hajiya ta rufeshi da fada,
"Saboda ban isa ba Khalil ina cikin gidan nan ka tura matarka gida se uwarta ce ta kira take gaya mun ko? To ka kyauta kuma yanzu zaka tashi kaje yanda ka turata ka dawo da ita dan ni ba butulu bace bana manta Alkhairi. Yanda Yarinyar nan da iyayenta sukayi mana Halacci bana tsammanin ko Dukanka takeyi zaka ce ta tafi gida ballantana akan abinda na tabbata bekai ya kawo ba".

Ransa yayi bala'in baci, wato Qararsa ta kawo gurin Hajiya bayan yasha jaddada mata baya so. Irin halin Umaimah zata dauka kenan, su guma masa sannan su hadashi da mahaifiyarsa tayi masa fada toh kuwa zata gane kurenta, ya dena shiru cutar da kansa da ya ringayi lokacin Umaimah yanzu ya gane kuskurensa kuma baze maimaita ba duk wadda ta masa abu seya fada idan yaso ran kowa ya baci. A fusace abinda tayi masa yana sake tunzurashi yace
"Hajiya baki san meta mun ba, turata gidan kawai shine maslaha idan na huce zan dawo da ita"
Chapter 248 · 0% Book details