← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 262 OF 267

Sashe 262

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama kanta ta shiga damuwa tunda ta shaida mata bata samunsa a waya idan ta kira baya dagawa har seda ta yiwa Abba maganar a cewarta ko ze tuntubi Alhaji Zakari yaji lafiya kar aje wani abun ne ya sameshi basu sani ba yace mata babu komai, ya tabbatar idan da wata damuwa kafin ma su tuntuba zasu sanar dasu su zuba ido koma menene Allah ya shiga ciki kawai.
Ranar Juma'ar data kama sati daya cif daya kamata yazo din da daddare tana kwance a daki Abba ya kirata a waya yace taje falonsa ta sameshi ta zura Hijabinta ta tafi tana shiga gabanta ya fadi saboda yanda ta taraddasu jigum jigum ta samu gefe ta zauna tana gaishe da Baba Abdullahi da Baba Liman. Baba Liman din ne yayi magana cikin sanyi yace mata

"Yanzu waliyyan Abdulwahabu suka tashi daga nan kuma sunzo bamu haquri ne akan cewar Dansu ya janye daga neman auranki bisa wasu dalilai sannan sunce mu baki haquri a madadinsa yace yana jin nauyinki dalilin dayasa ya gaza daukar wayarki kenan dan haka kiyi haquri ki kuma yi addu'a Allah yasa hakan ya zame miki Alkhairi daman Allah yayi ba mijinki bane shidin kinga babu yanda za'ayi"
"Yo haqurin me zaka bata kuma ai daman duk wanda ya siyi rariya yasan zata zubda ruwan mugun halinta da abinda ta aikata a baya sune suka koma kunnensu har yasa suka hana dansu auranta ba wani abu ba daman kuma ai za'a rina, a zamanin nan ka shuka Alkhairi ma yaka qare ballantana kayiwa kanka mugun tabo? Ai keda aure dai yanzu sedai ki samu Dattijo irinmu wanda bashida me sakashi ko ya hanshi amma badai Matashi me jini a jika ba dan babu dan da uwarsa take raye da zataji abinda kikayiwa Halilu da uwarsa ta bari a auro ki cikin Ahalinsu" Baba Abdullahi ya amshe, kanta na qasa wani qululu daya taso mata tunda Baba Liman ya fara magana ya tokare mata wuya, sam ita maganganun Baba Abdullahi basu bata mata rai ba dan tuni ta haddacesu sedai idan basu haduba cinmutunchi se wanda ya manta ne baya mata.

Abba ne ya dakatar dashi jin ze cigaba da tijarar tasa yace mata
"Kije, karki saka damuwa a zuciyarki kinji kullum muna yi muku Addu'a da fatan Alkhairi a rayuwa komai ya faru da sanin Allah kinji"
"Toh Abba" ta fada muryarta na rawa kafin ta miqe ta fita daga falon. Bata tsammaci zataji ciwon fasa auranta da Abdulwahab yayi har haka ba, ita bata ma san tana sonsa ba se yanzu da wannan abun ya faru ranar kwana tayi tana sallah tana Addu'a tana kuka gwanin tausayi. Meyasa Abdulwahab zeyi mata haka? Dayasan ba auranta zeyi ba meyasa ze bata mata lokaci har ya bari ta sakashi a ranta meye ribarsa yanzu akan abinda yayi mata kenan ya bata lokacin sa da dukiyarsa a banza alhalin ba auranta zeyi ba duk a na me?

Hankalinta be qara tashi ba seda magana ta shiga yawo a unguwa, batayi mamakin yanda akayi zancen auranta da fasuwarsa ya bazu ba tunda da Alhaji Zakari akayi komai tasan kuma ko a bakin matansa maganar zata fita amma abinda aka ringa yawo dashi ana jifanta dashi yayi mugun tabata da har seda ta kwanta jinyar data qarawa magauta hujjar yamadidi da ita a gari cewa akeyi tayi cikin shege abinda yasa Abdulwahab ya fasa auranta kenan, yanke jiki tayi ta fadi lokacin da Yasir ya shigo yana maida musu da abinda yaji a Unguwa ana fada, da yammane, Masu zaman banzan unguwa sun kafa majalissu aka fita da ita Asibiti ranga ranga tuni labari ya chanza salo cewar gata can tasha maganin zubar da cikin an tafi Asibiti da ita harda masu cewar Jini har qofar gida sun ma gani da idonsu kai maganganu dai kala kala masu fadar dama sun sani kullum da motar da take zuwa gurinta aikin da akace tana zuwa ma duk qaryace kawai fakewa take da yawon ta zubar ba wani abu ba.

Bata taba zaton haka sharri yake da ciwo ba se daya fado kanta, tayi kuka babu iyaka har idanunta suka soye zuciyarta ta qeqashe, ta ringa tuna Hadiza ita da ba iya unguwa ba Nigeria gaba daya babu inda hoton batancinta be zaga ba har yau bata fitar da ran hotonta na kan yanar gizo da batancin da tayi mata ashe haka taji? Tabbas irin Hadiza basu da yawa a duniya, ta yafe mata abinda tayi mata gashi Allah ya saka mata cikin ruwan sanyi ya jarabceta da abinda ta jefeta dashi, idanta kalli irin quncin da Abba da Mama suka shiga akan wannan sabon Al'amari hankalinta na matuqar tashi batayi musu Adalci ba. A kullum burinsu su faranta mata sannan tayi musu sakayya da bacin rai. Ita ta fita zakka a yayan da suka haifa Maza da mata babu wanda za'a daga a kawo wani aibunsa se take kullm cikin janyo musu magana take.

A wannan karon seda akayi dagaske kafin nutsuwarta ta daidaita, ciwon damuwa ya nemi kamata ta dena fita dan duk inda tayi nunata akeyi ana cewa tayi cikin shege ba ita ba Mama kanta seda ta dena zuwa taro a unguwar saboda yanda ake zundenta duk inda ta shiga saboda Umaiman, ance tana zaune shekara bakwai Ashe karuwancinta kawai takeyi se yanzu da ta samu Miji Asirinta ya tonu, Addu'a da tawakkali yasa suka cinye wannan jarabawar har masu surutu sukayi suka gaji rayuwa taci gaba da tafiya a yanda take. Yanda Abdulwahab be nemeta ba itama bata sake nemansa dan taji dalilinsa na fasa auranta ba, tasan dai koma menene yana da alaqa da rayuwarta ta baya haka ta sake fawwalawa Allah komai taci gaba da aikinta zancen aure ya sake fice mata daga rai saboda duk wanda zezo badan Allah bane se kuma Dattijai irin su Baba Abdullahin masu mata uku da yaya bila Adadin. Maman da take matsa mata da zancen auran ma ta haqura tana mata addu'a dan haka ta aje komai ta rungumi aikinta da sana'ar siyar da turaran wuta data fara dalilin na auran Abdulwahab da tayi, suna da yawan gaske sunfi qarfin tace zata ajiye ta ringa amfani dasu ita ba Gida ba ba Miji ba Maman Asad ce ta bata shawarar siyo container ta zuba su gwada tallatawa dan Turaruka ne masu kyau da Inganci tayi ai kuwa Allah ya saka mata albarka a sana'ar sosai take samun Alkhairi a ciki.

Rabuwarsu da Abdulwahab da kusan wata shida kamar daga sama Allah ya sake hadata da Alhaji Kabir taje kasuwar Sabon gari siyo Mai da sabulun wanka suka hadu a shagonsa tayi siyayyar babban dan kasuwane dan shagunan sa sun kai biyar a cikin kasuwar yana ganin Umaiman ya rikice nan duniya yace shi yaga mata, daya daga cikin yaransa yace ai ya santa unguwarsu daya, shi ya bashi labarin abinda ya sani game da Umaiman Alhaji Kabir yace yaji ya gani dan irinta yaie ta nemi tuntuni abinda ya hanshi qara aure kenan. Shiya kaishi gurin Umaiman, Matarsa daya da yara biyu babban dansa Sa'an Iman ne. Shekarun sa talatin da takwas ya bata shekara uku kenan Nasibin rayuwa daya samu da kuma kamala ta yan kasuwa yasa ake ganinsa kamar wani babba ita kuwa tunda ya sanar mata da shekarunsa ta rainashi, gurinta shekaru uku sunyi kadan tsakananinta da Mijin da zata aura musamman a matsayin da take yanzu. BTa bashi fuska ba dan tun a zuwan farko ta nuna masa cewar yayi haquri ita ba aurene a gabanta ba amma ya nace.

Kiran waya kamar maye haka idan bezo yau ba gobe zezo tun tana shareshi harta haqura ta fara kulashi musamman da kowa yake ce mata tunda tana addu'a ta saurareshi ta yuwu Alkhairin da kowa yake roqar mata ne yazo. Abba da kansa yayi mata magana saboda nacin Alhaji kabir din yayi yawa kuma a yanayinsa mutumin kirki ne ga ladabi idan ya bazo babbar rigar nan tasa har Yasir girma yake bashi autan gidan gaba daya wadannan abubuwan suka saka dole ta fara sakar masa fuska tana qoqarin ganin sun fahimci juna a sannu har maganar aure tayi qarfi a tsakaninsu a wannan karon bata maimaita kuskuren da tayi lokacin Abdulwahab ba. Da kanta ta bashi labarin duk abinda ya faru a baya cikin tsantsar nadama da dana sanin da fuskarta ta gaza boyewa, Mamaki ta kusa kasheta sanda yake ce mata yaji komai hatta da sharrin ciki da aka mata ya sani kuma shi wadannan dalilai ma suka qara masa sonta har yake son auran nata a maimakon taji dadi se abin ya shiga bata tsoro. Ya za'ayi yace shi komai da tayi burgeshi yayi hakan nema yasa ze aureta anya qalau yake kuwa? Ko ita a karan kanta tasan halintavna baya bame kyau bane kuma idan da ace wata ce take da wannan Halin wanda ta sani ze aureta zata hana. Addu'a ta sake tsanantawa a kan lamarin, babu wani shiri da tayi wannan karon dan gani ta ringayi kamar shima auran bame yuwuwa bane yan uwansa zasu hana kamar yanda daga baya ta samu labari a bakin Hadiza cewar Hajiyarsu Abdulwahab dince ta hanashi auranta bayan uwargidan Alhaji Zakari taje qafa da qafa ta bata labarin gaskiya da qarya daya faru itace kuma ta kafa masa sharadin ko sake waiwayar Umaiman yayi bata yafe masa ba, wata biyu kenan daya auri diyar Alhaji Zakarin yanzu ita bata ma san shi ta aura ba seda Hadizan take gaya mata shiyasa take taka tsan tsan da Kabir kar shima iyayensa suji wani abu daga baya suce zasu hanashi auranta sedai kamar yanda akace Al'amarin aure da Mutuwa daya suke idan lokaci yayi babu fashi se gashi cikin hukuncin ubangiji ranar wata Juma'a aka daura auran Umaiman da Kabir auran da yazowa mutane da yawa a bazata irinsu Khalil dan ba'asan da labarinsa yinsa ba.
Chapter 262 · 0% Book details