← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 267

Sashe 22

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wallahi Khalil ina sonka, idan kace zaka barni rayuwata zata shiga cikin garari, zan iya rasa raina idanka rabu dani saboda na rigada na saddaqar maka da ruhina. Nayi maka alqawari zan zama me maka biyayya bazan taba tsallake umarninka ba, bazan sake tayar maka da hankali akan wani abu ba zan shanye komai saboda farin cikinka koda hakan yana nufin yankewar numfashi na saboda na sani wata rana kishinka ze iya zama ajalina" Umaimata sake fada cikin wani irin kuka me tsuma zuciya da ya saka jikin Khalil daukar rawa, a maimakon ya samu nutsuwa da  kalamanta sema qara shiga rudu da tashin hankali yakeyi, tabbas yana son Umaimah ko yace yana Qaunarta, amma ita a nata bangaren wannan ya zarce Love sedai a kirashi da Obsession.

"Umaimah ki dena kuka haka, kiyi haquri amma bana tunanin zamu rayu tare, wannan tsananin kishinda kike dashi a kaina ze iya zamar mana tangarda a cikin rayuwar auranmu saboda a kullum zuciyarki zata ringa raya miki abubuwan da ba haka suke ba, kinga kuma ke yanda kike handling bacin rai, bana so muyi abinda wata rana za muzo muna dana sani.
Ina sonki amma bazan iya auranki ba, Kiyi haquri muyi Addu'a Allah ya hada kowannen mu da Alkhairinsa" Khalil ya sake fada abinda ya janyo tsayawar ji da tunanin Umaimah na wani lokaci, sedata kwashi kusan minti biyar shi kansa A nasa bangaren seda Numfashinsa ya rage sauri na wasu sakanni kafin yaci gaba, jiran amsa yake daga bangarenta amma yaji shiru, har ya yi tunanin ko Network ne ya dauke yaji yo ta tana magana cikin wani irin sauti me kama da wadda kw komawa da numfashinta tace

"Khalil daman ka shiga rayuwa ta ne saboda kaga bayana? Waya turo ka? Me nayi wa wani daya zabi hukuntani da irin wannan hukuncin me tsanani, kasan yanda Sonka ya yi wa zuciyata illah? Ka qaddara a ranka Khalil tunda na rasa ka babu wata mace data isa ta rabeka, yanda zanqare rayuwata babu aure kaima haka idan kuwa har kayi gigin kula wata to tamkar ka siya mata tikitin tafiya lahira ne dan kuwa sena kasheta, muddin ina numfashi sena kashe duk wata Mace data shiga cikin rayuwarka.

Saboda ni aka halicce ka babu macen data isa ta ratsa zuciyarka bayan ni, idan kuma kana ganin wasa ne ka gwada Khalil, ka gwada kula wata mace wallahi sena ga bayanta" ta qarasa tana sakinwani siririn kuka daya saka Khalil zabura ya miqe dan tunda ta fara magana hankalinsa yayi qololuwar tashi, kafin yace wani abu ta kashe wayar.

"Innalillahi wa'inna ilahi raji'un" yake maimaitawa yana zagaye office din, dukda kasancewar Ac a kunne take amma zufa ce take keto masa ta ko ina kamar wanda yake naquda, wannan shi ake kira da anyi gudun gara an tadda zago. Shi daya ke neman rabuwa da ita saboda gudun tashin hankali gashi ya gayyatowa kansa babban tashin hankalin daya shallake na da.

Kisa fa take iqirarin yi akansa kenan shi kansa tasa rayuwar a cikin hadari take, idan har zata kashe wata saboda shi toh shine ze zama target dinta na farko kenan yanzu yaya zeyi? Meye mafita?
Zabi biyu gare shi a yanzu, kodai yayi jahadi ya auri Umaimah ya siyi tashin hankali da kudinsa ko kuma ya barta ta zama barazana ga rayuwar duk wata mace da ze kula, duk cikin wadannan zabin kuma babu wanda yake jin ze dauka dole akwai wata hanya bayan wannan, dole ya nemawa kansa mafita daga Tarkon Umaimah.

End of free page

Domin jin yanda zata kaya tsakanin Umaimah da Khalil Ku hanzarta biyan 500 dinku zuwa Asusun
8142548705
Opay
Maryam Farouk

Seku tura shedar biyan zuwa ga
07061838488

Yanzu ma aka fara wasan, Littafin Halin kishi yazo muku da sabon salo tareda tabo jigon da yake jijjiga mata a halin yanzu, ina me baku tabbacin bazakuyi nadamar bibiyar labarin Umaimah ba, kudai ku hanzarta biyan kudin karatun ku se naji ku 💃🏾💃🏾💃🏾

PROMO
PROMO
PROMO

BEFORE 4K NOW 2500

3968303018
ZAINAB SHU AIBU
FCMB
KITURA SHEDAR BIYA 👇🏻

08162859027

AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA

INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK DATTIN MARA CIWON MARA CIWON JIKI HANA HAIHUWA RASHIN NI IMA RASHIN JIN SHA AWA FITAR FARIN RUWA KAIKAYI KURAJEN PP DA NA JIKI JIN ZAFI YAYIN SADUWA FITAR FARIN RUWA MAI WARI BASUR KOMAI DADEWARSHI CIWON NONO

SHIRYE NAKE ZANYI MAKU PROMO SABODA WA ANDA BASU SHA BA SU ZO SU DA DANA MAGANIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID DUK LABARIN DA AKE BAKU GASKENA MAGANINA KANKAT NE KOBAKISHA KOMAI BA YA ISHEKI

*HALIN KISHI*
*(NADAMAR UMAIMAH)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

Page 11

Umaimah

Kuke take tamkar ranta ze fita ta kasa yarda wai Khalil yace ya fasa auranta, wai me yasa? Me takeyi wanda har suke kasa jurewa suke iqirarin bazasu iya ajiyeta a gidan su ba? Laifine dan tayi kishin abinda take so? Ita a ganinta ai abin Alfaharin namiji ne ma ayi kishinsa amma a maimakon ta burge se gashi hakan ya zamar mata kamar wani tabo da kowanne namiji ya tashi yake fakewa da shi ya gujeta.

"Wayyo Allah na na shiga uku zuciyata zata fashe" ta fada cikin kuka tana dafe qirjinta da take jin kamar ana hura mata wuta. Anty na tsakar gida tana suyar qosai har sannan tana mitar abinda ya faru ta kwallo mata kira akan tazo ta debi Abin karyawa kafin yayi sanyi, ta kirata yafi sau uku dan haka data tsame na kaskon seta miqe ta dauko plate da cup ta zuba mata komai ta wuce dakin tana cewa "Qila qafarce, a zafin nan ka qone ai dole mutun yaji jiki. Gaskiya dole ma a kaota Asibiti a duba ko bata tashi ba sa bata abinda zata shafa ya rage zugi" dai dai nan ta isa qofar dakin wanda tun daga wajen take jiyo nishi da kuka kukan da Umaimah takeyi tamkar me Naquda.

Cikin tashin hankali ta ajiye kayan kan mudubi ta hau jijjiga Umaimah dake kwance a qasa tana juyi fuskarta tayi kaca kaca da Jini da alama Habo tayi in banda wayyo wayyo babu abinda take fadi.
Na shiga Uku nu Saratu, Umaimah meya same ki? Alhaji" Anty ta kwala kiran Abba se gashi a firgice dan da qarfi tayi kiran kuma kanaji kasan bana lafiya bane

Yanda yaga Umaiman shi kansa hankalinsa ya tashi, bugun lugude zuciyarsa ta shigayi a ransa yana tunanin jinin daya gani a jikinta na meye? Kardai yarinyar nan nema tayi ta lahanta kanta akan rashin hankali?

"Alhaji ka kamata mu kaita Asibiti ka tsaya kana kallon mu" Anty ta fada cikin kuka, seya sunkuya ya dauki Umaiman cak ya juya ya fita, bin bayan sa tayi saboda rudewa ko mayafi bata saka ba seda ta kai qofa ta tuna da mai data bari a kan wuta gashi babu kowa a gidan kar kuma wani abun ya sake faruwa dan haka ta koma jikinta na rawa da kyar ta iya tattara hankalinta ta sauke Man gefe ta kashe wutar kafin ta rurrufe sauran kayayyakin ta figi Zanin data samu akan Igiya tayi waje jin An fita da mota.

Emergency aka karbi Umaimah, Abba, Anty da Salman da suka kawo ta se zarya suke a qofar dakin da take likitoci nata shige da fice amma babu wanda yace musu komai. Seda aka kwashi kusan Awa daya kafin wani likita ya fito fuskar sa dauke da damuwa ya kalli Abba yace "Bismiah Alhaji muje office ina son magana dakai"

"Dr a wane hali take? Zamu iya shiga mu ganta? Anty tasha gabansa tana tambaya, seya girgiza mata kai Alamar Aa yace
" Babu matsala hajiya munyi qoqarin ganin ta fita daga dukkan hadari yanzu munyi mata Allurar bacci ne wanda dakyar ta dauke ta shi yasa baza muso ayi wani motsi me qarfi a kusa da ita ba, idan ta tashi se ku shiga ku ganta".

Guri ta samu ta zauna tareda Salman Abban ya wuce shida likita, yanda ta shiga tashin hankali tamkar ita ta haifi Umaiman a cikinta, koda yake basu banbanta yaran, yanda Mama ta ja nata ta riqe kamar ita ta haife su dole itama ta cusawa zuciyarta irin wannan aqida duk kuwa da zuga ta yan uwa da qawaye harma da wadanda abin be shafa ba amma da ta toshe kunnenta gashi nan sama da shekaru Ashirin suna zaune lafiya idan ka cire qananan sabani da ake samu tsakanin ko wandanne yan Adam.

Suna da kyakykyawar fahimta da alaqa me kyau wanda kuma Maman ce ta assasa. Daman ita Uwargida itace bango, duk yanda ta tsara ta tafiyar da rayuwar gida haka ake dorewa koda kuwa ace an samu fitinanniyar Amarya indai Uwargida ta tsaya akan gaskiya da Adalci ana samun daidaito.

A office din likita bayan sun zauna ya dubi Abba yace
"Damuwa ce tayiwa yarinyarka yawa data haddasa wa jininta hawa, kuma idan abin yaci gaba bama fata amma ze iya shafar zuciyarta ko ta kamu da ciwon damuwa (Depression).
Amma Alhaji a shekarun ta wane abu ne ya dameta haka da har yake barazana da rayuwarta?"

Abba da tashin hankalin sa ya nunku, Umaimah keda hawan jini a yan shekarun ta da basu wuce Ashirin da daya? ba yanzu bazata samawa kanta salama a rayuwa ba kullum daga wannan matsalar ta kau wata zata kunno kai shi yama rasa abinda zeyi akan lamarin Umaimah.

Yanzu dai Alhaji zamuyi iya qoqarin gurin bata kulawar data kamata sauran aiki kuma yana gurinku, dole kuyi qoqarin sanin damuwarta domin a maganceta amma fa cikin rarrashi bada fada, Allah ya bata lafiya" Likitan ya sake fada kafin ya turawa Abban takadda dayayi rubuce rubuce akai yace yaje gurin biyan kudi da kuma pharmacy a karbi magani. Godiya yayi masa jiki a sanyaye ya tashi ya fita.
Chapter 22 · 0% Book details