← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 210 OF 267

Sashe 210

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A can gidansu Umaimah kuwa suna isa kowanne ya wuce dakinsa, cikin wani yanayi me ban tausayi Mama ta zube a tsakiyar falonta ta sake rushewa da Kukan daya tokare mata maqoshi, bata damu da kashedin da akayi mata yanzu a asibiti ba akan ta daure ta cire damuwa jininta ya hau sosai to ta ina ma hankalinta ze kwanta duk duniya babu wanda ze fahimci irin zafi da qunar zuciya da takeji se ko Abba wanda suka da matsayi daya dashi a gurin Umaiman. Yau a wayi gari a ce dan da ka haifa a cikinka ne ya zama taqadiri Umaimah bata kyauta wa kanta ba bata kyauta musu ba. Kuka takeyi tamkar ranta ze fita, tunani takeyi idanhar Khalil ya rasa ransa Umaimah ce sila daman ta dade tana fadar zata kashe shi basu taba yardar da gaske takeyi ba se yanzu domin irin dukan datayi masa a makasa ya nuna daman ta shirya yin hakan.

Maman Asad ce ta shiga falon da sallama tayi saurin wullar da jakarta ta isa gurin Maman cikin kukan itama ta dagota tana cewa
"Kiyi haquri Mama dan Allah ki dena kuka kodan saboda lafiyarki idan wani abu ya sameki mu ta shafa ita bata da Asara dan bata dauki kowa cikin Ahalinta da muhimmanciwani.ldan Allah Mama karki bari bacin ranta ya shafi lafiyarki ki barta kiy mata Addu'a Allah ya shiryeta idan tana da rabon shiriyar" suka hada kai suna kuka riris babu merarrashin wani Anty ta shigo fuskarta itama jiqe da Hawaye ta zauna tana cewa

"Hajiyayye keda zaki rarrasheta kuma se ki tayata kuyi dan Allah Kiyi haquri qaddara ce a rayuwa kowa da kalar tasa ina fatan kuma abun ya tsaya iya haka sannan hakan ya zame mata izina a rayuwa"

Seda sukayi me isarsu kafin kowa ya bawa zuciyarsa haquri yayi shiru. Dakyar Hajiyayye ta lallaba Maman tayi wanka tasha ruwan shayi da maganinta ta kwanta Anty Ma gurin Abba ta koma dan seda yayi wankan yasha shayi da magungunansa bacci ya dauke shi daman kafin ta fito gurin Maman. Mamaki ya kamasu ganin yanda yan uwa da maqofta suka ringa shigo musu Jaje, Maman Asad ta tambayi Anty Zee cousin dinsu da tazo tana ta kuka itama a bakinta taji wai a WhatsApp ta gani an tura da hoton Umaimah da Khalil din harda na Amaryar wai Uwargida ta kashe Ango saboda kishi a daren Angwancinsa.

A can Asibitin Malam kuwa bayan kammaluwar duk wasu gwaje gwaje daya kamata ayiwa Khalil din suka sake mayar dashi Asibitin Dr Al'amin zuwa sannan ya dan samu nutsuwarsa dukda dai baya magana kallon Likitocin kawai yakeyi da Khalifa da suketa kai kawo akansa har aka mayar dashi Asibitin bayan likitan ya fita ya kalli Khalifa dake zaune gefensa yace
"Ina Hajiya?"
"Tana nan an bata gado itama tun jiyan" Khalifa ya bashi amsa seya gyada kai kawai kafin a hankali ya sake cewa
"Humaira fa? Ina fatan babu abinda ya sameta"

"Lafiyanta qalau dan tana tareda kai se da zamu tafi AKTH ne bata bimu ba, bari naje gurinsu Hajiya na gaya musu mun dawo probably tana tare dasu" daga haka Khalifan ya miqe ya fita Khalil ya bishi da kallo a zuciyarsa yana hakaito abubuwan da suka faru a daren jiyan. Ajiyar zuciya yayi ya gyara kwanciyarsa gaba daya ji yakeyi daga qugunsa zuwa qafafunsa kamar ba a jikinsa suke ba, Umaimah ta cutar dashi ta nakasa masa rayuwa
A iya saninsa babu komai tsakaninsu se Alkhairi me yayi mata daya cancanci wannan danyan hukuncin daga gareta?
Ko ba'a fada masa ba yasan bashida sauran amfani a matsayin Da namiji ta kassarashi.

Tausayin Humaira me girma ya lullubeshi, idan da yasan jarabawar da zata afka masa kenan dabe tabata ba, dabe rabata da burcinta ya dora mata iddarsa ba haka kawai domin yasan dole ze haqura da ita ko yana so ko baya so baze cutar da ita ba ta hanyar zama da ita alhalin bashida ikon sauke mata haqqin da shi ya banbanta Matar aure da Marar aure. Zuviyarsa ta tambayeshi
Waya ce masa ya nakasa da har yake tunanin baze qara amfanuwa ba? Take ya bawa kansa amsa da tabbacin hakanne ba kuma ya buqatar wani ya gaya masa shi kansa a Jikinsa ya sani ya rasa lafiyarsa. Wasu hawaye masu dumi suka ziraro masa yayi saurin daukesu saboda qofar da aka bude. Hakiya ta shigo sauran yaranta da Yar uwarta biye da ita a baya tana ganinsa ta fashe da kuka ta qarasa gaban gadon ta kama hannunsa ta kasa cewa komai se Kuka takeyi abinda ya karyar da zuciyar sauran gaba daya suka saka kukan suma Khalil ne yayi qarfin halin cewa

"To kuma kukan me kukeyi bayan ba mutuwa nayi ba ai murna ya kamata kuyi tunda dai gani a gabanku a raye"
"Allah ya isa tsakaninmu da wannan shaidaniyar yarinyar, ranka ta nema da Allah yasa da sauran shan ruwanka a gaba gashi ka tsallake kuma in sha Allahu se taga sakayyar abinda ta aikata maka tun a duniya ba se taje lahira ba. Duk wahalar da kasha ta sanadinka da baqin cikin data qunsa mana se taga ninkinsu a kanta da yardar ubangiji seta qare rayuwarta cikin nadama mara amfani" Hajjya Maimuna ta fada cikin matsanan ci kuka se Khalil yayi saurin dakatar da ita yace

"Haba Mama ki dena magana haka ko babu komai Umaimah uwar yayana ce duk wata muguwar Addu'a da kikayi akanta zata iya shafarsu, ki nema mata shiriya a gurin Allah shi kadai ne abinda take da buqata"
"Ai Allah ba Azzalumin sarki bane babu ta inda zaluncin Umaimah ze shafi Ahalinmu sedai ma haqqin ubansu data dauka dasu kansu ya bibiyi rayuwarta. Allah dai ya kwashewa Umaimah Albarka kaikuma Allah ya baka lafiya abinda take baqin cikin wata ta mora sedai ta mutu dan tana Kallo zaka samu lafiya kaci gaba da Sasakar matarka tana zazzago maka Yaya" Hajiya Maimuna ta sake fada tana kuka dukda halin da suka ciki seda maganarta ta qarshe ta basu kunya Khalil ya sunkuyar da kansa qasa, ransa ya rasame yake ji akan abinda Umaimah tayi masa, ko kadan beji ya tsaneta ba amma abu daya ya sani koda ace ita kadai ta rage mace a rayuwa ya haqura da ita kuma har abada ze dawwa ma yana nema mata shiriya a gurin Allah domin ya yarda tana da lalura da kowa ya gagara ganewa.

UMAIMAH

Bayan Azahar ta farka, surutai da ta ringa yi cikin fitar hayyaci ya saka dole suka sakeyi mata wata allurar data dauketa har zuwa bayan Isha'i kafin ta sake farkawa a lokacin Anty da sauran yayyanta duk suna Asibitin. Daga yanda suke mu'amalantarta zaka tabbatar sunayi mata ne kawai Albarkacin zumunchi idan sukace zasu bi ta halinta babu wanda ze taka qafarsa yaje Asibtin gurinta. Iyakar bacin sunan data ja musu ya isa, a iya yau mutanen da suka je gidansu qafa da qafa da wanda suka kira a waya bazasu irgu ba duk akan Abinda Umaiman ta aikata. Labari nata yawo a gari anqara masa gishiri da maggi babu ta sigar da ba'a chanza zancen ba, wasu sunce ma har ana kamata tana hannun Yan sanda, wasu kuma suka ce yan uwan Mijin ne suka mata dukan mutuwa tana Asibiti a kwance masu son tabbatar da yanda akayi ne suka ringa binsu gida su dai babu wanda suka bude baki da sunan yiwa bayani daga gaisuwa shikenan idan mutum ya gaji da zaman gulmarsa ya tashi ya tafi. Daga Mama har Abba kuwa yini sukayi a dakunansu suna jinyar jiki data zuciya. Ruwan shayi kadai suka ringa iya kurba bisa tirsasawar Yayansu har kuma suka fita zuwa Asibitin a cikin Mama da Abban babu wanda ya sake tayar da maganar.

Jikinta yayi mata nauyin da ko bakinta ta gagara budewa tayi magana se binsu takeyi da kallo kawai, so takeyi ta tambayesu ina Khalil, ta tabbatar da yana raye ko kuwa da gaske ya mutu? Idan har ya zama Khalil ya mutu kuwa tasanbata da sauran amfani a duniya binsa zatayi. Seda Likita yazo ya sake duddubata ya tabbatar da komai normal kafin ya fita yana sake jaddada musuda su barta ta huta kar su sakata magana ko yin wani dogon yunquri Likitan na fita gaba dayansu suka miqe da niyyar tafiya. Babu wadda ta kula Umaiman a cikinsu haka itama ta rakasu da ido suka bar dakin Anty Hafsa ta rakasu a hanyarta ta dawowa suka hadu da Jalilah da Humaira sun dawo Asibitin suka gaisa babu yabo babu fallasa ta tambayesu jikin Khalil kafin ta juya jiki a sanyaye ta koma dakin da Umaiman take.

Kujera ta samu ta zauna ba taredata kulata ba itama, Umaimah tayi qarfin halin bude baki ta kira sunanta tayi mata banza seda ta sake maimaitawa kafin a hasale Anty Hafsan tace
"Karki kuskura kice zaki matsawa rayuwata saboda kin ganni anan, banda ina tsoron Allah ya kamani da laifin watsar da zumunchi da wlh Umaimah baki isa na sake kallon koda inuwarki ba, kiyi ta kanki kawai ni bana zauna bane saboda nayi hira dake ko wani Ahto".
Chapter 210 · 0% Book details