← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 267

Sashe 114

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana tafe yana cizon yatsa da dana sanin tsayawar da yayi gashi yanzu Allah kadai yasan inda suka tsere, wata nannauyar Ajiyar zuciya ya sauke daidai sanda ya shigar da motarsa gurin parking yayi arangama da Motar da yake bi. Gaggauce ya shiga ciki, ya ringa baza ido a reception ko ze gansu amma shiru seda ya biya kudi aka bashi muqullin daki ya shiga kafin tunanin kiran Yaya Aminu yazo masa. A taqaice yayi masa bayanin komai da kuma inda yake a yanzu Yaya Aminu ya bashi tabbacin zasu dauki mataki dan yanzu haka ma yana office be tafi gida ba saboda wani pending case da basu qarasa na.

Dakyar ya iya shan coffee a cafeteria dukda baqar yunwar da yakeji ya koma can bakin qofar gurin ya kafa ya tsare duk wani me shiga da fita akan idonsa har zuwa sanda Yaya Aminu ya sake kiransa akan gasu sun shigo Munjibur, yayi mamakin yanda suka fito operation din da daren nan, yanda kasan wanda sukazo kama wata qasurgumar yar fashi haka suka zagaye gurin, a cikin daren akayi Nasarar damqe Khausar dake can cikin daki ita da saurayinta Nasman suna shirya yanda za'ayi ta fece daga Kano har zuwa sanda abubuwa zasu lafa. Shiya takura akan su tsaya a nan su kwana kafin da safe su wuce dan daman sun hadu kenan zasu tafi yawon sheqe ayarsu ta samu kira daga gidansu cewar Jami'an DSS sunje nemanta kuma an baza nemanta a duk inda aka san tana zuwa suna fakonta shiyasa babu shiri tace su tafi, shi kuwa ya rigada yayi caji dalilin da yasaka yace su kwana anan kenan ya samu ya rage zafi kafin da safe ya gudu ya barta dan baze saka kansa a rigimar da be san mafarinta ba haka kawai.

Kwanan da Khalil beyi a can ba kenan ya biyo su suka dawo Kano, tunda ya kife akan gadon dakin Hotel din daya koma be farka na se qarfe goma da Rabi na safe shima saboda bugun qofar da ake tayi daga waje. Dakyar ya tashi ya zauna yana dafe kansa, labulen window a dage suke hasken rana ya cika dakin abinda ya ankarar dashi cewar gari ya waye kenan ya miqe a hankali yana jin kamar iska zata kwashe shi saboda rashin kwarin jiki ya bude qofar.

Room service neda kayan shara, ya sanar dashi ya dade yana bugu dan har ya fara zaton ko ba lafiya ba tunda an tabbatar da mutum a ciki Khalil ya daga masa hannu yace yaje, idan ya gama abinda yakeyi ya fita se yazo yayi aikinsa Mutumin ya juya yana waigensa yanayinsa yayi masa kama da wanda yasha tafi qarfinsa dan dakyar yake iya bude idonsa haka tsayuwa seda ya jingina da qofa.

Wanka ya farayi tareda Alwala yayi sallar Asubar da ta kufce masa. Ta Landline yayi order abinda za'a kawo masa abinci tuli a hakan ma gani yake kamar bazasu qosar dashi ba dan rabonsa da Abinci tun wanda yaci a Jirgi se Coffee daya sha da daddare tas kuwa ya tada abincin nan sunfi kala uku yasha ruwa yayi qyatsa sannan ya fara fahimtar abubuwa dakyau. Kan Gado ya koma ya miqe bayan ya cire jallabiyyar jikinsa, wayarsa ya lalubo tana cikin Aljihun rigar daya fita da ita da daren Tarin Missed calls din daya gani akai sunfi Hamsin duk ya share ya tafi kan na qarshe wanda Yaya Aminu ne ya kirashi. Sanar masa yayi da tun dazu suna CID shikadai ne bezo ba har yan gidansu Hadiza gasu nan harda ita ya bashi haquri akan baccine yaci qarfinsa amma gashi nan zuwa ya kashe daga nan ya kira Jalilah da itama ta kirashi sau ba Adadi.

Muryar Hajiya yaji ita ta dauki wayar, cikin tsananin bacin rai tace
"Ibrahim kana ina? Duk abinda kakeyi ka bari kazo nan inason ganinka kaji ko?"
Da "Toh" kadai ya iya amsa mata danyasan tunda ta kirashi da Ibrahim yau ranta a Asalin bace yake.
A gurguje ya shirya ya fita, gidan Hajiyar ya fara zuwa ko zama bata barshi yayi ba tace su tafi ya daga kai ya kalleta ya Kalli Jalilah da Anty Amina da suke zaune duk sun sunkuyar da kawuna cikin son qarin bayani amma babu wadda tayi magana.

"Ka tashi mu tafi Office din yan sandan, saboda rashin Imani a hada baki dakai a dauki yarinya da tsohon ciki a kukketa a Cell baka ko tsoron wani abun ya sameta sannan a rasa cikinku Wanda ze sanar dani badan wannan yaron Munzali Abokin Khalifa ya ganku acan ba ya gaya masa da sedai mugun labari kake so naji ko me? Kun hada kai da uwarka Jalilah abu na faruwa kun boye mun har ka dawo qasar nan ban sani ba ai shikenan" Hajiya ta ringa sababi a mota gaba dayansu dai suka mata shiru babu wanda yace komai har suka isa.

Sun tarar da Abban su Umaimah tareda qaninsa Baba Abdullahi fuskar Abban kadai zaka kalla kasan yana cikin tsananin damuwa. Tun a daren Jiya da Mama ta sanar dashi bayan ya dawo seda hawan jininsa ya tashi jiri ya debe shi badan Allah ya taqaita ba ya zauna a kujera da ba'asan abinda ze faru ba, ya ringa sauke ajiyar zuciya yana nanata hasbunallahu wani'imal wakeel a zuciyarsa kafin yaji dama dama har ya iya miqewa ya tafi dakinsa. A daren kwana yayi da ciwon rai, Asuba nayi ya kira dan uwansa ya shaida masa se gashi kuwa tun gari be gama haske ba ya ringa fadan me yasa tun a jiyan su Maman basu kirashi ba ya za'ayi su barta ta kwana a can haka suka dungumo gaba daya suka tafi amma ko kallon arziqi basu samu ba dan a sannan bangaren Hadizan basu rigada sun qaraso ba.

Daidai isowarsu Khalil a sannan kowa ya hallara bangare hudu harda yan gidansu Rufaida Babban yayansu da Mijin Yayarta da shima Jami'in tsarone aka hadu ana ta jajantawa juna ga Babansu Khausar daya iso a rikice shima dan katsahan a safiyar mugun labari ya riskeshi.

A daya daga cikin ofisoshin gurin suka hallara, sega Umaimah, Rufaida da Khausar an taso qeyarsu cikin dare daya sun zama abin tausayi karma Khausar taji labari. Ita Umaimah da Rufaida tsabar Azabar cizon sauro da zafi ga warin da gurin yakeyi ne ya gigitasu. Maganin sauron da Khalil ya kai musu masu gadinsu ne suka kwace harda bargon Rufaidah Umaiman cema suka dan tausaya mata suka bar mata nata haka sukayi kwanan zaune suna make maken sauri jikinsu kuwa yayi rudu rudu kamar wanda Sukayi birgima a gidan tururuwa Umaimah tayi Amai yafi sau goma daga daren zuwa safiya shiyasa ta sake jigata tafiya ma seda wata ta ruqota sannan take iya daga qafarta.

Khausar kuwa abin nata yafi muni, daman sanda suka kamata sun tarar dasu a daki bayan sun gama sheqe ayarsu suna kora kwayoyi saboda su samu nutsuwar bacci a cewarsu, tun a hanya ta ringayi musu shirme da masifar me tayi da zasu kamata rabi cikin hankalinta rabi a maye dan haka suna zuwa a maimakon waddata taho da ita ta sakata Cell din su Umaimah seta jefata cikin Matan nan da dama cike suke da haushin su Umaimah da suke ganin suna da gata. Tana shiga ta taka daya daga ciki bata yi wata wata ba ta hankadata Khausar na daidaita tsayuwarta dan ta kusa ta fadi ta kwashe mata da mari nan fa sauran sukace dawa Allah ya hadasu suka rufu akanta sukayi mata dukan kawo wuqa masu ganin na kallonsu babu wadda ta kai mata dauki.

Kaca kaca sukayi mata fuska ta kumbure baki kamar ta boye fanke saboda yanda ta tashi kamar ma sun cire mata haqori ne oho sannan tun farar safiya aka jefata a dakin tuhuna. Kamar masu jin haushinta seda suka fara lallasata abinda ba'ayiwa su Umaimah ba kafin suka fara mata tambayoyi. Da farko tayi gardama, dukda wayarta dakw hannunsu sun binciko duk wata shaida da suke buqata harda ma abinda be shafi case din ba sun qara tara wani chages din akanta amma dukda haka tayi qememe taqi amsa laifinta.

Dukan mutuwa suka mata har daya daga ciki na cewa a bashi belt ya shaqw mata wuya kawai ta mutu su huta dan sun fahimci yanzu tura nasu laifi Kotu bata lokaci ne kawai dan idan sunada hanya se kaga shari'ar bata wani kasancewa yanda ya kamata ake sallamarsu amma idan suka kasheta anan sun kashe banza qarshenta suce sun wayi gari sun tarar da gawarta shikenan ai kafin ma ya kai aya jiki na rawa Khausar tace zatayi magana. A gaba suka sakata suna mata video ta amsa duk abinda ake tuhumarta dashi harda dalilan ta da ya sakata aikata komai daga nan suka mayarda ita se yanzu aka sake dakko su.

Kowacce na ganin idon iyayenta ta fashe da sabon Kuka, Hajiyar Khalil ta shiga tafa hannu kwalla ta kawo mata tana cewa
"Na shiga uku ni Aisha kalli yanda kuka mayar da yarinya a dare daya fisabiliklahi bakuda tausayine baku ganin halin da take ciki me tayi muku?"

"Idan baki rufe mana baki ba Hajiya zaki fita daga nan, ita ce bata tausayin kanta da har ta jefa kanta a wannan halin kinga kuwa babu abinda ya shafe mu" daya daga cikin Jami'an ya fadawa Hajiyar a dake dole ta kama bakinta tana share kwallar tausayin Umaimah.

Bayani Detective Adnan ya farayi akan bincike ya kammala ga kuma sakamakon da suka samu dan haka yanzu sun gama cike duk wasu takaddau da suka kamaya zasu turasu kotu kowanne yaje ya nemi lauya dannan zasu ci gaba da tsare su ne a hannunsu ba wai zasu barsu su tafi gida ba. A tare Su Umaimah suka fashe da mugun kuka kowacce ita kadai tasan azabar data dandana adare dayan nan inaga ace zasu ci gaba da zama anan kawai mutuwa zasuyi.
Chapter 114 · 0% Book details