← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 267

Sashe 71

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata shida da haihuwar Mu'ayyad idanka ganta seka dauka Yara biyar take raino yanda gaba daya ta hargitse shikansa gidan ya fita a kamanninsa duk inda ka duba kayane zube na sakawa da kayan wasan Mu'ayyad.
Misalin qarfe tara bayan Khalil ya fita aiki tana kishingide akan kujera da waya a hannunta Mu'ayyad data samu ta lallaba dakyar yayi bacci na kwance akan dan gadonsa me lilo yana shillashi, wani series take kallo a YouTube taji ana qwanqwasa Get, tasan baze wuce Aliyun Maman Hauwa ba ko yayi mantuwar wani abun, wake ta aikawa da Ramatu kishiyar Maman Hauwan tayi mata Alalan gwangwani zatayi baqi qannen Hajiyar Khalil ne sukazo daga Gaya zasu zo ganin Mu'ayyad din.

Hijabi ta saka taje ta bude, Rufaida ce da qaton cikinta ta sako wani uban Hijabi se haki take saboda tafiyar da tayi ta bud mata ta shigo tana cewa
"Uwar biyu daga ina haka?"
"Wallahi gajiya nayi da zama ni kadai shine nace bari na shigo na dan rage lokaci kafin rana tayi" Rufaidan ta bata amsa suka wuce ciki Umaimah na cewa
"Kin ganni nima fa wai baqi zanyi amma babu abinda nayi na samu dai na bada Ramatu tayi mun Alala ina da zobo in hada musu dashi gyaran gidan ne na gagara yi wallahi duk na gaji"

"Ai kina ma qoqari ni idan kinga nayi shara yanzu ai Abban Anam yana gari ne, ina zan iya dazu ma na kira Maman Salaha inji yaushe zata dawo idan ba haka ba na nemi wata kawai na gaji da wanne zakaji da aikin gida ko da wahalar kanka, kema da me aikin kika nema kawai kika huta ta rage miki aiki"
Rufaida ta fada, Umaimah ta yatsina fuska tace

"Me aiki ni Allah ya rufamun Asiri zanyi abinda zan iya na bar sauran kawai"

"Iyayen kishi" Rufaida ta fada cikin sigar tsokana kafin taci gaba da cewa
"to ko ba me kwana ba ai seki nemi me zuwa ta tafi, da safe idan megidan ya fita tazo kafin yamma ya dawo ta gama miki ayyukanki ta tafi ba shikenan ba"

"Ke nifa me aikince gaba daya bana so ki barni zanyi aikina" Umaiman ta fada cikin qosawa da zancen me aikin da kullum Rufaida se tayi mata kamar ita take mata ayyukan gidan balle tace ta gaji, a maimakon ta tashi tayi abinda zatayi kafin zuwan baqin nata nan suka shantake suna hira bata ankare ba se jin bugun qofa tayi ta kalli Agogo qarfe sha daya na safe ta miqe tana salati ta je ta bude, Ramatu ce da kanta da kular data bada a zubo mata Alalen, daga bakin Get ta tsaya ta bata tana cewa
"Yaran duk suna makaranta kuma naga lokaci yayi shiyasa nace bari na miqo miki da kaina"

Umaimah ta karba tana cewa
"Wallahi nima ban ankare da lokaci ba se yanzu, nagode sosai Allah saka da Alkhairi" daga haka ta juya ciki da kular Alalen ta ajiye a kitchen tana jiyo kukan Mu'ayyad daya farka daga bacci ta shiga tana yamutsa fuska ta kalli palour tana tunanin ta ina zata fara gyaransa, Mu'ayyad din ta karba ta bashi Nono, Allah ya sota da wuri tayi masa wanka yayi kashi ya bata jikinsa ta hada gaba daya tayi masa wanka kawai, yana gama sha ta ajiyewa Rufaida shi, kayan wankin dake kan kujera ta shiga kwashe tana watsa su a kan gadon dakinta, ta tattare Gadon da sauran tarkacen Mu'ayyad ta kai Store.

Sama sama ta share palour ta kunna turaren wuta ganin sha biyu saura kwata yasa ta kwaso kaya da diaper ta ajiyewa Rufaida tace ta canza masa ita kuma ta shige bandakin dake palour ta daurayeshi ta dauraye jikinta dan tasan zasu buqaci shiga yin Alwala dakinta kuwa baze shigu a yanzu ba dan gyaransa ze dauki lokaci.

Tana gama saka rigarta taji bugun qofa tasan baqin ne suka iso dan qarfe sha biyu daman aka ce zasu zo, ta goge fuskarta da soson powder ta fesa turare ta yafa mayafi, ita da kanta data kalli kanta seda taji wani iri yanda kasan wadda ta tashi daga bacci duk a firgice haka ta fita ta bude musu tana yiwa Rufaida datayi rashe rashe magana kan ta gyara.
Su biyu ne manya da tana ganinsu taga kamanninsu da Hajiya se wata da zasuyi Sa'anni da Khalifa daya kawo su.
Ta tarbe su da fara'a tayi musu iso cikin palour suka zauna, seda ta gabatar musu da Ruwa da Lemo da Cake suka gaisa tana kallon yanda yarinyar ciki ke qarewa palour kallo duk seta tsargu taji wani iri, basu taba zuwa ba be kamata ace sunzo sun  tarar da wani abu ba daidai ba.

Sun jima sosai a gidan har seda Khalil ya dawo sunci Alalen suna ta santinsa da zasu tafi ta juye musu ragowar da tarin tsarabar data hado musu cikin kayayyakin data samu na barkar Mu'ayyad ta hada musu da turaren wuta, Khalil ne ya tafi kaisu suna fita ta goye Mu'ayyad ta shiga gyaran gidan dan ta tabbata mita ce zata sha ta kamar ba gobe idan ya shiga dakin ya tarar dashi yanda ya barshi da safe.

Allah ya taimaketa har ta gama ta sake wanka tayiwa Mu'ayyad sannan ya dawo gidan lokacin har anyi sallar Isha. Wanka ya farayi shima ta kawo masa Taliyar data dafa ta dumama masa stew yace ya qoshi yaci abinci a gidan Hajiya.
"Anty Umma tace ya kamata a samo miki me aiki wai taga kamar aiki yayi miki yawa sannan ga raino" Khalil ya fada yana kallon Umaimah dake shayar da Mu'ayyad, ta yamutsa fuska a ranta tace
"Tsabar munafunci ko ina ruwanta oho" a fili kuwa tace

"Ni na gaya mata ina da buqatar me aiki ko nace na gaji, kaima sonbata bakinka ne kawai amma sau nawa zna gaya maka bana son wata yar aiki indai ba kuma so suke su kawo mun wadda zata kwacemun miji ba"

"Kin yarda wata zata iya kwace miki mijin kenan?" Ya tambayeta yana dage gira ta harareshi tareda tura baki tace
"Sedai uwar yarinya ta haifi wata kuwa"

"Toh nidai na gaya miki ne dan kar kiga me aiki daga sama dan ta rigada tayiwa Hajiya magana ma kuma an kira wata da take kawo su tace a bata kwana biyu, karki damu na wassafa musu irin wadda za'a kawo baqa mummuna da bazan iya kallon fuskarta" Khalil ya fada cikin sigar tsokana, bata kulashi ba se qananan mitocinta ta dura a ranta ko ta ayyana ko uwar wa tazo mata gida seta koreta dan ita bata ce musu tana da buqatar mataimaki ba balle a mata iyayi.

Ashe abinda ya faru tun a hanyar mayar dasu gidan Anty Umma da sam bata gani tayi shiru tayiwa Khalil maganar hargitsewar gidan nasu da rashin kintsin ita kanta Umaimar.
"Ita wannan matar taka daga haihuwa daya ji yanda ta fita hayyacinta se kace me yaya goma gida duk ya qazance kodai daman kazamace se yanzu ne abin ya fito fili? To koma dai yaya ne ka nema mata me aiki ta ringa kama mata wasu ayyukan dan idan ba haka na wannan ta qara tara yara bamu san yanda zata zama ba kuma" Anty Umma ta fada, Khalil yayi shiru a ransa yana juya maganarta, shikansa halin qazantar da Umaimah ta koya yaja damunsa danshi Allah yayi shi sam baya son datti ko kadan ita kuwa yanzu ta daura abota da qazantar da take fakewa da sunan jego.

Gida se yayi kamar anyi yaqi a ciki sannan zata gyara, kwalliyar safe kuwa ya manta yaushe rabon daya fita ya barta tsaf se an auna arziqi ne ze dawo ya tarar tayi wankan tayi kwalliya kayan wanki kuwa na Mu'ayyad se yayi kamar me sannan zata wanke abubuwan dai gasu nan kala kala se shegen chatting din da baze amfana mata komai ba ta tasa a gaba shi yasa koda suka isa gidan Hajiya Anty Umma tayi mata zancen a nemawa Umainah me aikin be musa ba dukda yana hango takurar da zasuyi saboda yanayin gidan amma in har zata ringa kintsa gidan yanda yake so zasuyi manaji na dan lokaci kafin ya samu yanda yake so ya canza musu muhalli wanda shine plan dinsa na gaba.

Kwana biyu a tsakani kuwa sega Habiba tareda wata yarinya da bazata wuci shekaru sha uku zuwa sha hudu ba da qullin kayanta Habiba take gaya mata Hajiya ce tace a kawo mata me aiki aikuwa ko ruwa bata basu sun sha ba tace su juya bata buqata ranta kamar ana hura mata wuta saboda ganin yarinyar fara kyakykyawar bafulatana dukda yarinya ce amma tana da kyau me daukar hankali.

Ta ringa surfa masifa ita kadai a gida koda Hajiya ta kirata akan me yasa tace a maida yarinya kai tsaye tace
"Nifa Hajiya ban buqaci wata me aiki babu abinda ya gagareni yi a gidan nan" ta bawa Hajiyar Amsa kanta tsaye, Hajiyar bata ja ba tace shikenan tunda tace haka sukayi sallama ta kashe. Koda Khalil ya dawo shima seda ta tasa masa wata mitar akan kawo me aikin ya mata banza har ta gaji tayi shiru dan kanta kafin ya kalleta yace

"Tunda kin kori me aiki ki tabbata karna sake ganin wani abu da ba daidai ba a gidannan, daka kan tsaftar jikinki zuwa ta cikin gida har abincina bana son a sake samun wani akasi idan ba haka ba dole ki nemi me aiki dan bazan iya rayuwa cikin qazabta ba"

"Amma dai ina iya qoqarina, kana kallon dai yaron nan idan ya tasa rigimarsa komai hanani yi yakeyi sedai na goyashi ni kuwa ina zan iya sunkuyon aiki dashi a baya, zanyi abinda zan iya kawai wanda be samu ba a ringa haquri kwana nawa ne ze girma komai ya dawo daidai" ta bashi amsa tana daddanna wayarta se ya ja tsaki dan kulata ma qara masa ciwonkai zatayi tunda ita duk maganar da aka fada tana da amsarta.
Chapter 71 · 0% Book details