← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 252 OF 267

Sashe 252

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannunta na rawa ta karbi wayar cike da Mamaki ta wuce falon Mama, seda ta fada mata yanda sukayi ta nuna mata wayar da kudin kafin ta wuce ta bawa Anty kudin Hijabin sannan ta shige dakinta tana juya wayar. Rasa ta inda zata fara amfani da ita tayi gaba daya se kawai ta ajiye, shekara biyar ba wasa ba, ta dai ganta da chaji full a ranta ta ringa mamaki tsahon lokacin kuma wayar batayi komai ba.
Seda yamma bayan Salman ya shigo gidan ta bashi yana murmushi yace
"Ni ya tambaya fa ya za'ayiwa waya karta lalace ai kuwa duk kwana biyu se Abba ya chaja wayar nan ba qaramin aiki kika bashi ba, ba yanda banyi dashi ba ya bani ita a lokacin ma in kin tashi amfani da ita na siya miki wata yaqi gashi ke kin manta ma yanda ake operating nata, kyanki Rakani kashi yanzu" ya fada yana gwada mata yanda zata yi amfani da wayar nan da nan ta tuno tunda daman ta sani mantawa tayi.

Shiya siyo mata layi yayi mata register sa dan da yace suje tare qi tayi, haka kawai take tsoron fita waje, bayan ta dora layi a wayar ta shiga duba numbobin kai duk sunanan babu abinda ya goge ta tsayar da idonta kan number Khalil qirjinta yana bugawa da qarfi tanajin kamar ta danna kira wani sashi na zuciyarta kuma yana hanatayin hakan, dakyar ta yaqi zuciyarta ta haqura da kiran, seta kashe wayar gaba daya ta ajiye ranta babu dadi abubuwan datayi qoqarin bunnewa suka fara dawo mata dalilin wayar nan, haka datazo bacci ta sake kunnata ta shiga hotuna ta ringa kallo lokaci daya hawaye ya shiga zubo mata data gaji da kallon hotunan ta ajiye wayar tasha kuka taqoshi kafin bacci yayi awon gaba da ita me cike da mafarkai kala kala. Kamar yanda Abba yayi Alqawari ya karbo mata form din amma ba kamar su Mama da suke zuwa sati sau biyu ba ita sau hudu ne litinin zuwa Alhamis qarfe goma zuwa daya na rana.

Ta ringa saqa da warwara akan yanda zata fara fita makarantar, to

*HALIN KISHI*

*NA MARYAM FAROUK*
*(UMMU-MAHEER)*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATON*
*(DON CIGABAN ADABIN HAUSA)*

Page 86

Ta ringa saqa da warwara akan yanda zata fara fita makarantar, da ranar tazo kuwa tun Asuba haka ta tashi da faduwar gaba, a sanyaye ta ringa ayyukanta. Tunanin yanda zata fuskanci mutanen unguwarsu kawai takeyi ta tabbatar ganinta seya maido da labarin baya amma ya zatayi? Ba zata cigaba da zama haka ba, dole ta fuskanci komai ta girbe shukar da ta dade tana yi. Qarfe tara da Rabi ta shirya tsaf cikin Hijabin Makarantar Ruwan Madara me haske, ta leqa Dakin Mama tana zaune a falo tace
"Har kin shirya?"
"Eh na shirya Mama" ta fada tana zama. Maman ta tura mata litattafan data ware mata wanda aka rubuto na Ajin da aka dauketa tana cewa
"Gasu nan toh, amma da kin jira Firdausi na aiketa ta siyo mun kati seta rakaki dan ba a inda kika sani ake makarantar yanzu ba"

Seta gyara zamanta ta zuba litattafan a jakar data sako Alqur'aninta, Firdausin ta shigo da aiken Mama ta karba tana gaya mata ta raka Umaiman makaranta tace toh. Harta miqe Mama ta tsayar da ita, dakinta ta shiga ta fito da baqar safa da niqab ta bata ta karba tana sakin boyayyar ajiyar zuciya. Tuntuni take shawarar neman niqab din amma tsoron kar Maman tace wani abu yasa ta haqura zata fita a haka. Dalilin Niqab din yasa ta ringa taka qafarta da kwarin guiwa har suka fita daga gidan. Seda ta tsaya tana kallon layin nasu kamar sabuwar baqauyiya. Kwalta har qofar gidansi dukda daman Hanya ce babba motoci nabi amma babu kwalta yanzu kuwa harda fitulun solar aka saka musu. Unguwar ta sake habaka sosai, shagunan data sani qanana duk sun bunqasa gidajen kansu wasu bata ma gane su ba saboda gyare gyaren da suka sha. Haka suka ringa tafiya tana kalle kalle kamar farin shiga birni, suka wuce tsohuwar Islamiyyar su wadda take hade da babban Masallacin unguwar suka qara tafiya kadan kafin suka isa sabon ginin makarantar qato hawa uku ga Ajujuqa birjik da ofisoshi.

Har gurin shugaban makarantar ta rakata, Umaimah ta daga Niqab din tana gaishe shi, kalolin iya shegen data ringa tsula masa na dawo mata a shekarun baya Yah Sheikh din ya zama babban mutum yanzu gemunsa duk furfura dukda be kai shekarun su Abba ba amma girman daya hau kansa ya qara masa kwarjini da haiba ake masa kallon Babban mutum sosai. Fuskar sa da walwala ya amsa gaisuwarta kafin ya kira wani Malami da baze wuce sa'an Salmab ba yace masa ga sabuwar dalibar Ajinsa. Ta kalli Malamin daman tun Asali abinda ya ringa hadata da makarantar kenan, Yah Sheikh baya dauko Malamai manya sedai ya debo qananan yara da acewarta basufi sa'anninsu ba suzo suna zare musu ido ku suce zasu dake su shiyasa ta raina Malam a wancan lokacin amma a yanzu cikin tsantsar ladabi ta gaida Malamin da aka ce na Ajin nasu. Yayi gaba yana cewa ta biyo shi, harta yunqura ta koma ta zauna, wannan dama ce ta samu da zata fara rage tarin haqqoqin Jama'a dake kanta.

Muryarta na rawa ta shiga roqon Yah Sheikh din gafara akan abubuwan data yi masa a baya, ya ajiye Takaddun da yake dubawa har sannan yana murmushi ya kalleta yace
"Haba Umaimah wace yafiya kuma kike nema a gurina ni ai bakiyi mun komai ba. Ko a baya nayi miki uzurin yarinta a duk abubuwan da kikeyi bani kadai ba duk sauran Malamaina bana zaton akwai wanda ya taba qullatar abinda kikayi masa a baya har yanzu duk kusan muna tare, a cikin Malaman ku Malam Sa'adu ne kadai Allah yayiwa rasuwa se Malam Lawi daya bar qasar yana Jami'atul Madina yanzu saura koda bama aiki tare suna yawan kawo mana ziyara har su bada darussa a wasu ranakun nasan wata rana zaki gansu. Ki saki ranki kinji kiyi abinda ya kawoki yawancin karatun Tishi ne akan abinda aka koya muku a baya kuma duk kin iya da an tuna miki zaki tashi se kiyi qoqari a wannan karon ba wai kiyi karatu kawai ba Aa ki maida hankali gurin fahimtar abinda kika koya tare da aiki dashi, Allah ya wuce gaba".

Jikinta a sanyaye ta fita bayan ta maida Niqab dinta. A waje ta taradda Malam Najib kamar yanda taji ya kirashi yana jiranta ya wuce gaba har Aji biyu inda aka sakata suka shiga tare ya nuna mata gurin zama cikin sauran Dalibai da sukayi shiru saboda shigowarsa. A sanyaye ta nemi guri ta zauna, murya babu Amo tayiwa wadanda ke kusa da ita sallama suka amsa suna kallonta. Malam Najib ya zauna a teburinsa ya dauko Register, seda ya kira suna kowa ta amsa wanda basu zoba ya saka musu kafin yayi gyaran murya yace
"Sabuwar Daliba menene sunanki?"

Gabanta ya fadi, dukda da Niqab a fuskarta seda ta zaro ido ta waiwaya kamar me ciwon wuya ta kalli Yan Ajin da suka zuro mata ido suna jiran amsarta a haka dai bataga fuskar sani ba duk cikinsu dukda dai ba wani kallonsu tayi dakyau ba. Seda ya sake maimaitawa kafin ta bude baki a hankali tace
"Umaimah Sabo"
"Masha Allah Malama Umaimah muna miki barka da zuwa" ya nuna wadda take kusa da ita yace
"Wannan Malama Aisha kenan itace Monitar ku, duk wani abu daya shige miki duhu ki tuntubeta, Daliban Ajin nan Dalibai ne masu hazaqa ina fatan kema zaki bamu taki gudummar gurin tabbatar da kambun mu".

Kai da gyada masa kawai dan ta kasa magana. Ya bude Drawersa ya ciro Littafin UmdatulAhkam tuni daman sauran yan Ajin kowa ta fito da nata suka shiga bitar inda suka tsaya kafin ya dora musu sabon Karatu. Yana gamawa wani Malamin ya sake shiga a haka har qarfe daya basu samu hutun ko minti biyar ba dan da wani ya fita wani ze shiga duk kuma wanda ya shigo seya tambayeta sunanta Malamin qarshe dayake da surutu yace ta dage Niqab din tasha iska dan kusan duk yan Ajin suna saka Niqab din amma kowacce ta daga nata se zasufita suke saukeshi, shima dai kai ta girgiza masa Alamar Aa. Da yake bema tambayeta sunanta ba yace
"Tohz, kurma ce kenan", maganar ta bata haushi amma ta dake da lokacin baya ne seta maida masa da martani in ma bata ce uwarsa ce kurmar ba amma yanzu kura tayi lafiya.

Da aka tashi tareda monita suka fito tana ta janta da hira har suka fita saga makarantar tareda wasu yan Ajin. Masu Motoci suka ragewa wanda suka saba tafiya tare hanya masu hawa na haya suka tafi su kuma na kusa suka daba a qasa. Kusan su bakwai suka jera acikin yan Ajin nasu, Malama Aisha take ce mata
"Kema gidanki nan kusa ne Ashe"
"Eh" ta bata amsa, layi daya tsakanin gidansu suka rabu Malama Aishan ta shiga gidanta dake bakin hanya, Umaimah tasan Matar gidan dan tana Amarya sun dan yi hulda suna haduwa a gidan Maman Nana kafin tayi aure ta bar unguwar kenan kishiya aka mata. A cikin layinsu suka rabu da sauran mutum biyu da suka taho tare ta shiga gida tana Mamakin ganin daya ta shiga gidansu Maman Nana dayar kuma ta miqe.
Chapter 252 · 0% Book details