Sashe 178
Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Dan Allah kayi haquri Habibi, wallahi bani nace ya biyoni ba kawai ganina yayi a hanyar Islamiyya ya tsayar dani kuma ni bansan zakazo ba ma da na shiga gidan Anty Habi kawai saboda karka ganshi ranka ya baci" Humairan ta fada cikin muryar shagwaba. Kallon wayar yayi ya kalli Umaimah data zura masa ido kamar farin shigar maita ya rasa abinda zece se kawai ya dannan ya kashe wayar, Mu'ayyad da Bibi ya kalla yace
"Kuje gurin Hajiya nima gani nan shigowa" suka kwasa da gudu suka fita seya juya yana kallonta zuciyarsa na wani irin tsalle yanda kasan wanda ya tsaya gaban Alqali yace
"Umaimah wallahi..."
"Ka riqe rantsuwarka munafiki karka kuskura ka gaya mun wata magana anan, abu daya nake so yanzu ka kira koma wace yar iska ce a gabana ka gaya mata daga yanzu koda wasa karta sake kuskuren kira layinka, idan kuwa ta sake ka gaya mata da bakinka seka lalata rayuwarta".
Zare ido ya shiga yi yana kallonta amma ya kasa bude baki yayi magana, ta yaya ma ze iya haka ya kira Humaira ya gaya mata wadannan maganganu gaskiya abun da wahala. Yawu ya hadiye yana qoqarin kama hannunta ta fizge yace
"Dan Allah base na kirata ba, zanyi blocking number kawai yanda bazata qara samu na ba"
"Kayi abinda nace Khalil idan kana buqatar kwanciyar hankali idan ba haka wallahi" Umaiman ta fada cikin daga murya se ya janyo wayar ya shiga kiran layin Humairah saboda yanda tayi maganar ji yayi akmar saukar aradu akansa.
*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*
*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼
Page 65
A fusace ta fizge wayar daga hannunsa ganin ya tsaya yana mata magiyar banza da wofi, seda ta fara ringing taji an daga kafin ta saka wayar a speaker ta cilla masa tana cewa
"Maza gashi nana ka gaya mata da bakinka idan ba haka ba wallahi ba zaka so abinda zanyi ba, ai ka sanni tsaf bana shakkar kowa idan nayi niyyar rashin mutunchi babu wanda ya isa ya dakatar dani"
"Haba Umaimah haba Umaimah yanzu ina hadaki da Allah amma kamar ba musulma ba aba zaki haqura ba? Dan Allah ki bari nayi miki alqawari ni da kaina zance gurinta amma kar kisakani yin abinda be kamata ba, ko wani naji yayiwa Humaira haka se inda qarfina ya qare guri kwatar mata haqqinta balle ace ni da kaina zan wulaqantata karki manta jinin Mansur ce" Khalil ya fada cikin rawar murya, wata gundumemiyar Ashar ta mulmulo ta watsa masa tana jifansa da wani matsiyacin kallo tace
"Ni kake gayawa haka Khalil? To karkayi abinda nace kaji har ka iya kallona kana gayamun dole ka kare darajar wata banza shashasha a waje amma ni kana wulaqanta tawa darajar ko? To karkayi, wlh se kayi nadamar qin yin abinda nace. Sena balbaltata na lalata darajar tata da kake iqirarin karewa"
"Babu abinda ze sameta da yardar Allah sannan kibi duniya a sannu Umaimah in har kina so ki mutu ki taradda ubangiji cikin salama to kiyi gaggawar tuba ki koma ga Allah in ba haka ba wlh ina tausayawa qarshen ki, sannan aure dai babu fashi da yardar Allah gara ma ki saka a ranki dan dazun ma munyi magana da Hajiya Aisha kuma a cikin satin nan masu zuwa nema zasuje can Jalingo" sukaji Muryar Mama daga cikin wayar, a firgice ya kai hannu ze dauki wayar dan shaf ya manta da cewar tayi kira suke ta wannan taqaddamar amma ta rigashi dauka ta miqe da sauri tana ja da baya tace
"Idan kutumar ubanki ne yake rabon Aljannar karya bani ko kuma idan nazo shiga ku hanani tsohuwar banza kawai"
"Ke Umaimah baki da hankali" Khalil daya yunquro ya figze wayar ya fada haryana tureta ta fada kan kujera se ta taso yanda kasan babu wani nauyi a jikinta, Ashar ta shiga dura masa ta uwa ta uba tana jifansa da duk kalaman da sukazo bakinta. Waiwayawa yayi ya kalli falon seya sauke ajiyar zuciya ganin Ruqayya da da take jera abinci a Dining bata gurin, yaran daman ya kada su da yanzu a gabansu zatayi masa tijarar kenan.
"Wallahi Tallahi Khalil se nayi Ajalinka in har kace ba zaka janye qudurinka ba, sannan kuma na kashe duk yar abu ta kazan da tace zata shigo gidan nan, ni zaka munafunta ka mayar sakarya to wallahi dakai da duk wanda suke daure maka gindin yin abinda kake shiri daidai nake daku se kun gane kurenku".
Kururuwa take tana surutai shidai tuni ya haye sama ya kullo qofar nan bakin qofar ya durqusa ya dafe kansa dake neman rabewa biyu saboda tashin hankalin daya riske shi. Yana jiyo yanda yake ihu daga qasan tana zaginsa shi da iyayensa kafin daga bisani ta fashe da kuka se kuma qarar fashe fashen abubuwa daya fara jiyowa da alama kayan falon take farfasawa seya miqe dakyar ya shige daki, bandaki ya shiga ya sakarwa kansa ruwan sanyi yafi minto talatin a tsaye har aka kira sallar Magriba kafin ya dauraye jikinsa ya fito zuciyarsa tana bugawa da qarfi. Jallabiyya ya jura a jikinsa ya dauki wayarsa da muqullin mota, cikin takatsantsan ya bar gidan bayan daya tabbatar da bata falon.
A bakin qofar sata raba bangarensu dana Hajiya ya tsaya saboda jiyo hargaginta da yayi tana cewa
"Haka kikace? Toh na rantse da girman Allah sedai kowa ya rasa, se nayi sana din Khalil dani da ku sedai kowa ya rasa" kafin ya gama tantance abunda take nufi aka bude qofar Umaiman ta fito buzu buzu yanda kasan farin shigan hauka gashin kanta a tsaitsaye fuskar nan tamkar Hadari banda kumburi da idonta yayi kamar an doketa a gurin. Wani kallo ta watsa masa da se da yaji hantar cikinsa ta kada taja tsaki ta wuce cikin gida ta barshi a tsayr daidai nan Hajiya ta fito itama tana kiran sunan Umaiman Jalilah na biye da ita a baya tana cewa
Haba Hajiya yanzu har zaki bita saboda son ki qarasa zubar mana da mutunchi a idonta, saboda ita ba mutuniyar kirki bace vata dubi ko darajat shekarunki ba idan ma bata kalli matsayinki a gurinta ba ta iya takowa har gabanki ta zageki to idan duk kun makance ta gama da ke da Khalil din wallahi mu ba zamu zuba ido qata yar iska ta taka uwarmu ba, kuma idan ta cika mara kunya ta dawo ta sake miki ko kallon Banza na rantse sa Allah sena karyata idan yaso a kaini inda bazan fito ba".
'Ki rufe mun baki Jalilah kima wuce ki dau gyalen ki kibar gidan nan tunkafin na saba miki, haka kawai muna zaune lafiya zaki janyo mana jidali ina ruwanki keta zaga ko kuwa? In ma haka ne ai abin zagin aka mata gara ita an ga kalar nata kishinke wayasan abinda zakiyi idan naki Mijin yace ze qara aure?" Hajiyar fada a fusace tana kallon Jalilah se tayi saurin tare Hajiyar da cewa
"Allah ya tsareni ya tsari zuri'ata da hauka irin na Umaimah dan wannanba kishi bane zallar jahilci hauka da son rai take gwadawa. Ita har tana da bakin crwa ba zata zauna da kishiya ba bayan data tashi gidan ubanta ma ina mata biyu ta tarar? Da haka tata uwar take ai da bata zauna a gidan ba harta haifeta shine mu zata zo nan ta daga mana hankali to karta fasa, aurene kamar anyian gama da izinin Allah sedai baqin ciki ya kasheta Khalil kuwa nan gani nan bari wlh tana kallo ze dauko santaleliyar Matarsa su more soyayya ita yana can Kishi ya haukatata an kaita Dawanau"
"Idan baki bar gidan nan ba se na bata miki Jalilah" Hajiyan ta sake fada, se Jalilah ta koma ciki tana qunquni, jakarta da gyalenta ta dauko ta fito tana Kallon Khalil dake nan kamar gunki tace
"Har daki ta tarar da uwarka ta zaga tace kuma idanka haifu kayi mata kishiya ta gani, to ina jira na gani nima ka haifu cikin Bayero ko kuwa a Asibiti aka qarawa Hajiya kai bayan ta haifeni" dukan da Hajiya ta kai mata yasa ta matsa da sauri ta fice daga gidan Hajiya ta kalli Khalil tace
"Babana ya isa haka tun ba'aje ko ina ba kaga abinda ka kira mana to ka janye maganar nan kawai ka haqura kayita addu'a Allah ya daidai ta maka zamanka da matarka kawai dan ni bazan iya tashin hankali ba" ta juya ta koma cikin gida.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya daga qafarsa da kyar ya fice daga gidan, seda yayi sallar isha kafin ya dawo, a compound din tsakiyar ya zauna ganin Khalifa a gurin shima is muzurai yakeyi Khalil din na zama yace
"Gaskiya Yaya ya kamata kayiwa gidanka garambawul, ace har rashin mutunchin Anty Umaimah ya kai taje har gaban Hajiya ta kirata da munafuka? Wallahi tun wuri kayiwa tufkar hanci dan idan ba haka na gaba bamu san abinda zatayi ba kuma muma ba zamu zauna mu zuba ido tanayiwa mahaifiyar mu duk cin kashin dataga dama ba"