← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 254 OF 267

Sashe 254

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abin ya munana ya zarce makaranta dan labari sabo ya koma a unguwa data fita an ringa nunata ana tuno ai ga abinda tayi. Majalissun Samarin unguqarsu suka samu nayi, sun kuma dana mata tarko jira kawai sukeyi lokacin da zata afka ciki yayi.
Wannan sabon yanayin ya saka damuwar da take ciki qara nunka tada saboda a baya iya damuwar yan gidansu ce yanzu kuwa tsangwama take fuskanta sosai daga gurin mutane tayi kuka akan haka harta haqura, ta saki zuciyar ta dole ta tunkari koma menene ba zata cigaba da buya tana gujewa Laifukanta ba Niqab dinma ta dena sakawa.

Wannan kwarin guiwar data bata kanta da kuma tasirin addu'ar da takeyi babu dare babu rana yasa ta samu sauqin Al'amura. Taci gaba da zuwa Islamiyyarta masu gulma da zundenta har sun gaji babu dai me kulata in ka cire Malama Aisha da tsirarun yan Ajinsu wannan be dameta ba karatunta takeyi dan shine a gabanta ba kuma neman qawa takeyi ba dan ta shata ta warke.

An samu dogon hutun yammakaranta, babu tsammani sega su Mu'ayyad an kawosu da Jakar kayansu abinda ba'a tabayi ba ko na kwana daya tunda ta bar gidan Ubansu. Zuwan yaran ya sake rage mata kewa da gaske dukda ta wani bangaren zuwan nasu Fami ya zamar mata na abinda take qoqarin shafewa daga rayuwarta. Tunda Bibi ta qyalla ido taga wayarta data sake ajiyewa dan ba abinda take da ita. Ba me kiranta babu wanda take kira social media kuwa bata gabanta ma yanzu kullum sedai kawai tayi mata chaji ta ajiye amma tunda su Bibin suka zo ta samu wayar shikenan ta banu ta mayar da ita kamar tata. Kullum seta kira Dadynsu idan suna wayar sedai Umaimah ta tashi ta fita saboda abinda takeji. Iya kallon Mu'ayyad ya isheta tashin hankali, a shekaru sha biyun da yake gaba daya ya rikida ya zama Khalil, kamanninsa, tafiyarsa, maganar da komai nasa na Khalil ne.

Idan yana cin abinci zama take ta zuba masa ido dan hatta yanda yake riqe cokali da tauna abincin sak Khalil, lokaci da yawa seta juya gefe ta share hawaye, babu abinda ya ragu daga ranta na daga soyayyar Khalil sedai ma abinda ya qaru son zuciyarta ya rabata dashi gashi suna raye cikin duniya daya amma yafi qarfinta. Idan suna waya da yaran se taji kamar ta kwace taji muryarsa, haka wani sa'in kasa riqe kanta takeyi ta kirashi amma kafin ya dauka seta kashe shi dan bata san me zata ce masa ba. Tana so suyi magana, ta roqi yafiyarsa amma ta gagara hada wannan jarumtar, a haka hutu ya qare yara suka koma gidansu. Ranar da zasu tafin da kansa yazo daukarsu tareda Humaira data qara zama wata hamshaqiyar Mace. Tana cikin irin matan da shayarwa take karba suyi kyau su cika ga jin dadi da zaman cikin raba ya qarawa farar fatarta kyau da sheqi duk inda ta wulga daukar ido takeyi.

Yanda ta ringa fara'a tana gaida Umaiman ya soketa ta ringaji da biyu take mata haka, ta gama hade musu kayansu tana jiyo tashin hirarsu a falon Mama Bibi ta shigo tana tura baki ta fada jikinta, murmushi tayi kawai tun safe take rigimar ita ba zata tafi ba anan zata zauna seda Mama ta binciko Dorina ta ajiye kafin ta shiga taitayinta. Iman ta shigo tareda Aryaan Umaimah ya kalleshi fari tas kamar ka tabashi jini ya fito a haka zaka dauka da Mamansa yake kama amma ita tana kallonsa ta hango kamanninsa da Khalil sedai banbancin launin fata ya boye wasu. Tayi masa murmushi kamar yanda shima yakeyi Iman na kallon Bibi tace
"Dady yace kizo mu tafi"
"Ni bazan tafi ba" ta fada a tsiwace Umaimah ta daki bayanta ta zabura dan taji zafi ta kalleta tace
"Wuce ku tafi, daman karki fasa halinki kinji ko" hawaye ya zubowa yarinyar se kuma Jikin Umaiman yayi sanyi, duk cikinsu ita ce me qulafucinta sauran basu wani damu da rashinta a gidan ba ko sun damu basa nunawa ita kadai take damuwa da son ta koma gidansu.

Hijabinta ta zura dogo jin sun fito daga dakin Maman. Mu'ayyad ya shiga ya fara daukar musu kayansu yana fita dasu ta fito masa da ragowar qofar dakin ta tsaya. Kanta na qasa tana jin suna sallama da Mama, bata so ta dago balle taga abinda ze sosa mata rai, dariya da kuma muryar Khalil dataji dab da ita ta sakata dagowa ba tareda ta shirya ba. Yana riqe da Abid yanayiwa Humairan magana fuskarsa a washe ita kuma tana dariya wani abu ya dirar mata a zuciya amma tayi qoqari ta hadiye jin Humairan nayi mata sallama ta amsa yanda be kulata ba haka itama ta dauke kanta har suka fice daga gidan kafin ta koma daki tayi shiru.
Wunin ranar haka tayi shi babu dadi, ga kewar yaranta ga tasowar tsohon tsumi, duk yanda taso tayi baccin a daren ya gagareta. Ta tashi tayo Alwala tayi salloli, qarfe uku da wasu mintina haka kawai ta dauki wayarta ji takeyi tamkar idan bata kirashi ba zata iya madewa hannunta na rawa qirjinta na bugawa ta dannan kiran muryar matar kamfanin Mtn ta shaida mata da cewar layin a kashe yake, seta sauke ajiyar zuciya me nauyi ta kifa kanta tsakanin cinyoyinta hawaye suka shiga yi mara tsere. Ta dade tana kukan daga qarshe ta lallabi kanta tayi haquri.

Babu zato Abba ya bata offer aiki a qarqashin Ma'aikatar sadarwa ta Jaha. Ranar rasa abin cewa tayi se kuka da godiya kawai dan abin yazo mata a bazata, bata san da zancen neman aiki ba bata ma taba zaton za'abarta tayi aiki ba se gashi Abban da kansa ya nema mata seda komai ya kammala kafin ya sanar dasu. Inda gizo yake saqar rashin sanin ta inda zata fara, se take ganin kamar ba zata iya ba amma da Abban ya zaunar da ita ya sake yi mata nasiha tareda gargadi seta samu nutsuwa a ranta. Kafin ta fara zuwa aikin seda Salman ya sake koya mata abubuwan computer dan tace ta manta komai abin Mamaki kuna daya fada mata zata tuna yanda akeyi kodan tana buqatar aikin ne yasa kwakwalwarta tayi qoqarin tuna duk abinda ta sani a baya cikin qaramin lokaci oho, a haka ta fara fita aiki wanda hakan ba qaramin taimakonta yayi ba dan a dan lokaci Walwalarta ta fara dawowa, yanayin aikin da mutanen da take mu'amala dasu suka taimaka mata matuqa gurin fuskantar gaba ta dena tuna bayanta.

Qarfe tara take fita ta taso hudu dan haka zatayi Breakfast, an cire mata shara da wanke wanke se kuna girkin dare idan ta dawo wata rana ma yin abinsu sukeyi basa jiranta musamman Anty takance ta gaji taje ta huta kawai tayi abinta. Albashin da ake bata ya matuqar taimaka mata, bata da matsalar suturu dan yanzu datake fita nema take saka kaya dan haka ta dinka dogayen Hijabai har qasa kaloli masu kyau dasu take zuwa aiki yanda ta kame kanta bata shiga sabgar komai da bata aiki haka magana ma ba kasafai takeyinta ba se abinda ya zama dole hakan yasa kowa a gurin yake mutuntata.

Da sallama ta shiga office din Hajiya Huda zata kai mata wasu takaddu data buqata, Cike da tsananin mamaki take kallon matar data kira sunanta tana zaune akankujera tana zabga mata murmushi. Umaiman ta gyara tsayuwarta tana sake kallon matar. A jikinta tana jin tabbas ta santa a wani guri amma ta kasa tuna ina ne. Hadiza ta qara fadada murmushinta tana cewa
"Baki gane ni ba ko Umaimah? Hadiza ce, shekarun da yawa kin ganni na zama qatuwa duk wanda ya dade be ganni ba se yayi da gaske yake ganeni"

Qirjin Umaimah ya buga da qarfin gaske da jin sunan matar, Numfashinta ya tsaya na wani lokaci har bata san sanda ta saki takaddun hannunta ba kafin ta shiga jansa da qarfi jin sunan Hadizan kadai ya haifar mata da wani yanayi tareda shigar da ita rudani na gaske, lura da hakan ya saka Hadiza miqewa ta kama hannunta tana cewa
"Lafiya dai ya naga kamar bakiyi murna da gani na ba?"

Idon Umaimah yayi rau hawaye suka shiga sakko mata, so take ta bude baki amma ta kasa cewa komai se kawai ta fashe da kuka, Hadiza ta sake kallon Umaiman cikin yanayin nuna rashin jin dadi tace
"Kiyi haquri, ban dauka ganina ze bata miki rai ba, tunda na shigo na ganki kafin nayi miki magana kika shiga wani office na bari se zan fita se mu gaisase kuma gaki anan amma kiyi haquri, da nasan bazakiji dadi ba da ban miki magana ba" ta sake hannun Umaimah tana yunqurin tashi se Umaiman ta damqe hannunta lokaci daya ta durqushe a gaban Hadizan cikin tsananin kuka tace
"Dan girman Allah ki yafe mun, nayi nadamar abinda na aikata miki a kullum cikin Addu" a nake Allah ya hadani dake ya bani ikon neman yafiyarki gashi yau ya amsa mun Addu'ata ki yafe mun" ta qarasa tana riqe qafar Hadizan dake qoqarin dagota amma ta kafe taqi tashi.

"Dan Allah ki tashi kar wani ya ganki haka, Anty Huda kiyi mata magana ni zumunchi kawai nazo muyi ba tayar miki da hankali ba ki tashi koma wace magana ce se muyi a zaune dan Allah" Hadizan ta sake fada, dakyar ta samu Umaima ta zauna a kan kujera har sannan hannunta riqe dana Hadiza tana kuka kamar me ta sake cewa
"Haqqinki ne yake bibiyata, na rasa aurena, uwa uba na rasa mutunchina Khalil din da nayi hauka akansa na rasashi ina Ji ina gani ya zama mallakin wata bani ba. Dan Allah ki yafemun Hadiza ko zan samu sauqin rayuwar da nake ciki".
Chapter 254 · 0% Book details