Sashe 192
Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ranar da aka cika sati guda da daurin auran ta kama Juma'a, kamar yanda ya saba yana ya tashi daga Masallaci ko office be koma ba ya wuce gurin Humaira. Yunwa yake ji sunyi waya ya gaya mata dan haka tace zata hada masa Lunch, a cikin satin nan har wata yar qiba yayi ta kwanciyar hankali har tunani yakeyi shib baze yuwu ba aci gaba da tafiya a haka ba tareda Umaimah tasan da batun auransa ba? Shi a nasa bangaren bashi da Matsala tsaf ze iya dauke Humairan ya ajiyeta inda koda wasa Umaimah ba zata tana sanin da zamanta ba haka kuma ze iya takunsa kamar yanda yakeyi a yanzu ba tareda ta gano ko ta zargi wani abu ba amma matsalar yasan babu me bashi goyon baya akan hakan.
Jiya seda Hajiya tayi masa magana akan ya kamata zuwa yanzu yasan matsaya akan maganar auran saboda sunyi waya da Mama Hauwa kuma a cikin hira ta kawo mata zancen son sanin inda ze ajiye Humairan saboda su san shirin da zasuyi nayi mata kayan daki. Rasa abinda ze cewa Hajiyar yayi a zuciyarsa so yakeyi yace mata ita da kanta ta sanarwa da Umaimah maganar auran idan wannan qurar ta lafa daga baya se azo ayi ta zancen inda ze ajiye amarya amma ya kasa.
Jalilah tayi masifar tayi bala'in lusari ko ta kirashi yafi sau cikin kwando akan ya tsaya tsoron mace ya kasa tabuka komai, badan iyakar da Haiya tayi mata shiga sabgar gidansa ba da tuni ta fasan kwan kowa yaji amma ko yanzun lokaci ta basu idan taga sun gaza zatayi musu aikin dan babu yanda za'ayi a bar yarinyar mutane da aure yana zagayawa yana lalubeta ya kasa yin jarumtar da ze kawota cikin gidansa a cewarta kenan.
A falo tayi masa masauki kamar koda yaushe, irin kwalliyar da tayi dole ya kasa riqe kansa a gaban Unaizatu ya rungumeta kunya kamar qasa ta bude ta shige ita kanta Unaizatun babu shiri ta basu guri ya zauna akan kujera kafin ya dorata akan cinyarsa yana kallon fuskarta da tasha light make up. Dinkin doguwar riga ne a jikinta na wani Burn orage din Lace ya karbi farar fatarta ya mata kyau mara misaltuwa ga qamshibta da yake gigitashi kullum suka rabu se yayi wankan turare a mota gudun kar yaje gida Umaimah taji wani qamshi na daban tsiya ta balle. A baki yau ta ringa ciyar dashi saboda gataz Khalil ya lalace a gurin yana kallonta kawai kamar wani soko, Allah ya sani dauriya yake ba yar kadan ba amma da tuni ya dade da daukarta sunje wani gurin ya kashe qishinta daya addabeshi amma bazeyi hakan ba, yafi so ta samu kulawa kamarta kowacce Mace me gata ya kwanta da ita a cikin gidansu kan Gadon auransu dalilin daya saka ya rage aikin daya dakko kenan a gidan da yake so ya ajiyeta, Bene yaso ya dora amma ze ja masa lokaci dan haka ya barshi a flat din da yake amma ya canza masa fasali kuma yana saka ran aikin ze kammala a qasa da watanni biyu in Allah ya yarda.
"Wannan kallon fa haka kamar zaka cinyeni" Humaira ta fada cikin salon kissar da Anty Mariya da Unaizatu suke koya mata, seda ya gyara zama saboda yanda muryar ta shige shi kafin yace mata
"Kyau kikayi mun ji nakeyi kamar na daukeki mu tafi kawai"
"Mu tafi ina?" Ta tambayeshi tana bude ido seyaja hancinta yace
"Gidana mana ko ba zaki bini ba?"
"Aini banga alamar kanaso na kasance a gidanka ba dan babu wani shiri da naga kanayi" ta fada tana kallon gefe. Mamakin maganarta yayi se ya janyo wayarsa yana cewa
"Waya gaya miki haka? Kin san yanda abubuwa suka faru so fast ban taba tunanin za'ayi haka ba amma kalla ki gani tuni har anyi nisa a gyaran gidanki ke baki san na fiki qaguwa da ki tare bako kawai dan kince ke ba zaka zauna da matata bane da kawai bangarena zan bar miki kiyi zamanki a sama" ya miqa mata wayar bayan daya kunna mata video aikin gidan da akeyi.
Baki ta tabe bayan data gama gani ta sake cewa
"Wancan ai gidan matarka ne kaima da kank kana fada kuma ni bana raba abu da wani na fison nawa ni kadai"
"Gashi kuwa kin yiwa wata kwacen Miji" ya bata amsa cikin zolaya seta gimtse fuska tayi masa shiru wato abun ya motsa.
"Haba mana karki bata ranki hak kawai muje ki dan rakani wani guri mana" ya fada yana jan kumatunta seta miqe ta shiga tattara kwanukan da yaci abincin. Bayan dogon gargadi da jan kunne data sha a gurin Unaizatu suka fita taren, gidan Jalilah yakaita data kwarzabeshi akan seya kawo mata ita zasuje a aunata ayi mata dinkunan fitar biki. A gidan ya barta saboda Anwar daya kirashi suna da wani emergency daga qarshe se Khalifa ya saka yaje ya mayar da ita saboda Magriba tayi kuma har sannan be gama abinda yakeyi ba.
Yana komawa gida ya tarar da saqon Baba Abu da yaje be same shi ba, kamar yanda ya barwa Hajiya saqo cewar sunyi waya daga can Jalingo Alhaji Musa ya kirashi yana tanbayarsa gurin zama zasu siyawa yarsu Gado sun kuma tambayi Mama Hauwa ta sanar musu Basu rigada sun nuna guri ba dan haka ya kirashi da kansa dan yaji. Baba Abun ya bar masa sallahu bayan da Hajiya ta gaya masa shirin Khalil din na raba gida yana kuma kan aikin gyaran inda ze saka Amaryar ne. Baba Abu ya ringa fada yana cewa
"Wane irin gurin zama kuma yana nufin duk girman gidan nan babu daki fmda ze sakata a ciki ina a can sama ma a kwai bangare guda nasa ko kuwa ita uwar gidan duk ta baza kaya a ciki? To idan ma ta baza se ya gaya mata ta kwashe dan ba zan dauki wannan sakarcin ba a bar yarinya qarama da aure wannan ai ba girma bane duk karamcin da iyayenta suka mana bayannaje na gama cika baki akan a shirye yake shine ze zo da wani sabon shaqiyancu? Ni wlh ban zata za'a ci kwana uku ma be san abinyi ba gashi har sun gaji sun magantu to yazo ya share mata daki a nan a basu suyiwa yarsu jere yawwa".
Mamaki be kashe shi ba seda yaji cewar har a sannan matar gidan bata san da halin da ake ciki ba seya miqe yana cewa." Wannan kuma ya rage nasa da yasan be isa ba ya dakko abin Isassu? To ki gaya masa tun wuri idan ze ari Jarumta ya sanar mata yayi idan ba haka ba ni nan zanzo da kaina na shigo mata da Amaryar se muga qaryar boye boye, ki gaya masa na bashi daga nan zuwa rana irin ta yau Takwararki ta tare a dakinta idan ba haka ba kuma ze gamu dani".
Da wannan maganar ya kwana a ransa, idan ta qure dole ya ajiye Humaira da Umaimah a gida daya na wani lokaci amma ta yaya yanzu ze sanarwa da Umaimah wannan al'amari? Shine babban tashin hankalinsa da tunanin yake kwana yake tashi a kullum kuma ya tabbata dole komai dadewa maganar zata fito idan be gaya mata da kansa ba Baba Abu ya shammaceshi kamar yanda ya fada ya kuma san ze aikata kai qaramin abu ne daga ayyukansa ma.
*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*
*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼
Page 69
Yanda yaga rana haka yaga dare washe gari kuwa qarfe shida ya fita daga gida bayan ya shiga bangaren Hajiyarsa ya sakeyi mata magiya akan ta kira Umaimah da kanta ta gaya masa maganar auran.
"Babana kaida kake Mijinta ka kasa gaya mata se ni kake so na debi baqin jini bayan wanda na rigada nayi? Idan ba zaka iyaba ka kira Jalilah nasan da murna zatayi maka wannan aikin amma ni kagan ni nan idan ka shirya gaya mata ma ka sanarmun dan na bar gidan ranar kar tsautsayi ya rutsa dani" amsar da Hajiyar ta bashi kenan se kawai ya zabi daya bar gidanya tafi can wani gurin ya samu damar yin tunani da kyau.
Can kan hanya ya samu inda babu hayaniya ya faka motar ya lula cikin tunani. Duk Abokanansa daya nemi shawara amsa daya suke bashi akan wai ya sameta suyi magana ta fahinta ya nuna mata qaddara da muhimmancin yarda da ita sannan ya nuna mata cewar beyi aure danya wulaqantata ba ta qaddara cewar Allah ne ya hukunta faruwar hakan kuma ba zaka tsallake ba to idan banda abinsu a yaushe a kuma wanne lokaci zata samu nutsuwar fahimtarsa?
Ya tabbatar daga inda ya faro mata wannan nasihar tasan inda ya dosa ba duk kuma abinda ze biyo baya ya tabbatar da be me kyau bane.
Allah sarki Yaya Aminu, da ace yana raye kai tsaye gurinsa ze tafi ya kai kukansa kuma ya share masa yau gashi baya nan a lokacin da yake tsananin buqatarsa ya kuma kasa zama Jarumin da har a maganarsu ta qarshe seda ya goranta masa. Shi dai indai a gurin Umaimah ne baya zaton ze taba zamowa wannan Jarumin yanzu bayan Yaya Aminu se waye fada mata taji kuma tayi babu ja'in ja?
Mama Malika ce ta fado masa a rai, sosai kuma yayi na'am da shawarar zuciyarsa dukda wani bangaren yana so ya hanashi dalilin nauyi da kunyarta da yake nema ya kamashi. Yana ganin rashin kyautawar ba iya Umaimah yayiwa ba ita kanta Maman abin ya shafeta amma dukda haka uwa uwa ce yasan kuma a karamci irin nata ita kadai ce zata fahimce shi kuma ita take da kalaman Ladabtarwa da zatayi amfani dasu gurin kwantar masa da hankalin Umaimah.