← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 225 OF 267

Sashe 225

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salman daya shigo ta cewa ya kama mata suka kaiwa Maman ta bude ta kalli uwar Shinkafar data dafa ta zarce awon Abincin da suke sakawa koda ace duk yaran gidan da iyalansu suna nan ga girkin babu kai bare qafa, Babu mai a ciki yaji kamar yayi magana sannan bata tsammanin ta saka Maggi salam yanda kasan girkin Asibiti na masu Hawan Jini ko ciwon Sugar.
"Kirawo mun ita" Mamanta fada cikin tsananin bacin rai, se Anty Amina tayi saurin cewa
"Dan girman Allah Mama ki kyaleta, ta rigada tayi abinda take so zuwan ta nan babu abinda ze canza illah ya qara miki bacin rai da damuwa shiyasa nace ki bari muyi girkin amma yanzun ma Kiyi haquri bari na tashi na dora ko Taliya ce aci ki barta dan Allah".

Badan Maman taso ba ta barsu suka fita su ukun suka fara kiciniyar dora sabon girki, Nuratu ta gyaro Kitchen din ta fito da kwanuka ta taresu gurin wanke wanke su kuma suka hura wuta suka dora Sanwa suna aikinsu suna yan hirarraki dan basu bari Abinda Umaimah tayi ya bata musu rai ba, nan da nan suka gama tsaf suka raba kowa aka saka masa Nasa, Maman Asadta kaiwa Anty nata daki suka gaisa cikin mutuntawa da Fatiman dake ta zubawa yar uwarta qorafi akan Umaimah suka sallami duk sauran yaran kafin suka saka nasu a babban Try sukaci. Bayan sun gama Nuratu ta hado kan ragowar kwanukan zata wanke Mama ta dakatar da ita. Da kanta ta wuce dakin Umaimah, tana kwance daidai a Gado cikinta na juya mata saboda yajin data nada gana abinci ga wanda ta qara dan ta samu abincin ya ciwu mata Mama ta shiga da Sallama ta tsaya akanta tace
"Tashi kije ki wanke kwanukan da aka bata".

Bata musa ba ta biyo bayan Maman ta kalli uban tulin kwanukan a bakin famfo ga wata babbar tukunya bayan wadda tayi girki da ita ta tabe baki ta zauna tana shafa kwanukan kamar me wasa, tun ana dab da kiran La'asar ta fara ba ita ta gama wanke wanken ba se ana Haramar shiga Magrba shima ganin Laqai laqai din nata na mafita bace yasa ta ware ta shigayi tana hawaye tsabar wulaqanci tanayi ana qaro mata wasu seda ta Zagi Salman daya shigo da kwanuka daga dakinsa wasu ma da gani sunfi Sati ba'a wanke ba dan har wari suke ko a jikinsa ya ajiye mata aiko ta ware su gefe ta rantse ba zata wanke ba. Duk tana zaune yayyenta kowacce tayi Harama ta tafi gidanta. Bayan ta gama dakyar ta tashi daga gurin ta bar kwanukan. Seda ta watsa ruwan Zafi ta gasa jikinta dan an kawo wuta kafin ta iya yin Sallar La'asar da Magriba tana shirin aje haqarqarinta ta huce gajiyar girki da Wanke wanke Sharifa ta sake shiga fuskarta a washe da alama tana jin dadin aiken zuwa kiran Umaiman tace

"Mama tace ki fito ki dora Tuwan dare"
"Na rantse da Allah se naci kutumar ubanki idan na riqeki" ta fada cikin tsananin fushi tana tashi zaune muryar Abba ta jiyo daga waje yana cewa
"Gani a kusa fito kici uban nata kuma karki fito kiyi abinda tace kinji".
Kuka daya riga ya zema mata jiki ta fasa amma bame qara irin na jiya ba, jikinta kamar ana sarata haka take ji bata warke daga jinyar dukan data ci jiyan ba ga Azabar aiki an tasota a gaba. Harta sauke tuwon tana kuka, Miyar dai yanzu ta saka musu maggi dukda bata dan dana taji yanda yayi ba gurin kadin ne daman ita hannunta baya yauqi dan haka kubewar ta tsinke kamar Romo, ta Jibge Tuwon a Kula gaba daya ba tareda ta Malmala ba danma na Semovita ne amma dukda haka jikinta ya gaya mata gurin tuqin tana gamawa ta tsallake komai a inda yake ta wuce daki harda kwanukan data wanke tun dazun bata kau dasu ba. Seda ta shiga dakin Mama dake lura da duk abinda takeyi ta fito.

Ta bude tukunyar Miyar ta dandana, kai kawai ta girgiza ta maidata kan wuta ta qara abinda ya kamata ta kuma daureta sannan ta sauke ta shiga rabon tuwon dan Goma ake nema a lokacin daman badan Abba daya ce setayi girkin ba batayi niyar sake jira ta kwashi takaicin Umaimah ba da tuni ta gama girkinta.

Guraren sha daya tuni tayi nisa a bacci dan tana shiga dakin ta kife tana kukan takaici a haka baccin ya kwasheta kiran sunanta taji anayi tareda bubbuga qafarta ta bude ido dakyar dan bata da Nauyin bacci taga Ummu-Salma tsaye, seda ta tashi zaune da kyar kafin Ummu-Salman tace
"Anty Umaimah kije inji Abba"
"Inje kuma Me zanyi masa?" Umaiman ta fada tamkar zata fasa kuka wannan wane kalar bala'ine?
Ita dai Ummu-Salma na tsaye a gefe, bata dade da shigowa gidan ba ta taho daga makaranta Dutse take FUD tana Final Semester dinta Motarsu ta lalace se goma ta iso tana shirin kwanciya Abban ya ce ta kirawo masa Umaiman.

Seda ta gama qunquninta da qananun hawaye kafin ta miqe tana layi ta fita, tsoronta karya sake mata irin dukan jiya da babu inda zata wlh haka ta isa falon Abban suna zaune tareda Mama da Anty ga Kular abincin ranar da tayi a gabansa tana kallon fuskarsa gabanta ya fadi saboda fushin data gani akanta wai shi da Bashi da lafiya dan Allah baze sararawa zuciyarsa haka ya dena fushi ba? Qasa ta samu ta rabe idonta har sannan yana yajin bacci Abban ya fara magana cikin fada yana cewa
"Wato saboda ki nuna ke bakya ji duk kuma abinda aka ce kiyi sekin bata wa mutane rai shiyasa kikayi haka ko? To bari kiji daga yau kamar yanda na fada miki zan sake jaddadawa aikin gidan nan kaf ya rataya a wuyanki kuma Tilas kiyishi akan lokaci sannan a mutunce yanda kikaga iyayenki sunayi.

Karki kuskura qarfe bakwai tayi baki gama abin karyawa ba a ranakun makaranta sannan duk rintse karki wuce biyu ba tareda kin sauke na rana ba haka na dare kin sani kafin na dawo daga Sallar Isha'i an ajiye mun abinci. Sannan maganar wanke wanke da shara bana so na sake maimaita miki daga yanzu kinsan yanda akeyinsu Kwanukan da kika ajiye tun Yamma kuma suna nan suna jiranki ki gyara su yau kin samu yan uwanki sun rage miki aiki gobe basa nan ke zakiyi komai kuma ki yarda kiyi wani abu da ba haka ya kamata ba zamu gauraya a cikin gidan nan maganar wannan abincin kuma( ya nuna kular gabansa yace) daga yau har zuwa sanda ze qare shine abincinki a cikin gidan nan Umaimah koda ace zeyi tsutsa Wallahi se ya qare zan ci gaba da baki abinci a cikin gidan nan idan kuma kika ci wani abu nawa ba tareda umarnina ba Allah ya isa"

A firgice suka kalleshi gaba dayansu Anty tayi saurin cewa
"Haba Alhaji me yayi zafi zakayi mata Allah ya isa akan Abinci?"
"Sharadi na bata idan kuma idan har ta qi bi na maimaita Ban yafe ba" ya sake fada cikin tabbatarwa se aka rasa wadda zata sake magana a cikinsu se Umaimah data rushe da sabon kukan tashin hankali dan lamarin kam ya girmama ya zarce tunaninsu, Abba kuwa ko a jikinsa yaci gaba da cewa
"Sannan komai ruwa komai Iska da Itace zakiyi girki ban yarda ki sake kunna mun Gas a gida ba tunda bada kudinki na siya ba wanda kikayi amfani dashi yauma se kin biyani".

Anty da Mama dai sun rasa ta cewa Umaimah ko kallonsu takeyi a qoqarinta nason su roqa mata sassauci akan wannan lamari ina zata kai wannan shinkafa da ta ranar ma dakyar ta iyaci muguntarta ta qare akanta kenan ai wlh gara yace ta biyashi kudin shinkafar kawai da wannan tsatstsauran hukunci ita zancen karta kuma ci masa abinci ma be dameta ba tana da yan kudadenta zata iya ciyar da kanta na tsahon lokacin da yace amma zancen tayi ta cin shinkafa ai bema taso ba. Ganin Abban ya miqe Alamar zeje ya kwanta kuma har sannan Anty da Mama basu roqa mata sassauci ba yasa ta zabura cikin kuka me tsanani tace

"Dan girman Allah Abba kayi haquri wlh bazan iya ci ba na yarda ayi lissafi zan biyq duk kudin amma ka barni na fita dashi na bawa Almajirai" s Abban ya dakata ya juya ya kalleta fuskarsa babu yabo babu fallasa yace
"Wato saboda su basu da uwa da uba a kusa shine zaki basu abinda kika kasa ci ko? To ban yarda ba kuma ban janye maganata ba" daga haka ya shige cikin dakinsa ya barsu. Anty tayi tsaki qasa qasa ta miqe ta fice daga falon Mama ta bita da kallo a ranta tana ayyana idan ba'ayi wasa ba Umaimah na shirin rusa zaman lafiyar da sukeyi a cikin gidan dab tun a daren jiya ta lura da Anty ta kai maqura da Al'amuran Umaiman dan a daren jiya da Abban ya yanke jiki ya fadi bayan ya fito daga wanka Allah ya rufa Asiri Antyn na tsaye ta kai masa ruwan shayi ita ta tareshi tana kuka take cewa Maman
"Gaskiya kija mata kunne ta dena dagawa Alhaji hankali haka dan idan ya mutu bata da Asara ke kanki kukanki kadan ne dan duka yayanki kin aurar kuma suna da Madafa nice me qananan yara" tun a daren Jiyan maganar take nuqurqusarta amma ta shanye ko su Nuratu bata gayawa ba ta kuma tabbatar dalilin da ya saka dazu har Sharifa take sake maimaitawa Umaiman cewar karta kashe musu uba kenan qila ita Antyn tayi zancen da yayanta.

Gajiya da kukan da Umaiman takeyi ya saka Maman miqewa ita ma se ta zabura ta bita har suka je bakin qofar Maman bata dena gunjin kukan ba ganin tana shirin shigewa daki ta barta yasa cikin kuka tace
"Dan Allah Mama dan darajar Manzon Allah kisa baki Abba ya haqura na bawa Almajirai abincin wlh bazan iya ci ba ni na yarda kar a bani abinci har tsahon lokacin daya kamata na cinye wannan din".
Chapter 225 · 0% Book details