← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 267

Sashe 19

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

koma dai yaya shidai he is done with anything concerning Umaimah, yana sonta amma dole ya haqura da ita dan beyi zaton Rigima da Hayaniyarta da Nasir ya ke fada ba ya kai haka. Koda yake ya so ya rufe shi ne amma banda haka ai kaitsaye kawai kamata yayi yace masa tana da matsalar saiti.
Gata dai mace har mace amma babu cikakken hankali Allah kenan me yanda yaso.

Haka ya juya Asibiti bangarorin zuciyarsa na mahawara da juna, tabbas yana son ta so me tsanani amma menene amfanin soyyar da babu kwanciyar hankali da girmamawa a cikinta. Idan ya tuna yanda take riritashi tana lelen sa idan suna yar dadi se yaji kamar baze iya rabuwa da ita ba, amma abinda tayi masa dazun ya saka shakku a zuciyarsa game da auranta.

Tayi kishi da yan uwansa na jini inaga kuma duk randa tsautsayi yasa ta ganshi da wata, bama wannan ba ita rayuwa bata da tabbas. Har zuciyarsa bashida burin ajiye mace sama da daya musamman ace Allah ya cika masa burinsa ya bashi mace irinta amma babu wanda yasan gobe, idan qaddarar sa ta auran mace sama da dayan ce fa yaya zasu kaya?

Yanda yanzu kullum ya kunna radio labarai ne marasa dadi akan mata sun kashe mijin ko sun kashe kishiyar toh maganin kar ayi kar a fara, indai soyayyace ze roqi Allahn daya saka masa ita a zuciyarsa ya cire masa ita kuma ze ci gaba dayi mata fatan Alkhairi ubangiji ya rage mata abinda yake damunta a zuciya amma tabbas baze siyawa kansa tashin hankali da kudinsa ba amma ta yaya ze tunkari Hajiya da wannan magana yanda take son Umaimah kamar ta goyata?

Bama wannan ba, gaba daya fa auransu befi sati hudu masu zuwa ba anya idan yace ze fasa yaya iyayenta zasuji dan shi su yafi tausayawa, mutanen kirki, Mamanta ta dauke shi kamar dan cikinta basu boye masa komai akan Umaimah ba tun fara zuwansa gurinta dan hatta da takaddun Asibitin gwajin kwakwalwa da aka mata seda Abba ya nuna masa amma sam shi be fahimci Al'amarin ba, be taba zata haka abin nata yake ba se yanzu da tafiya take qara nisa daman hausawa sunce Hali zanen dutse ashe lokaci take jira ta fara zayyano masa su, toh koma dai menene ze jira a sallami Hajiya ta koma gida kafin yaje mata da wannan maganar.

A can gidan su Umaimah kuwa rigima ce sosai ta sarqe tsakaninta da Nuratu dan tsayawa tayi daga cikin Gareji Nuratu na shiga ta hau kanta da kokawa itama batayi wata wata ba kuwa ta zage suka fara kwasar dambe dan a zuciye take da lamarin Umaiman, tayaya zatayiwa kanta asarar miji kamar Khalil wanda tasan muddin ta rasa shi bazata maida kamar sa ba sannan rantsuwar Abba ta bada ita sadaka ta tabbata kenan.

Dambe sukeyi haiqan har cikin gida sosai kuma Nuratun ta zage tana jibgar Umaimah dan ko a qirar jiki zubinsu ba daya bane. Nuratu doguwa ce me garin jiki dan ta ninka Umaiman da tsabar tsaurin ido ne ma ya sakata cukumarta da dambe.

Sosai ta lallasata, dan takaicin shekara da shekaru ta samu dama tana sauke mata shi yau akayi sa'a babu kowa a gidan dan suna fita ba dadewa akayi rasuwa a bayan layi dab haka su Mama da Antyn sun tafi Jana'iza se Salis ne kadai a gidan Dan Anty na biyu da suke sa'anni da Umaiman, shi kuwa yana leqowa daga dakinsu yaga abinda yake faruwa ya koma ciki harda turo qofa.

Yaya Aminu ne yaje gidan, tundaga waje yake jiyo ihu da kururuwar Umaiman tana zagin Nuratu a ransa yace "abin ya motsa kenan, ai kuwa yau zaki ci ubanki daman ina da cikin ki ai" se ya juya ya koma motarsa. Dorinar da yake ajiyewa saboda horon yaran sa idan ta kama ya dakko har wani murmushi yake yana hasaso irin dukan da ze mata kafin su Mama su dawo dan sunyi waya ta gaya masa sunje jana'iza amma gasu nan zuwa.

Yana shiga kuwa beyi wata wata ya shiga sakar musu duka kan me uwa da wabi saboda yanayin daya tarar dasu gaba daya kowacce jikinta na buqatar ya gaya mata. A zabure kuwa suka rabu kowacce ta hau sosa jiki dan dukan ya shige su musamman da daman rabi kaya rabi tsirara suke dan tun a Get aka tuge Hijabai da dambe yayi dambe kuwa aka ringa farke farken kaya.

"Ashe baku da mutunchi a cikin gidan kuke mana kokawa se kace wasu yan tasha?" Ya fada a fusace yana kallon yanda kan ko wacce yayi buzubuzu kamar sababbin kamu se sosa inda ya tsula musu bulala suke, jikin bango suka maqale kowa tana sosa jiki, ya sake kallon Nuratu yace
"Harda ke ina miki kallon me hankali ashe zama da ita yasa kema kin koyi hauka ko? Uban me ya hada ku fada?" Ya daka mata tsawa, se Umaimah ta fashe da kuka tace

"Wallahi Yaya babu abinda nayi mata kawai ta hau ni da duka..." Bulalar ya kai mata duka da ita tayi azamar gocewa ta fada dakinsu da gudu tana masa Allah ya isa a zuciya. Kan Nuratu ya juya ya shiga surfa mata masifa uffan batace ba har yayi shiru dan kansa kafin ta miqe ta shige dakin Mama dan tasan idan ta shiga nasu Umaimah na ciki tabbas fada be qare ba shi kuwa Yaya Aminu samun su zeyi kamar jakai ya lafta.

Baafi minti sha biyar ba kuwa su Maman suka dawo, Aminu ne ya fada musu abinda yazo ya tarar se a sannan Salil ya fito daga daki yace "Umaimah ce da laifi dan ta riga Yaya Nuratu shigowa ta labe a bakin qofa se ji nayi sun kaure da dambe".

"Ai ko baka fada ba daman nasan itace da tsokana amma itama Nuratu da laifinta akan me zata biye mata har suyi dambe se kace wasu qananan yara" Maman ta fada.

"Ki qyale su Allah ya taimaki wata yarinya ta sake mana dambe a gida wallahi se jikinta ya gaya mata dan se nayiwa mutum mugun duka a gidannan" Aminu ya fada, daki Mama ta wuce yabi bayanta bayan sun gaisa da Anty.

Nuratu na ganin Maman ta saka kuka, babu bata lokaci ta zayyane mata duk yanda akayi a Asibiti da abinda Khalil ya gaya mata a hanya harda dalilin yin damben nasu.
"Ai shikenan" Mama data gama saurarenta ta fada tana miqewa tsaye, Allah kadai yasan abinda taji a zuciyarta se kuma wanda Ubangiji ya jarabta da fitinanniyar yarinya irin tata.

"Ai kuwa sena ci ubanta yau a gidan nan, kuma bata isa ba a wannan karon ta sake lalata magana tunda naga abinnata ya zamana tsantsar iskanci tana da buqatar a dawo da ita kan hanya" Aminu ya fada afusace yana miqewa shima se Mama tayi saurin dakatar dashi da cewa

"Karka kuskura ka taba ta, baka ji abinda akace bane shima yaron yace ya fasa toh ka barta zaman gidan nan ne ko gata gashinan. Kuma kar naji zancen a bakin wani koda mahaifin ku ne kuwa, idan sunzo da kansu sun janye a lokacin ya sani. Amma Umaimah koh idan har ta bata wannan auran bazata maida kamarsa ba" ta qarasa maganar cikin rawar murya tareda daga kanta sama a qoqarin ta na dakatar da hawayenta daga zubowa dan daman daga yanayin muryarta suka gane kuka ne yake neman zuwar mata abinda ya qara sanyayawa Aminu da Nuratu jiki.

"Dan Allah Mama karkiyi kuka, kin sani hawayen ki masifa ne a tattare da ita addu'ar dai ita zaki ci gaba dayi mata in sha Allahu wata rana se labari" Aminu ya fada sedai kamar me jira kuwa kukan ya kwace mata tace
"Na gaji, nagaji Aminu da halin qanwarku. Kullun ta Allah da zullumin ta nake kwana nake tashi a raina, yanzu idan aka fasa auran nan karo na hudu fa kenan me kake zato mutane zace a kanta? Ni kadai nasan irin qunci da baqin cikin nake fama dashi akan lamarin auranta yanzu ina murna yan satittika suka rage ta tafi shine ta ja gwalo abinda ze saka a fasa ko ai shikenan" tana gama fada ta shige daki tana ci gaba da matsar hawaye.

Nuratu dake nata hawayen a zuciyarta tana dana sanin sanarwa da Maman, amma tasan dole zata ji, kuma ita a nata dabarar ta fada mata da wuri ne saboda idan da yanda zaayiwa tufkar hanci ayi se gashi ta sake lalata al'amarin.

"Indai junin mutum munafunci dason ya hadani da uwata sedai abinsa ya qare masa in sha Allahu badai aga bayana ba sedai mutum yaga nasa, kuma aure na babu fashi duk baqin cikin mutum" Umaimah da basu san da tsayuwarta ba ta fada tana jijjiga jiki irin na tsabar fitsara da rashin kunya, Aminu ne ya yunqura kafin ya tarar da ita ta kwas ada gudu ta koma dakinsu harda sakawa qofa sakata dan tasan a yanda ya zaburo tabbas ya riqeta toh ko be kasheta ba se tayi dogon Suma.

Zama tayi akan gadonta gaba daya kuma seta rasa sukuni, hawayen da ta gani a fuskar Mama sun daga mata hankali dan ita ba jahila bace ba kuma mahaukaciya bace tasan illar da hakan ze yi mata wai me yasa a kullum itace sanadin Kukan Mama?
Bama ita kadai ba duk wanda ya tashi qorafi a gidan akanta ta fita zakka a cikin su goma sha uku da aka haifa a gidan.

Iya qoqari kuma tanayi gurin kaucewa duk abinda zaace tayi ba daidai ba amma sau tari ma tsokanarya akeyi idan ta maida martani kuma ace tayi laifi, ko kuma su dauki damuwar data shafeta su dorawa kansu kamar yanzu da wannan munafukar Yaya Nuratu taje ta fadi qarya da gaskiya ita sam bataga abin tayar da hankali a ciki ba. Aure ita ce me auren nan ko maza ashirin suka fasa auranta mijin tane bezo ba hakan kuma baze hana shi zuwa ba sannan maganar Khalil da tace ta fasa wasa takeyi bacin raine kawai yasa shima kuma tasan haka ne idan an barsu daga nan zuwa dare ma zasu shirya kansu amma shine Mama zata dauki damuwa har tana zubda hawayenta.
Chapter 19 · 0% Book details