← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 217 OF 267

Sashe 217

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Se bayan da akayi suna yaro yaci sunan Mahaifin Humairan Auwal suna kiransa da Aryaan, Gida ta koma tayi sahihin wanka Maman ta kula da ita sosai kuma taji dadi yanda a zaman Kwana Arba'in din dukta yanda zatayi ta bigi cikinta taji ko tanada wata matsala akan zaman da takeyi ta nuna babu, dukda tana so ace Humairan tayi Yaya da yawa saboda ita kadai iyayenta suka haifa amma ko iya haka ta qarasa rayuwarta da Khalil ta bar baya ba lallai se ta qara wata haihuwar ba zasu ci gaba da lallaba rayuwarsu a haka. Seda suka kwana hamsin kafin ta koma dan har Taraba seda sukaje yawon Arba'in, kiran da Khalil ya ringayi da zaryar da yakewa Maman tasa ta tattara masa matasa suka koma dan be qara sanin tasirinta a rayuwarsa ba seda ta tafi wankan gidan, jin sa ya ringayi kamar wani Maraya Hajiya kanta seda ta ringa tsokanarsa idan taga ya zauna ya rafka tagumi tace ya tashi ya tafi gidan Hajiya Hauwa mana sedai yayi dariya ya sunkuyar da kai dan shi kadai yasan me yake ji akan rashin matarsa kusa dashi.

Kwanci tashi akace asarar me rai se gashi Shekara ta cika, watanni goma sha biyu da Khalil ya nemi Alfarmar Umaimah ta shayar masa da Malika da suke kira da Iman sun cika. Zullumi ya shiga akan karbo yarinyar, tausayinta yake ji sosai saboda za'a rabata da mahaifiyarta tun bata san kanta ba amma hakan ya zama dole, yasan kafiya da Nacin Umaimah, tunda ta fada da kanta ba zata riqeta ba gara ya karbi yarsa cikin girma da Arziqi ya hadata da sauran yan uwanta shi kansa yana kewarta dan rabon da ya sakata a idonsa tun tana kwanaki a duniya. Ba'a taba kawota ba kamar yanda suma basu taba kai musu su Mu'ayyad ba tun bayan rabuwarsu kowanne bangate sun kama kansu sun zauna inda Allah ya ajiye su. A gurin Khalifa yake ganin hotunanta duk sanda yaje kaiwa Umaimah kayan abinci qarshen wata ze dauki yarinyar yayi mata hotuna ya nunawa Hajiya a nan shima yake samu ya ganta ta girka tayi wayo sosai kamanninta da Mahaifiyarta sun sake fita sedai kamar yanda kowa yake fada baya fatan Allah yasa ta kwaso zuciya irin ta Umaimah wadda sam babu salama a cikinta.

Yana kwance kan Gadonsa yayi nisa cikin tunani Humaira ta shiga dakin, qamshinta ne ya fara sanar masa da ita ce, ya bude ido ya kalleta tayi kyau harta gaji cikin doguwar rigar Atamfar data saka ga daurin nan ta kawo gaban goshi Umaimah ta fado masa, Humaira da Umaimah suna kamanceceniya ta wasu halayen kamar bangaren kwalliya da tarairaya idan fa yan mutunchinta suna kusa kenan sabanin Humaira da a kullum haka take cikin kyautata masa dayin duk abinda tasan ze faranta masa rai badan tana buqatar wani abu daga gurinsa ba. Ta qarasa ta zauna gefen Gadon tana murmushi tace
"Wai kana kwance har yanzu? Ka tashi kayi wanka ga abinci nan yana jiranka"

Mirginawa yayi kusada ita ya jata ta fada jikinsa yana kallon idon ta yace
"Kinyi kyau".
Yanda tayi farr da ido kamar Umaimah a duk sanda yayi complimenting nata seya miqe yana cewa
"Bari nayi wankan ki kawo mun abincin nan qyuyar fita nake ji"
"An gama ranka ya dade" ta fada tana miqewa ya rakata da ido yana murmushi seda ta kulle qofar sannan ya wuce ya shiga wanka yana yi yana tunanin karbo Malika, Hajiya bazata iya da hidimar yaran ba saboda shekaru da yanayin lafiya da tayi mata qaranci daman Habiba ce qarfin Kula dasu to yanzu ana maganar saura watanni biyu Bikinta data bar gidan kulawar yaransa zata koma kacokan hannun me aiki kenan dan baze iya bawa Jalilah ita ba kamar yanda take haqon in an dakko yarinyar ita zata karbeta, indai zeyi haka to gara ya barta a hannun Mahaifiyarta shi kuwa yana so ya hada kan Yaransa su tashi tare a gabansa.

Duk wannan abun uwarsu taja musu da tayi haquri da yanzu suna tare bashi da tunanin ya zeyi dasu, shawarar daya yanke ita ce ze kira Nuratu tunda ita ta kawo musu Ruqayya ta dawo taci gaba da Aikinta ya yaba da Qoqarinta yasan kuma bazata cutar masa da yara ba saboda ko a lokacin baya duk sanda suke a nan bangaren ita take musu duk wata hidima sun saba da ita.
Tsaf ya shirya, yana fesa turare Humaira ta shigo da qaton Try yayi saurin ajiyewa ya kama mata yana cewa
"Bakya tsoronsu zube kika hado kaya haka?"

"Ba gashi na kawo ba ai ba zasu zube ba" ta fada tana sauke kwanukan qasa ya koma yaci gaba da taje Sajensa ita kuma ta bude Warmer ta shiga zuba masa hadadden Dambun cous cous din da tayi. Ta mudubi ya kalli abimcin yawunsa ya tsinke ga wani qamshi na musamman daya karade dakin take yunwar da yake ji ta qara qarfi ya ajiye Comb dinya dawo kan Carpet din inda ta zuba abincinya tankwashe qafa yana cewa
"Gaskiya a bani a baki bazan iya ci da kaina ba"
"Da ze yuwu ma base ka tauna da bakinka ba kawai sedai kaji cikin ka ya qoshi amma babu komai Allah ya kaimu Aljanna" ta fada tana kai masa abincin baki. Haka ta ringa feeding nasa kamar wani qaramin yaro yana ci yana sakin murmushin da shikansa be san na menene ba kawai dai yasan dadi har ya masa yawa. Seda ya qoshi sannan ta barshi ta kwashe komai ta fita dasu kafin ta sake dawowa ta tarar dashi yana saka hula ta qarasa gyara masa zamanta tana cewa
"Kayi kyau da yawa Allah sa kar wata mace ta kalleka sau biyu idan ka fita" seya ja dogon hancinta yace
"Babu wadda zata kallar miki ni, muje ki rakani nasan Anwar na can yana jirana".
Haka suka fita ta rakashi har gaban motarsa tana masa Addu'a, se bayanya fita ya tuna da yanaso yayi mata maganar dauko Malikan dukda ta sani amma ya kamata ya sake tuna mata kar ta ganshi da yarinya kawai. Da dare suna kwance yake mata maganar nan tace tare zasuje, daman su Mu'ayyad nata cewa suna so suje gurin Momynsu, bata son masa maganar ne saboda taga duk sanda suka tambayeshi da kansu se ya nuna bacin rai dan haka yayi haquri ya tafi tareda su su ganta
"Yaya baze yuwu kace zaka rabasu da Mahaifiyarsu ba Alhalin tana raye, koni dana rasa tawa hat abada wani lokacin nakanji dama ta dawo badan na rasa komai ba sedai kawai dan ita uwa batada madadi" Humairan ta fada a hankali seya sake janta jikinsa sosai ya rungumeta ba tareda yace mata komai ba.

Ranar kuwa da tayi daidai da cikar Iman shekara daya bayanya dawo daga Masallaci yace mata su shirya ita da yara zasuje dakko Iman, irin Ihu da murnar da yaran suka ringayi ya sanyaya masa jiki matuqa saboda kiran yau zasuga Momy kawai suke suna tsalle. Tsaf Humairan ta shirya su cikin kyakykyawar shiga Mu'ayyad ya saka shadda irin ta Mahaifinsa ita kuma Bibi ta saka mata Gown kalar Lace din da ta saka a jikinta se suka fito kamar wasu furen fulawa da baza'a iya dauke kai daga kallonsu ba. Seda sukayiwa Hajiya sallama kafin suka kama hanya, kamar yanda ya saba duk lokacin da zeje gidan su Umaiman a wani super Market ya tsaya yayi musu siyayya sosai kafin suka dauki hanya yaran nata surutu suna gayawa Humaira wadanda zata tarar a gidan idan sunje a haka suka qarasa gidan su Umaimah.

UMAIMAH

Tana kwance a dakinta tana sana'ar ta ta danna waya dan bata aikin fari balle na baqi illa taci tayi wanka ta kwanta tana latsa waya. Tana nan kwance Anty ta shigo tana tambayarta rigunan sanyin Iman da Naziyya ta aiko mata dasu ta nunaww Antyn inda ta ajiyesu ta wuce ta dauka Umaiman ta bita da kallo dan tun jiya taga Anty nata kai komon har hada kayayyakin Iman, ko a jikinta bata nemi jin ba'asin dalilin hada kayan ba dan kusan wata biyu kenan data yaye yarinyar gaba daya ta sallamawa Antyn koda yake daman tsakaninta da ita shan Nono ne wanda shima se taga dama tsakanin Anty da sauran yaran gidan take gararanba har zuwa kan Mama da daga baya ta sauke fushin daya shafi harda Iman din ta rungumi yarinyar ganin cewar Uwarta tayi nisa a lamarin Duniya, duk abinda Anty zatayi mata kuwa karace ita din ce a haqqu datayi mata dan haka taja ta a jikinta sosai ya zamana sun raba hidimarta ita da Anty.

Tunda satin ya kama daman Hajiyar Khalil da sukanyo waya jefi jefi da Maman ta kira akan ranar Juma'a ne cikar Malikan shekara daya kuma kamar yanda suka Alqawarta zasu karbeta su hada da sauran yan uwanta a lokacin taji kamar ta cewa Hajiyar suyi haquri su bar musu yarinyar domin tana jinta a ranta ta maye mata gurin Uwarta data rigada ta sallama sedai nauyi da kunyar Hajiyar ya hanata furta hakan suka rabu akan zata sanarda Mahaifinsu Umaimah a ranar kuwa bayan Abban ya dawo ta gaya masa ta ce
"Amma da zaka roqar mana Alfarmu su Alhaji su bar mana yarinyar nan kaga mun saba da ita"
Chapter 217 · 0% Book details