← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 172 OF 267

Sashe 172

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ikon Allah" Umaimah ta fada a ranta wato su Ahalinsu gaba daya sun maida bin malamai sana'a kenan tunda gashi har gado sukeyi toh Allah ya kyau. Suna nan zaune mamakin jama'ar data gani yasa ta manta ma da abinda ya fito da ita. Wato dagaske Safina take da tace duk macen data cika ta tumbatsa tana da Malami ko Bokan daya tsaya mata yanzu lalacewar harta wuce kan Mata harda Maza a yawo gidan Malamai to ita dai ba zata iya ba.

Tunawa tayi da maganar da Khalil ya gaya mata dazu da safen take zuciyarta ta dauki zafi hawaye ya kawo idonta, har ace an kai matsayin da Khalil zece koda ita ko babu ze iya rayuwa saboda ya samu wata? Wannan dalilin ne kadai yasa ta yarda da tayin safina kuma a shirye take data sabauta koma wacece take shirin kwace mata Miji, Khalil dinta dai bata da buqatar yin wani aiki akansa dan natane, ta sani itama me shirin shigar mata Hancin da Asiri ta neme shi dan haka zata kwato abinta kota halin qaqa kuma tana buqatar tayi hakan da sauri. Kallon Safinah dake faman danna waya tayi tace

"Nifa Safina zuciyata bata aminta da wannan abin ba kuma na tabbata koda anyi aikin baze yuwu ba tunda daman shi Asiri ai seka yarda dashi yake ci kuma ni kin san uzurina na sauri ne, kawai kinga ma fasa mu tafi zanje nayi duk me yuwuwa na samarwa kaina mafita iya wannan jiran banzan da mukeyi ya tabbatar mun bazan samu abinda nake buqata ba" Umaimah ta fada tana kallon Safina, murmushi Safina tayi tareda dafata tace

"Dadina dake Umaimah garaje wai me kike ci na baka na zuba ne? Wai bakiji sunan Malam bane? In kiyarsa fa sha yanzu magani yanzu ke dakanki ya kamata ki bada shaidar hakan tunda yayi mun kuma kin gani, duka dan jiran da zamuyi na minti nawa ne ko kuwa ke kinfi gane kje kiyi hauka ayita yawo dake a duniya ana surutu ki qarawa kanki baqin jini a gurin wanda kikeyi saboda shi din?
Ke yanzu baki ma tunanin abubuwan da kikayi a baya ne suka tunzurashi ga yin auran yanzu toh wallahi kika kuskura kika sake gwada wani shirmen na tabbatar ya sakeki ba wani abin wahala ze zamar masa ba tunda da bakinsa ya gaya miki yanzu bakya gabansa dake ko babu ke babu abinda ze fasayi to gara ki taimaki kanki kibi komai a sannu, ta qarqashin qasa ake yaqi yanzu ki koma gefe kisha kallo kina zaune zakiji zuwan da dawowar kuma babu wanda ze zargeki balle a sakaki a bakin duniya".

Janye hannunta da Safinan ta riqe tayi zatayi magana wani saurayi ya shigo dakin da suke zaune yace
"Hajiya Malam yace ku shiga bangaren Amarya ku jirashi daya sallami wadda take ciki ze shigo yanzu" yana gama fadar haka ya juya se Safina ta miqe ganin haka itama ta miqe tabi bayanta dukda zuciyarta cike take da wasi wasi. Cikin gidan Malam din suka shiga, part uku ne qerarru a ciki, kallo Umaimah tabi gidan dashi, Safina taja ta tana cewa
"Kinga badda kama ba?"
Ita dai tabita da "Uhm" a ranta tana sake qaryata aikin Malamin dan quru quru yanzu ta samu hujjar cewar dan damfarane. Yana can yana tatike masu dakon Asara ya danqara gida na gani na fada da kudin su yana shata musu qarairayi.

A falon Amaryar Malam din suka zauna, Umaimah dai se bin gurin take da kallo yanda ya gaji da haduwa abubuwan more rayuwa kuwa babu wanda babu a ciki. Seda me aikinta ta kawo musu ruwa da Lemo kafin ta fito, fara kyakykyawar yarinya da bazata haura shekara Ashirin ba da fara'arta suka gaisa da Safina wadda alamu ya nuna akwai sabo sosai a tsakaninsu kafin ta gaida Umaimah dake binta da kallo. Tashi tayi tace tana zuwa ta shige kitchen, Safina tayi qasa da murya tace
"Kin ganta yar qawar Hajiyarmu ce in gaya miki daga zuwa karban taimako wai Aljanu na damunta se ji mukayi wai Malam take so shi zata aura harfa an kawo mata kudin aure wani yaro dan masu kudi a gurinsa fa aka ringa aikin har suka shawo kan yaron ya fito za'ayi aure se gashi yarinyar nan ta dage se shi seda akayi auran nan yanzu watanta biyar kenan aiko uwar saboda Haushi tace ko cokali bazata siya mata ba yace babu komai saboda auran nata fa ya rushe gidan gaba daya ya tada wannan ginin kiga Aljannar duniyar daya zuba mata"

"Aikuwa taga taimako kinga an yi daidai kudin ku da kuke kawo masa dashi ya hada yayi mata kayan dakin da duk baku saka irinsu ba ma ai" Umaimah ta fada cikin gatsali. Sallamar Malam ta hana Safina bata amsa, Matashin Magidanci da baze wuce shekaru Arba'in da motsi ba ya shigo yasha Babbar Riga ta Shadda Getzner se maiqo take ga uban rawani ya kafa da zabgegen carbinsa a hannu. Ya washe baki yana yi musu sannu da zuwa Safina ke amsa masa Umaimah dai tunda ta gaidashi sau daya ta sake fuska dan ganinsa ya sake saka ta qin yarda da lamarin Na Safina. Wannan ne Malamin da take zuzutawa ta tabbata dai dan 419 ne shima yake kwasar rabonsa kawai.

"Hajiya Safina idonki kenan, ai nace tunda kin samu kan Yallabai an dena jinki" Malamin ya fada se Safina tayi dariya tace
"Ba haka bane Malam, kwana biyun ne ban fiya zama ba wlh amma ina nan zanyi zuwa na musamman, yanzu ma qawata na rako, abu ne ya taso mata Urgent shine nace bari na rakota inda za'a share mata hawaye".

"To to menene matsalar? Ko da yake ina zuwa" Malam ya fada kafin ya miqe ya shiga wani daki dake cikin falon. Amarya ta dawo me aiki na biye da ita da Qaton Try da ta doro kulolin abinci ta ajiye musu Safina tayi mata sannu ita dai Umaimah binta kawai take da kallo harta wuce ta koma dakinta. Minti kusan biyar Malam ya dawo da wata qaramar Jaka ya shimfida buzu a qasa ya zauna ya bude jakar ya ciro qaramin carbi da wasu kwalaben turare. Seda ya gama shafe carbin da turaren yana mammotsa baki kafinya kalli Umaimah yace
"Bismillah"
Kallon Safina tayi da rashin fahimta se tace mata
"Ki matsa kusa yake nufi".
Muskutawa tayi gefe tana sake kallon bakin Malamin dake ta motsi seya miqo mata carbin hannunsa yace ta zabi guda uku ta zaba seda suka maimaita sau uku kafin yaci gaba da jan carbin yana muimui da baki. Shiru gurin ya dauka Malam nata juya carbi yana girgiza kai daga qarshe ya ajiye yana kallon Umaimah da Safina da suka zura masa iso suna kallonsa yace

"Maganar gaskiya akwai Matsala babba".
A tare suka gwale ido suna kallonsa, Safina data dafe qirji tace
"Matsala wace iri malam?" Seya karkace ya gyara zama yace
"Mijinki ya fada soyayya da wata yarinya kuma munga akwai qauna a zuciyarsa hakan yana nufin aure kenan"

"Toh Malam ai munsan da wannan dalilin daya kawo mu kenan muke so a dakatar da auran" Safina ta fada seya sake jan carbi ya hau irga kusan minti biyar kafin ya sake kallon Umaimah yace
"Maganar Gaskiya Hajiya naga aure sedai lokacin yinsa ne ban sani ba, sannan akwai mutuwa kuma akwai mutuwar aure duka gaba daya amma zamu iya shawo kan matsalar gaba daya in Allah yaso"

"Kaga Malam ka tafi kai tsaye ka gaya mana abinda ka gani ba wani magana a duqunqune ba, nifa daman shi yasa na gaya miki bazanzo ba, akan me mutum be gama da tashin hankalin da yake ciki ba za'a qara kawo masa wani? Mutuwa daman dole ka ganta dan koma wacece take shirin shiga sabgar Mijina Ajalinta ta siya mutuwar aure kuma ka ganta a gidanka. Ni kinga tafiyata da nasan batamun lokaci zaki saka ayi wlh da ban biyo ki ba" Umaimah ta fada a fusace tana miqewa tsaye, riqeta Safina da hankalinta yafi na Umaiman tashi tayi tana kallonta tace

"Umaimah ki nutsu ki fahimci abinda yake fada, kin rigada kinji matsala s ki jira kiji yanda za'a maganceta"
"Karki rainamun hankali mana Safina, Mutuwar ze hana faruwarta ko auran wanne yake da ikon dakatarwa a ciki? Kinga karki qara batamun rai ki barni na tafi naje nayi wadda zata fishsheni kedai da kikaga zaki iya seki zauna yayi ta karanta miki qanzon kurege" ta fada tana fincikewa se Safina ta sake riqeta, miqewa Malam yayi yana kallonsu yace
"Bari naje, idan ta shirya kya yimun magana na bar mutane suna jirana a waje"

"Aa kayi haquri dan Allah Malam, wallahi damuwar da take ciki ce tayi mata yawa har ta fara taba tunaninta amma tana da buqatar taimakonka matuqa wallahi. Ka taimaka mana duk abinda ya dace ayi dan hana faruwar auran nan kayi shi kawai Malam" Safina ta fada se Malam yace

"Toh Hajiya naga wadda take da damuwar nan tace bata da buqatar aiki ke menene naki a ciki ne ki barta kawai taje, nidai na gaya miki akwai aure, akwai mutuwar aure sanann akwai mutuwa duk kuma inda zakije kije nasan bazakiji sabanin wannan binciken ba".

Yanda kasan wanda aka zarewa Laka haka Umaimah ta bishi da kallo ta kasa motsawa ta tafi daga gurin kamar yanda tayi niyya.
"zauna" Safina ta fada tana kama hannunta seta zauna kuwa babu musu zuciyarta tana wani irin bugu na tsoro data rasa tsoron menene.
Chapter 172 · 0% Book details