Sashe 60
Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hira ce ta sarqe a tsakanin su tun Umaiman na shareta har ta fara sakewa dan Zainab din nada faranfaran da ban dariya a dan lokaci bawa Umaimah labarinta ta dana Mijinta, mijinta hamsahqin me kudi ne kuma ba ita kadai bace matarsa yana da wata matar a Kaduna, ta ringa abin nema ya samu Umaimah taji aibun kishiya nan suka hadu suka ringa kwashewa Kishiyar Zainab da bata ji ba bata gani ba Albarka Umaimah na jaddada ai ita bazata taba iya zama da kishiya ba a rayuwarta idan taga masu itama mamaki suke bata.
Khalil na kallon news dinsa sedai ya waiwaya ya kalleta kawai yayi kwafa se gurin goma ya tashi itama ta yiwa Zainab sallama ta kashe Data ta bishi cikin dakin. Ya shareta haka tayita rara gefe dakyar ya kula ta bayan daya sake jaddada mata kan ta fita daga group din nan idan tana son zaman lafiya dashi tace toh zata fita badan zata fitan ba sedan a zauna lafiya. A Achieve chats ta saka groups din tayi saiti yanda ko saqo ya shigo baze fito a jerin chats dintaba se ta shiga can ta duba, tana qoqri idan yana gida ma ba kasafai ta fiya daukar wayar ba daya saka qafa kuwa ya fita wuni take a kwance tana sana'ar Chatting a group ko da sabuwar qawarta da yanzu babu abinda Umaimah bata sani akanta ba, kusan ko yaushe suna chatting dan har mamaki Umaimah takeyi yanda Maman Nihal din is always online kamar bata da aikin yi.
Koda yake Mijinta tace ba mazauni bane kuma wannan uban gida nata dole tana da masu aiki kala kala tasan shiyasa zata samun lokacin wuni a online.
Duk wani abu daya shafeta ko takeyi seta gayawa Umaiman har Mamakin rashin sirri irin na Maman Nihal din takeyi dan ko Maggi Mijinta ya siyo seta gaya mata an siyo mata kaza anyi mata kaza wayarta kuqa harta kusancika da hotunan tarkacen Maman Nihal, kayan sawa ne, wani abin amfani komai ta siya swta nuna mata ita a ganin ta sun zama daya ta dauki Umaiman kamar yar uwarta.
Sati daya tsakani Nuratu ta haihu akayi mata Cs ta samu Ya Mace dalilin haka ba'ayi taron suna ba se ranar da sukayi sati biyu, guri aka kama aka sha budirin suna Umaimah nata iyashegen wai dangin Dr Sagir anya ba Yarabawa bane sun fiya son bidi'a in ba haka ba suna ma ace se an kama guri anyi kamar wani biki haka aka watse taro yarinya taci sunan Maman Dr Sagir Ummulkhairi suke kiranta da Khairi.
Da daddare tayi posting hotunan da sukayi a gurin suna a status dukda ba wani kyau tayi ba dan ta rigada ta zama se an hankali. Zainab ce ta fara dubawa tana gani kuwa se gashi ta kirata a waya Umaima na zaune kusa da Khalil dake aiki a Laptop wayar tayi qara ya kalleta yace
"Waye kuma a daren nan" ta daga tana cewa
"Maman Nihal ce", shi kamya rasa wacece haka ta samo da yanzu motsi kadan zatace maman Nihal, abu kaza irin Maman Nihal Maman Nihal tayi kaza. Last week daya nuna mata hotom wata mota da yake so ya sake tana gani tace irin ta Maman Nihal ta dakko wayarta ta nuna masa shidai yana tunanin Umaimah tana da irin ciwon nan da mutumyake zama too attached to somethings, wani ko gurin zama ne baya iya chanzawa saboda baze manta ba lokacin suna secondary da akwai wani senior dinsu da yake da ciwon seda ya maimaita SS1 sau uku duk sanda aka K promotional exam seya fadi ayi masa repeating se daga baya aka gane ba qoqarine bashi dashi ba yanasane yake faduwa saboda wai baya so a chanza masa aji to itama dai yaga alamar tana da wannan ciwon akan qawaye kwafa yayi ganinta tashi daga kusa dashi ya maida kai yaci gaba da aikin da yakeyi.
Umaimah kuwa can kan Dining ta koma bayan sun gaisa Zainab take cewa
"Ashe suna kuka sha haka babu gayyata gaskiya Umaimah baki da kirki baki daukeni yanda na dauke ki ba. Nidai ina sonqawance dake tsakani da Allah kuma inason zumunchin mu ya dore amma ke naga ba haka bane a gurinki har na gaji da tambayar yaushe zakizo gidana tunda ke bakya so nazo, haka nayi ta kiran wayar ki ranar nan ina unguwarku kika qi dagawa dan kar nazo na sha Ac a Mansion dinki"
Dariya Umaimah tayi tace
"Ba haka bane Maman Nihal kin san nayi nauyi bana fita yanzu se wadda ta zama dole ko zuwa Asibiti amma in sha Allahu na haihu ai inaga se kin gaji kin ce na sena zuwa, gida na kuma fa sau daya ne kika ce zaki zo ranar bana nan naje gidan Hajiya wayar na cikin jaka amma kiyi haquri qofa a bude take duk sanda kika shirya kizo muna maraba da ke"
"Haba na sake zuwa kiqi daga waya in kin ganni a gidan ki to se randa kika zo nawa gidan tukunna kika tabbatar mutum ce ni ba aljana ba sannan zan saka rana nazo miki dan nasan qila har yanzu baki gama yarda dani bane" Zainab sin ta sakw fada se Umaimah tayi dariya tace
"In sha Allahu zan wuce gorin nan ki bani Address gobe zanje Antinatal zan fita da wuri idanna gama zan shigo"
"Wane Asibiti kike zuwa?" Zainab ta tambayeta se Umaimah tace
"Nan UMC nake zuwa"
"Amma kin cika kwankwararriyar mara kirki kice ma kusan duk sati kike zuwa layin mu amma baki taba leqo ni ba anya Umaimah" Zainab din ta sake fada kafin taci gaba da cewa
"Kamar qarfe nawa zaki zo toh dan in sani kar muyi sabani", se Umaimah tace
"Idan zaki fita mu bari kawai se wani lokacin dan se bayan la'asar likitan yake zama, zan yi qoqarine daman na fito da wuri yanda zan zama ta farko dana gama se na biyo"
"Aa ba nisa zanyi ba ai kinsan munata shirye shiryen bikin Hamida qanwata saura sati biyu to goben zamuje ganin gida amma inaga da safe ne ma, koma da yamman ne zan iya fasa zuwa tunda zakizo" Zainab ta bata amsa daga nan suka yi sallama bayan sun rabu akan Umaiman zata kira idan tazo Asibitin taji idan tana nan ta qarasa.
Bayan ta gama wayar ta koma kusada Khalil ta zauna tareda dora qafafunta da suka tasa akan cinyarta, ture qafar yayi ta bata fuska tace
"Haba mana Honey ka matsamun ciwo sukeyi"
"Ba kinje kinyi rawa ba ai dole qafa tayi ciwo kuma da kikaje kika zauna acan duk baki san zata qara ciwon ba kina ta shegen surutu se yanzu" Ya fada yana harararta seta yi qaramar dariya tace
"Maman Nihal ce fa qawata inaso ma dan Allah gobe daga Asibiti na leqa gidanta kaga kullum se tayi mita"
"Wai a ina kuka hadu ne haka?" Ya tambayeta yana kallonta seda tayi masa fari da ido kafin tace
"A WhatsApp group din da baka so gashi nan muna ta zumunchi da ita"
"Kinga ki raba kanki da kwashe kwashen matan online din nan ba dukkansu ne na kirki ba" ya fada yana nunata seta bata fuska dan tasan yanzu ze fara fadan nasa na ba gaira babu dalili akan WhatsApp tace
"Toh kaima fa naga ka hadu da mutane da yawa a online din nan baga Kabir Bala ba ina kace a Facebook kuka hadu kuma yanzu kuna ta harkokin qaruwa da juna"
"Ai ban fada miki a group din shashanci muka hadu ba daman a group din qaruwar muka hadu harkokin mu iri dayane shiyasa muka qulla alaqar kasuwancin mukeyi" ya fada jin tana neman ta raina masa wayo, seta juya kai tana cewa
"Mune bamu da group na qaruwa kenan se na shashanci kawai mutum shi bazeyi qawance na a rayuwarsa da Mama ce take takuramun yanzu kuma ka karba shi kenan ni banida yanci a rayuwata se abinda kuka tsaramun"
"Saboda baki san irin mutanen daya kamata kiyi mu'amala dasu ba dan haka dole se mun saka miki ido, kuma ni wannan matar batayi mun ba bana son mu'amalarku da ita dan bata da kamun kai bata da sirri ki fita a sabgarta" Khalil din ya fada ba tareda ya kalleta ba ta kuwa qara zumbura bakin rashin kunyarta tace
"Ai duk qawayena basuyi muku ba nima din ai bayi muku nayi ba daga kai har Maman dan dai Allah yayi babu yanda zakuyi dani ne kawai"
Banza ya mata dan yaga alamar so take ta fara tijarar tata. Washe gari kuwa kafin ya fita seda ya jaddada mata akan daga Asibiti be yarda taje ko ina ba ta wuto gida, bata ji ba Qarfe uku ta shirya tsaf cikin wata doguwar riga yar Dubai me kyan gaske, wani Abokin Khalil ne ya kawo mata ita da yaje musu kwanaki bata taba sakawa ba se ranar.
Harda simple makeup tayi wai kar Zainab ta rainata ta fesa turarukanta Designer ta kawo zobunanta guda biyu na zinare ta saka a hannu ga Agogonta Versace ta daura da cogen takalmi ta ciro Vinci data tuna Asibiti zata tasan yanzu sa rufeta da bala'i seta mayar ta dauko flat baqi na C&K da yar qaramar jakar sa mw baqi da ja me kyau ta saka.
Tuni ta kira me Adaidaitan da yake kaita unguwa duk sanda zata fita ita kadai ba tareda Khalil ba yana qofar gida yana jiranta dan haka ta kulle gidan ta hau suka tafi. Ita aka farayiwa Awon tana gamawa ta kira Maman Nihal ta shaida mata tace ta tsaya a qofar Asibitin yanzu zata turo a taho da ita, ta nemi guri ta tsaya dan ta sallami me Adaidaitan daya kaita tace idan ta gama zata kira shi haka kuwa akayi mintina kadan sega wani saurayi a wata hadaddiyar mota sunzo shida Nihal babbar yarta data gama haddace kamanninta saboda yawan hotunanta da akw tura mata.