← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 267

Sashe 112

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dukda bansan me yarki ta aikata ba da har kike wadannan kalaman amma nasan be kama qafar abinda Dana ya aikata ba. Yanzu haka an kamashi ya haura gida ya kashe Mata da Miji da Yayansu guda biyu kuma ya amsa laifinsa akwai abinda yakai wannan tashin hankali? Kenan da kece Uwarsa take yanke zaki tsine masa yabi duniya ko? To bari kiji sanda labarin ya riski Uwarsa Tasbihi tayiwa Ubangiji ta gode masa ta shiya bata Dan ya kuma tsara cewar qaddarar sa ce a haka tun kafin ayi mu Ubangiji ya shirya yanda kowanne bawa ze gudanar da rayuwarsa ta kuma roqi ubangiji yasa hakan ya zamo amsa kaffara. Tana can kwance, kowa yasan gigitar abinda ya aikata ce ta kwantar da ita amma bakinta be mutu daga ambaton Allah da nema masa sauqi a gurinsa ba dan haka na horeki da kiyi koyi da Matata, ki yarda da qaddara a duk yanda ta riske ki daman su Yaya da Dukiya Jarabawa ce".

Yanda kasan anyi ruwa an dauke haka gurin yayi tsit babu wanda ya iya motsi me qarfi gaba daya suka raka Dattijon da ido sanda wani da suke zaton Lawyer ne yayi kiransa. Aminu ne yayi qarfin Halin bude baki dakyar yace
"Kiyi haquri Mama na kira Abdulbasit yana hanya yanzu dan sunce da Lawyer kadai zasu bari tayi magana sun hanani ganinta, yanzu ku tafi gida mu zamu tsaya muga yanda abun ze kasance in Allah ya yarda ma baze dauki lokaci ba za'a sasanta komai su dawo gida shi yasa ma ban sanarma Abba bana so hankalinsa ya tashi yana kan hanya".

Haka suka taru suka lallabasu dakyar Ma'aruf ya kwashe su a motarsa harda Mahaifiyar Rufaida suka tafi Ya rage Aminun da Khalil se Barr Abdulbasit wanda Dan Yayan Maman ne da ya qaraso yanzu.
Se a sannan Khalil ya iya bude baki yace
"Ga wayar tata a hannuna, nasanita wadda ta tura mata da hotunan dukda na duba babu wani abu da za'a samu a ciki dan ta rigada ta goge duk wani Chat da sukayi exchanging kuma tayi blocking layin kaga babu wata shaida da zata tabbatar da ita dince saboda bada layin da aka santa tayi amfani ba. Yanzu idan da hali ina so na gana da wadanda suka shigar da qarar, ina fatan idan nayi musu bayani zasu gamsu mu samu fahimtar juna ta yanda za'a warware komai cikin sauqi".

Barr Abdulbasit ne ya karbi wayar tata ya duba kamar yanda Khalil din ya fada an yi deleting message din da aka turo seya kalli Khalil yana cewa
"wannan ba wata matsala bace tunda ga amsoshin da ta bata nan suna nan kaga ko daga mam za'a samu Idea na abinda suka tattauna. Yanzu bari na fara shiga cikin na gani idan da hali se kuyi magana dasu kamar yanda ka nema tunda kaima abin ya shafeka kai tsaye" ya wuce ciki ya barsu.

A ciki kuwa bayan ya gabatar musu da kansa yayi cike ciken takaddu kafin aka sake fito masa da Umaimah, kamar yanda dai suka tambayeta shima tishi yayi akai ya dauki bayanan da yake ganin zasuyi masa amfani kafin ya koma inda Musa Kallah da Isma'il tareda sauran wakilan qungiya suke zaune. Bayan sun gaisa ya gabatar musu da kansa da kuma buqatar Khalil nason yin magana dasu kai tsaye Ismai'il ya ce Aa, seda Musa Kallah ya saka baki yace ya shigo sannan ya haqura badan yaso ba.

Tiryan tiryan Khalil ya labarta musu yanda sukayi da Khausar a wancan karon da kuma abinda ya samu a wayar Umaiman, Musa Kallah ya karbi wayar yana dubawa tareda nazarin maganganun Khalil din ya gama ya miqawa Detective din dake akan case din shima ya karba ya duba. Number suka dauka suka saka ta a computer su ta bincike, wani rashin Azanci da Khausar din tayi shine na amfani da Layi Wanda tayi register shi da sunanta dan ana shigar da number nan take duk wasu bayanai nata dake kan layin suka bayyana.

Khalil ya sauke ajiyar zuciya, daga Umaimah har Hadiza a yanzu suna buqatar daukinsa kuma kamo Khausar a hannu ne kadai ze rangwantawa Umaimah laifinta ya kuma wanke Hadiza daga Qazafin da sukayi mata. An tura da Jami'ai dasu nemo Khausar din duk inda take kasancewar yamma tayi Barr Abdulbasit ya nemi da abasu Belin Umaimah da Rufaidan zuwa gobe se su dawo a ci gaba da bincike amma qememe suka hana, a cewarsu har yanzu itace prime suspect, dan haka babu halin bada belinta har se zuwa yanda hali yayi domin koda an kawo Khausar da sun gama tattara bayanai zasu miqasu kotune gaba daya su girbi abinda suka shuka matuqar ba wadanda suka shigar da qara bane suka janye wanda kuma ba abune me yuwu ba.

Wannan ya tayar musu da hankali dan dukda abinda ta aikata dole su tausaya mata kodan halin da take ciki ga Tsohon ciki, ko iya sauron da ze cijeta tsakanin dare zuwa safiya aka barya dashi ya isheta jin jiki amma ya suka iya haka suka tafi bayan an barsu sun gansu dakyar Khalil ya fita ya siyo musu abinci da abin sha harda guzurin barguna da maganin sauro suka tafi da niyyar gobe da safe zasu dawo a dora daga inda aka tsaya.

*KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ƳAR'UWA, WATA-ƘILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.*
Ƴar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassaƙe da garin magunguna na gargajiya, waɗanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu.
*Ina matan da basu taɓa haihuwa ba?* Ko kuma sun taɓa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa ɓari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? Ƴar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata ɗaya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari.

*Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haɗa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari.

*Ƴar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haɗa miki magunguna kala biyar, waɗanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daɗewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haɗi *Bye bye infection.*

*Mijinki ne bai da kuzari a shimfiɗa?* Ƴar'uwa ko ki faɗa ko kar ki faɗa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan ɗaya wanda zai dinga shan ƙaramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ƙara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda.

*Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huɗu da za ku fatattaki daji daga jikinku.

*Ingantaccen haɗin sabaya😍* Haɗin sabayarmu duniya ne ƴar'uwa. Baza muyi miki ƙaryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga sheƙi, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haɗin sabayarmu.

*Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk ɗauri ɗaya 500.

*Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuɗin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuɓeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo😍😍😍*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

Page 46

A gurin Ismai'il da Musa Kallah sukayi sallama akan se goben zasu dawo, kaitsaye gidan Mama ya wuce dan be sanar da ita abinda yake faruwa ba ya bari se komai ya kammala tukunna. A can ya tarar da an sallamo Hadizan, tundaga soro yake jiyo irin Tijarar da Mama take zubawa Malama Lawisa da Hadizan akan su fitar mata daga gida ita kuma Malama Lawisa ta kafe akan babu inda Hadiza zataje dan bata da inda yafi nan din, idan ma da Wanda ze fita toh Mamance dan ita Hadizan Gadon Ubanta ne gidan.

Mama Innai da Hajiya Barira basa nan ake wannan dambaruwar sun tafi Asibitin dubota sukayi sabani, yana shiga soron yaci karo da Hadiza dake durqushe tana rusa kuka kamar ranta ze fita, gabanta ya durqusa da niyyar kamata tayi saurin sunkuyarda kanta tsakanin cinyoyinta jikinta har rawa yake saboda Azabar tsoro bata manta dukan da yayi mata ba dan ga shaidarsa nan hannunta daya tsage a nade da bandeji ba'a kwance ba.
"Dan girman Allah karka dakeni wallahi Umma Lawisa ce seda nace mata bazan dawo ba kun koreni tace se nadawo" Hadizan ta fada tana kuka kamar zata shide tsabar tausayinta besan sanda Hawaye suka fara zubo masa ba shima ya saka hannu biyu ya dagota gaba daya ya runguneta yana cewa
"Ki yafe mun yar uwata nayi nadama ki yafe mun Hadiza".
Chapter 112 · 0% Book details