← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 171 OF 267

Sashe 171

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To kuwa seki shirya saboda nan bada dadewa ba wadda tafiki cancanta data zamo matata zata karbe gurbinta, idan kinga dama ki nutsu ku zauna lafiya idan ba baki ga dama ba kiyi duk abinda zuciyarki take ayyana miki da kiyin aurene babu fashi se nayi idan yaso ki kasheni ko ki kasheta kamar yanda kike fada se mu gani ke idan zaki zauna kiyi gadin duniya ne" daga nan yaja bakinsa yayi shiru duk irin ihu da kururuwar da takeyi tana zaginsa da iyayensa harda Mahaifinsa dake kwance a kabari bata manta dashi ba seda ta zaga yayi mata shiru be tanka mata ba, tafasa kawai zuciyarsa takeyi ya tabbata idan ya biyewa abinda zuciyarsa takr saqa masa to fa sedai ya maida gawarta gida dan se yayi mata dukan mutuwa a motar kafin su isa amma haka ya daure har suka je gida.

A bakin get ya tsaya ya kalleta da idanunsa da sukayi jajir ita kanta duk rashin mutunchin da taken zazzaga masa suna hada ido seda ta dauke wuta ta matsa can jikin qofar motar, cikin wani irin Amo yace ta sauka, bude bako tayi da niyyar gaya masa magana ya daka mata tsawar da har seda abinda yake cikinta ya wuntsila, babu shiri ta balle murfin ta fice tana haki, a bakin get din ta tsaya tabi motarsa daya fizga da gudu ya bar layin da kallo nan ta shiga tunanin me zatayi masa. Ta rantse da abinda ze kasheta Khalil yayi kadan dashi da duk ma wanda suke goya masa baya akan yayi auran za kuma ta tabbatar musu da ita Umaimah warkice daidai da qugun kowanne dan iska.

Haka taja qafa ta shiga compound din, idonta ya sauka akan sabuwar motarsa Marsandi daya siya ko cikakken wata biyu batayi ba gaba daya zata iya qirga sau nawa ya hauta dan ita kanta sau biyu ta shigeta daga randa aka kawota se da zasu bikin wata qanwar qawarsu ita da Safina ta uzzura mata seta ari motar ta dauka a sace ba tareda ya saniba. A qalla kudin motar ya haura naira Miliyan Goma sha biyar dan sanda ya siyeta ba qaramin fada Hajiya tayi masa ba a cewarta almubazzaranci ne. Ba tareda tunanin komai ba ta matsa gefe inda aka saka musu rumfar shan iska da kujeru, duwatsu ne a gurin ta sunkuya ta tsinci manya da take ganin zasuyi mata aikin da take so tayi ta kwashe su da dama kafin ta durfafi motar. Seda ta cire rigar da aka rufeta da ita kafin taja da baya ta tsaya. Tunani tayi duwatsun bazasu mata aikin da take so ba ta zubar dasu a gurin, cikin gidan ta wuce kai tsaye ta shiga kitchen ta dakko qatuwar tabaryata dawo gurin motar babu tunanin komai ta fara takan glass din baya da yafi kowanne tsada, seda tayiwa gilasan motar rugurugu ta hada harda jikin qarfen motar ta lotsa inda zata iya kafin ta haqura ta yarda tabaryar a gurin tana haki kamar kamar wadda aka saka dole.

Ciki ta koma ta dakko muqullin tata motar ta fice daga gidan, kai tsaye gidan safina ta nufa tana da buqatar ta ba zata iya ita kadai ba dan ta tabbatar babu qarya a kalaman Khalil ita kuma tayi alqawarin bazasu tabbata ba.

CIKIN GIDA
Umaimah na barin Gidan Anty Amina da Jamila suka fito da shirin tafiya. A gigice Anty Aminan ta shiga kwalawa Sammani me gadi kira ya shigo compound din hankali tashe sedai abinda ya gani yasa ya gane dalilin kiran nan da nan ya tsure har ya fisu shiga rudani, Jamila ce tayi qarfin halin tambayarsa wayayi wannan aika aikar Sammani ya watsa hannaye sama yana rantsuwa yace
"Na rantse da kwarankwatsa Hajiya bam sani ba, tunda Alhaji ze fita ya aikeni can bayan layi gidan da akayi rasuwa ya bamu Buhun shinkafa da kudi yace mu kai musu, ina dawowa kuma na zauna a bakin qofa ko ciki ban shigo ba se yanzu".

Hannu kawai ta daga masa alamar yaje, Anty Aminan ta janyo waya zata kira Khalil Jamila ta hanata tace su koma gurin Hajiya. A falo suka tarar da ita tana waya suka zauna kowacce ranta a dagule har Hajiyan ta gama wayar, tana shirin yin magana Jalilah ta fito daga kitchen da farantin Indomin da ta saka Habiba ta dafa mata, kallonsu tayi ganin yanda sukayi wani sanyi se kace wanda aka fadawa Rasuwa ta ajiye farantin tana cewa
"Aa, ku kuma fa ya haka kun fita da fara'a kun dawo kamar Wanda akayiwa mutuwa?"

Anty Amina ce ta kalli Hajiya tace
"Hajiya, yanzu muna fita muka tarar da motar anyi anyi kwash kwatsa da gilasanta, na tambayi sammani yace besan wanene yayi ba"
"Wace motar?" Jalilah ta tambaya tana dafe qirji Jamila ta bata amsa da cewa
"Mercedes dinsa"
"Babu shakka labari yakai kunnen Umaimah, to wallahi Allah duk wata asara da tayi masa tamkar ta qara zugi ne da qara matso da lokacin auran nan, tunda ta riga taji kuma babu abinda za'a jira Hajiya ki kira su Baba Abu suje su nemo auran nan kuma ko yanzu ta kama a daurashi kawai idan yaso ta hadiye zuciya ta mutu qarewar fasa masa mota, kuma duk abinda ta lalata seta biya bazamu sake daukar Asara bisa ganganci ba" Jalilah ta fada tana huci yanda kasan motarta akace an lalata.
*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

Page 63

UMAIMAH
Bayan fitarta gida kai tsaye gidan Safina ta wuce dan tana da buqatar abokin shawara akan ta inda zata bullowa lamarin. tana tafe a hanya kuka takeyi wiwi kamar wadda aka aikowa uwarta ta mutu, kalaman Khalil na mata yawo akai tana jinsu kamar wasu Allurai ne ake caka mata su a kwakwalwa a haka ta qarasa gidan tana shiga ta zube a falon Safina tana ci gaba da Kuka, Safina dake kwance kan kujera tana kallo ta miqe da sauri ta nufeta hankali tashe tana tambayarta lafiya amma Umaiman ta kasa ce mata komai se ihu take kamar wata zautacciya. Sda tayi me isarta ta samu sauqin abinda takeji kafin ta bude baki dakyar tace
"Safina na shiga uku na lalace dagaske Khalil aure zeyi har yana gaya mun rayuwata bata da muhimmanci a gurinsa yanzu dani ko babu baze chanza komai ba, ki taimakeni Safina zuciyata zata fashe" ta qarasa tana rushewa da wani sabon kukan.

Tsaki Safinan taja tareda komawa inda ta tashi tana kallon Umaimah dake kuka tamkar Mama ta mutu tace
"Amma wallahi kedai anyi banza yanzu daman saboda Namiji da wata kishiya da bata rigada ta shigo bama kikazo zaki saka jinina ya hau na zata ma wata mutuwar akayi miki, to uban me kike so yanzu ni nayi miki? Ina cewa kikayi zaki samarwa kanki mafita to yanzu basirar taki ce ta yanke da zaki sake dawomun kin wani kuka wiwi akan wani Khalil se kace da Gold akayi shi? Ki tafi inda za'a saka miki shi a kwalba se yanda kika yi dashi kin zauna kina batawa kanki lokaci kina zubar da mutunchinki a gari kowa yana miki kallon Mahaukaciya ina dalili, ni kinga bazan iya na ki dena zuwa kina raba baqin cikin ki dani bayan ga hanyar magancewa kin zauna taurin kai ke bazaki je ba".

"Ni na gaya miki ki bani wata shawarar banda ta zuwa gurin Malami dan ni bazan iya yawo kullum ina kaiwa qaton banza kudina yana cinyewa ba qila ma duk qarya ze ringa hadamun nazo nayi biyu babu" Umaiman ta fada tana goge fuskarta se Safina ta sake galla mata harara tace
"Ai idan baki kaiwa qaton banza yaci ba kyayita yawon Police station da kwanan Cell ko? Kinga nifa ban kiraki ba, shawara dai kike nema a gurina na baki kuma kince batayi miki ba dan haka kiyiwa Allah ki qyaleni nidai kiyi sabgarki ke kadai dan bana son abinda zesa kije kiyi wani cin kan sunana ya fito a ciki banji ba ban gani ba a zo a daureni. Duk ranar da kika shirya kika kuma yarda kizo na kaiki inda ko sunan Mace indai bake ba Khalil baze ambata a bakinsa ba. A kama miki shi a hannunki ba wani mugun abu zakiyi masa ba Kishiya ce bakya so shikenan a cire masa tunanin duk wata mace daga ransa se ke kadai ba shikenan ba meye wani abun zafi anan? Idan ma qyashin bada abin Sadakar kikeji muje ni zan biya miki kodan ki qylaleni na huta haka dan Allah".

Dukda bata so amma haka ta yarda da zuwa gurin Malam Sha yanzu magani yanzu saboda hujjojin da Safinan ta bata tana ganin zata iya amfani da hakan a matsayin matakin gaggawa na daqile abinda yake shirin faruwa kafin ta tsara gagarumin shirin a gaba, dan ita ba zata qarar da lokacinta da abinda ta tara a gurin Malamai ba. Babu bata lokaci Safinan ta shirya suka fita bayan ta kira Malamin nata ta sanar masa da zuwansu. Can wata unguwa sukaje a wajen gari.

Irin motocin da ta gani a qofar gidan Malamin ya bata Mamaki, haka a dakin da ake karbar lambar ganin Malam din Matane da Maza manya da kana ganinsu kasan sun kama qasa duk suke zazzaune suna jiran layi yazo kansu suga Malam din. Safina ce taje gurin wanda take bada lambar sukayi magana ta dawo inda take tace mata suje, wani daki qarami na daban suka shiga suka zauna ta kalli Safinan kafin tayi magana tace mata
"Kin san ni VIP ce tun kafin malam yayi suna a sanshi a duniya muke tare dashi. Asali malamin Kakarmune gashi anzo kaina nima ina cin gajiyarsa".
Chapter 171 · 0% Book details