← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 146 OF 267

Sashe 146

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A fusace Baba Abdullahi ya fice saga parlour ya tafi dakin Mama, a bakin qofa yaci karo da Umaimah da tunda taji qamshin turaren Khalil ta kasa tsaye ta kasa zaune. Tana can bacci bata san taron da Baba Audu ya hado ba shigowarsu Khalil ce ta farkar da ita saboda taji suna gaisawa da Anty ta kuwa fito da sauri amma sunrigada sun shige bangaren Abban se qamshin turarensa daya bari a iska tun sannan ta kasa zama Baba Abdullahi ya gama da ita wallahi. Muryarsa taji a tsakiyar kanta yana ta sako Hijabinta ta biyo shi. Ta zabura tana raba ido tace

"Uhm Ina zanje Baba?"
"Kizo muje wancan mara kunyar Mijin naki me yace wai se kizo ki fadi abinda ya hadaku, daman karki ji nauyin kowa ki fadi komai da kika sani idan shi be iya kama barawo ba ai shi ze kamashi. Ina Laure itama ta zauna cikin shiri dan itace shaidar gani da ido".

Jiki Babu Laka ta shige dakin Mama ta samo Hajibi, Maman dake zaune kan kujera ta kalleta tace
"Kinga da kika qi fada mun komai yanzu zakije gabansu ki fada in ma kece mara gaskiya kin jawowa kanki fadandaya fi wanda zanyi miki ai sannan a tafi dake a bakin duniya ana yamadidi kinga se kiji dadi" ta mayar dakai taci gaba da danna wayarta. Baba Abdullahi ya sake fafaro mata kira dan yana tsaye yana jiranta. Suna tafe yana qara qissima mata abinda zata fada harda qarin gishiri da Maggi har suka isa ta nemi gu daga bakin qofa kamar sabuwar munafuka ta shiga gaishe su suka amsa mata a kusan tare. Alhaji Garba da Alhaji Abubakar sukayi mata ya jiki ta amsa da sauqi kafin gurin yayi shiru.

"Mijinki ya nemi kizo aji ta bakinki akan abinda ya hadaku har kika dawo gida" Alhaji Badaru ya fada cikin kulawa yana kallonta. Umaimah ta dago kai ta kalli sashen da Khalil yake kafin ta hadiye miyau dakyar ta kalli Abba seta sunkuyar da kai tace
"Ni Dady komai ya wuce a gurina, daman dan sabani muka samu amma ya wuce"

"Ban gane komai ya wuce ba, zaki bude baki kiyi magana ne ko kuwa na kira Laure ita ta fada tunda naga alamar tsoronsu kikeji?" Baba Abdullahi ya fada se sannan Abba yayi magana yace
"Umaimah" ta dago ta kalle shi yaci gaba da cewa
"Me kika yiwa Mijinki da har ya saka shi ya dakeki ya shaqe miki wuya?"
"Ji wata irin tambaya dan Allah Yaya, kai anya ba Asirce mata iyaye kayi ba ace basa ganin laifinta se naka?" Baba Munzali ya fada nan cece kuce ya barke, wasu na fadin koma me ya mata tunda dai tace ya wuce to abarshi ya wuce din ta tattara ta koma dakinta ai damanko wacce Mace zaman haquri takeyi idan yaso shi kuma ya kiyaye kar haka ta sake faruwa Alhaji Badaru kuwa da yake nazarin Khalil da tunda ake maganar be dago ya kalli kowa ba ya kuma dubi Umaimah dake ta faman raba idanu alamun rashin gaskiya sun gama bayyanar mata ya dakatar da kowa, cikin muryar babu wasa dan daman shi bame wasan bane yace

"Kinsan Allah ko ki fada da kanki ta lallami ku kuma mu tashi mu tafi, duk ranar da kika bude baki kika fadi abinda ya faru se a sake zama danba zamu maidake cikin taraddadin irin zaman da kikeyi ba"

"Nidai wallahi Dady na yafe kuma yayi haquri kawai zan koma" ta fada tana fashewa da kuka se a sannan Khalil ya dago kai ya kalleta kafin ya kalli Alhaji Badarun shima yace
"Kuyi haquri Alhaji amma idan har Umaimah bata fadi abinda tayi mun da bakinta ba bazata koma gidana ba".

Shiru palour yayi kamar an dauke wuta Umaimah ko idanu ta zaro tana kallonsa bakinta na rawa amma ta kasa cewa komai, Baba Abdullahi ne ya ceceta ya furta abinda take so ta tambayi Khalil din yace
"Sakin ta zakayi?"
"Ko ban saketa ba bazan iya ci gaba da zama da ita ba har ze ranar data san daidai ta kuma koyi karban laifin da tayi ta bada haquri, daga nanzan duba idan da yuwar cigaba da zamana da ita dan wallahi ta kaini bango, Halin Umaimah ya isheni" Khalil ya sake fada cikin wani sauti dake nuna zallar takaicin dake cin zuciyarsa. Suka sakeyin shiru kafin cikin tsawa Alhaji Badaru yace mata
"Zakiyi magana ko mu tashi mu kama gabanmu dan duk muna da abinyi ba irinki ba"

Se sannan ta sake fashewa da Kuka, ta kalli Abbadaya tsura mata ido kafinta fara zayyano duk yanda akayi tundaga sanda ta fahinci Khalil yana kula Zahra, binsa gidansu da tayi, yanda ta lalata kayan dakinta har zuwa kwanciyarta a Asibiti da kuma sanadin Mari da shaqar da yayi mata.

Palour ya dauki shiru na kusan minti goma banda shashsheqar kukanta babu abinda kakeji tana cewa
"Dan Allah kayi haquri wallahi sharrin Shaidan ne, nikaina seda na aikata na fara nadama kuma da baka zo da fushi ba wallahi tun a sannan zan baka haquri
"Ki bashi haquri bayan kin cuce shi?" Alhaji Badaru ya fada cikin wani irin fushi da muryarsa ta kasa boyewa kafin yaci gaba da cewa yana kallon Baba Liman

"Zancen da nake maka zaman mu anan na wata kwangila da aka bayar a Office dinmu DG ya shiga ya fita ya bawa wasu qananan constructors se daga baya wai ya gano ashe yan Damfara ne ban masan Comapany Mijinta bane ashe yar iskar yarinyar nan ce take nema ta bata masa suna har yaushe zakiyi hankali Umaimah ki dena jefa mutane a masifa?

Yaushe akayi wancan Case din datayiwa yar mutane sharri aka gama saboda kin ga kinci bulus shiyasa kika sake kwanto masa wata kurar ko?
Daman tun wancan incidence din nake cike daku gaba daya yanda ace babu Wanda ya sanar dani se daga baya naji labari da kukayi yanda kuka ga dama. Dan ubanta da an dauki kwakwkwaran mataki akanta a sannan zata sake tunanin repeating any nonce like this ne?
Ita ga shafaffiya da mai, tayi tarnishing image din yarinya amma the only punishment she served was tayi video ta bada haquri shikenan taci banza saboda tsabar son kai da qin Allah irin naku. Idan itace aka yiwa qazafin iya abinda zamuyi kenan? Da yanzu wata magana ake ta daban because se nayi making sure that the culprit rot in jail, ai da aka tafi da ita ma be kamata ku bita ba se tayi sati ta fita hayyacinta sannan ta qara zaman prison kona shekara daya ne daga nan bazata sake dakkowa kowa magana ba amma yanzu gashi, ga abinda ta sakeyi saboda tasan qarqari kuyi mata fada shikenan ya wuce kai kuma lusari ka koma kaci gaba da zama da ita ba tareda ka nuna mata kuskurenta ba who does that?

Kinsan waye Dr Sabitu kuwa kin san irin tuggu da manaqisar daya iya hadawa?
Ubanwa ma ya saka ki shiga sabgar Business din Mijinki ina ruwanki dawa yake sabga dan ubanki idan ma uwar Zahra yace ze auro kina da matsala da hakan ko akan ki zata zauna eye?
To ai shikenan, yanzu kinyi yadda kike so ba daular da kike ciki kike baqin ciki wata tazo taci ba itama se ki shirya Allah ya kiyaye amma Jarabar da kika janyo masa sekin fi uban kowa dana sani wallahi dan ba'a shiga komar Dr Sabitu a fita lafiya musamman ta hado da wannan yar da yakeji kamar ransa".

Maganganun Alhaji Badaru ba qaramin tension suka qara a palour Khalil da yayi wuri wuri da ido yana kallon Alhaji Badarun, kalaman Uncle Anwar na sake dawo masa da yace
"Se kuyi taka tsantsan da duk wata contract da zaku dan Dr Sabitu mugune tsaf ze iya framing naku ya saka ku a matsa".

"Am nace kwangilar harta nawa ce ne haka?" Baba Abdullahi ya katse musu shirun a zafafe Alhaji Badaru ya sake cewa
"It worth billions of naira, inda yayi aikin nan Alkhairin daze samu Allah kadai ya sani amma yar baqin ciki ta hana"

"Biliyan kace, amma Umaimah anyi yar kutumar uba wallahi" Baba Abdullahi ya fada yana miqewa tsaye, kafin su ankara ya isa gabanta ya faska mata mari ya sake kifa mata wani Alhaji Garba dayafi kusa dasu ya riqe shi yana cewa
"Haba haba Alhaji ya haka kuma"
"Barni naci uban yarinyar nan ko bakaji abinda tayi bane?
Ai wallahi baka burgeni ba Khalil daka sani a Injin da kuke niqa sumunti ka jefa yar banza ka markadeta in yaso kazo kace mana ta bata kawai daga baya ka lallabo ka.gayamun abinda tayi maka mu taru mu rufe maganar wannan abin takaici har ina" Baba Abdullahi ya fada yana ciza yatsa, duk yanda suke cikin jimami seda maganarsa ta bawa kowa dariya suka murmusa banda Alhaji Badaru da Abba da yayi quri kawai yana kallon Umaimah. He can't believe it ace rashin tunanin Umaimah har ya kai haka. Maganar Alhaji Badaru ta katse shi da yake cewa

"Dallah rufe mana baki ba nan ka gama fuffuka da ihun zaka rama mata ba shine yanzu zaka zo da wata Dramar ka ta qarya. Ni dana san ma akan wannan yarinyar ne da babu abinda ze hanani komawa Abuja na zauna jin takaici, daman ki tashi yanzu ki shiga ki hada kayanki, tare zamu tafi gobe in sha Allahu zan wuce Abuja da ita tunda babu me iya wanke mata kwakwalwa a cikin ku to ni zanyi idan ta saitu ta dawo hayyacinta se a sake zaman".

Bala'i Alhaji Badaru ya ringayi kamar ze tashi gurin duk sukayi tsit aka rasa me dakatar dashi dan daman yan gidan su Abban ba laifi akwai bala'i dan zamanin suna yara idanka takali daya da fada tofa danginka kaf sun shiga uku haka zasu taso ku a gaba se randa Allah ya huci zuciyarsu. Dakyar Alhaji Badarun ya iya yin shiru kafin Baba Liman ya dora da Nasiha shi kuma yana nunawa Umaiman rashin dacewar abinda tayi.
Chapter 146 · 0% Book details