Sashe 232
Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Kin gani ko kar kisa ya dauka wani abun nayi miki" ya fada a hankali yana shafa bayanta seta bude baki cikin kuka tace
"To akan me zaka ce na gaji dasu ba Yaya na bane ko daman uwa tana gajiyawa da hidimar yayanta ne?"
"Kiyi haquri subutar baki nayi kuma na janye amma kema ki dena takuramun da maganar Umaimah bana so, akwai lokacin da ko ba'a kaisu ha da qafarsu zasuje" ya fada mata cikin rarrashi seta dago tana kallonsa tace
"A lokacin kuma zasu tsaneni dominzasuga nice silar da basu yi rayuwar quruciyarsu tareda mahaifiyarsu ba" se ya maida kanta qirjinsa yana cewa
"Ko kadan bazasu taba tsanarki ba ni nasan zasu soki saboda ke sukeyiwa kallon uwa ita sedai kawai ta amsa sunan Mahaifiyarsu amma ba Uwa ba. Tun kafin kizo Habiba suke yiwa kallon Uwa ita tasha wahalarsu ita tasan me sukeso da wanda basa so, ta rigada ta rasa wannan damar a gurinsu saboda ta sakarwa wasu al'amuransu da Uwa ce ya kamata ace ta dauka ke kuwa yanzu kin karba kinga kuwa har duniya ta nade suna miki kallon uwa a gare su, sannan ita take da abunda idan suka sani zasu tsaneta akansa kinsan da haka ko ita ce silar tashinsu ba tareda ita ba dan haka karki sake zargar kanki da laifinda ba ke kika aikata ba".
Seda ya lallasheta kafin suka ci gaba da tafiyar duk ransa babu dadi, baya qaunar abinda ze tuna masa da Umaimah saboda seya tuno da rayuwarsu gaba daya tun daga gabar daya ji dadinta har zuwa yanzu da yake dandana dacinta domin kuwa ta bar masa babban tabo a rayuwa, ya rasa lafiyarsa tsayin shekara uku a dalilinta sau da yawa yakanyi fatan dama ace ba Umaiman ce ta zama silar halin da yake ciki ba, dama ace accident yayi ya gamu da wannan matsalae da abin yazo masa da sauqi amma a duk sanda ya kalli kansa yaga abinda ta ja masa tsanarta da beyi niyya bace take qara shigarsa duk yanda yake qoqarin yayi mata uzuri abin ya faskara da wannan tunanin a ransa suka qarasa gidan.
Har powder seda yasaka Humairan ta sake gogawa kafin ya bari ta fita daga motar tana dariyar lamarin nasa yana nan zaune suka fito tun daga nesa ya hango Bibi da hawaye a fuskarta yayi saurin bude motar ya fita ya tarota tana zuwa kuwa ta fada jikinsa tareda fashewa da kukan shagwaba me daga hankali.
"Me ya sameki Mamana me akayi miki?" Ya fada a rikice yana duba fuskarta ita kuwa qara kukan take harda tirza qafa, Humaira dai ta bude mota ta shiga daman tuni Mu'ayyad ya shige da Iman da Aryaan suka bar uba da yarsa a waje suna nanaye seda ya rarrasheta badan ta fada masa abinda yake damunta ba kafin suka shiga motar, saboda tsabar tabara a kan cinyarsa ya dorata, Humaira ta kallesu ta sheqe da dariya tana cewa
"Yanzu saboda Allah ko kunya bakiji ba ga Iman ga Aryaan ko dane cinyar Dady to dake kike so yayi tuqin ko yaya?"
"Baki ta cuna irin na uwarta ta dauke kai gefe Khalil yayi qaramin murmushi, Bibi da Hajiya take kama amma halinta tas na uwarta ne babu abinda ta manto a ciki shiyasa be taba dora goshinsa a qasa ya tashi ba tareda ya roqa mata shiriya a gurin Allah ba da gudun zuciya irinta uwarta, Allah ya tsayar da ita ga gadon iyakar halayyarta ta kirkin ta zubar dana banzan amma tun yanzu fitsara a cikin Bibin se wanda ta manta.
"Koma cinyar Mamah kinji Bibina yanzu zan tsaya a hanya na siya miki Icecream ai kina so ko?" Ya fada cikin lallashi se Iman ta leqo tace
"Nima dady"
"Ki tambayi Yaya idan tace a siya miki toh" se kuwa ta noqe kafada kamar itace qaramar tana tura baki tace
"Baza'a siya mata ba ai jiya Mamah ta basu ni ta hanani kuma harda Burger zaka siyamun da Suya ko Dady?"
"Yes Dadys Girl, maza koma cinyar Mama kinga dare nayi mu tafi" ya sake fada yana dagata ze dorawa Humaira ita ta tare tana cewa
"Ba zaki hau mun cinya ba sedai Dadyn yayi tuqin dake"
"Haba mana Mamah ai kinsan bazaniya ba da dai kece se nayi dake" ya fada yana kashe mata ido se tayi saurin gyarawa ta dauki Bibin dake wani basarwa ta babu gaira babu dalili ta dan harareshi da wasa tace
"Kai kam baka jin kunya wlh a gaban yara"
"Kinga idan basu gane abinda na fada ba yanzu ke seka qara musu bayani" ya mayar mata daga haka taja bakinta tayi shiru. Tafiya sukayi motar shiru se Mu'ayyad da Iman da Aryaan dake baya suna buga game a Tab dinsa Bibi ta hade rai ta kalli window Humaira ko wayarta take dannawa shi kuma yana tuqi ya tsaya wani gurin siyar da kayan kwadayi ya fita Bibin ta balle murfin motar da gudu tabi bayansa se Humaira ta girgiza kai kawai a ranta tana ayyana rigimar yarinyar da taji Hajiya tana fadin Halin uwarta tayo aikuwa in hakane Mamansu ba qaramar fitinanniya bace dan Halin Bibin se a hankali wata irin yarinya ce me wuyar sha'ani da badan tana da haquri tana kuma dauke kai ba da tuni anji kansu da ita musamman akan shegiyar barbarta kamar Buranya wani sa'in idan tayi abu setaga kamar harda mugunta ma dan bata lalata abunta se na wani.
Basu jima baya fito da ledoji guda hudu a hannunsa Bibin na riqe da daya tana faman tura baki da alama ba'ayi mata yanda take so ba. A baya ya aje ledojin ya shiga suka dauki hanyar gida, tun a motar ta bude Ice cream dinta ta fara sha tana yi tana batawa Humairan jiki amma bata ce mata komai ba ganin kamar ma tana sane take zuba mata, titi ya hau suka dauki hanyar gida motar tayi shiru se ji sukayi Bibin tace
"Dady munga Momy ta dawo, kuma fa bata da lafiya dukta rame nace mata yaushe zata dawo gidanmu tace mu tambayeka, Dady yaushe zaka dakko Momy ta dawo gidanmu?" Tayi maganar tana tsare Khalil da ido kamar yanda shima yake kallonta tunda ta fara maganar ganin yana neman bugawa na gabansu yasa Humaira saurin kai hannu ta juya sitiyarin motar dukda yanda qirjinta yake bugawa da magabar Bibin yayi firgigit ya kama kan motar seda ya daidaita a titi kafin ya sauke ajiyar zuciya ya sake kallon yarinyar data zuba masa ido tana jiran amsa ya kalli Humaira data dauke wuta itama a hankali yace
"Seta warke tukunna tunda kince bata da lafiya"
"Toh ai ta warke Dady ta dawo kawai ta qarasa warkewa a gidanmu" tayi saurin sake fada seya maida hankalinsa kan titi ba tareda ya sake ce mata komai ba itama taci gaba da shan Icream dinta da rabi take zubawa a jikin Humairan.
Yanda yaga tana abubuwa a salube bayan sun isa gida ta shirya yaran bayan sun gama ciye ciyensu suka kwanta kafin ta wuce dakinta itama tayi wanka ta shirya a can ta kwanta dan gaba daya jinta takeyi se a hankali ta kuma rasa abinda ya janyo mata hakan. Gajiya yayi da jiranta ya bita dakin ya tarar harta kashe fitila seya kunna yana kallon yanda ta qudundune a bargo dukda dakin babu wani shahararren sanyi ya matsa kusada ita ya zauna yana cewa
"Ya kika zo kika kwanta baki ci abinci ba?"
"Naqoshi" ta bashi amsa kaitsaye ba tareda ta kalleshi ba se yaji wani iri yanda tayi masa maganar seya saka hannu ya dagota gaba daya zuwa jikinsa ya cusa fuskarsa a wuyanta yana cewa
"Fushin me Humairata takeyi?"
"Ni ba fushi nakeyi ba kawai bana jin dadi ne bacci nake so nayi" ta fada tana qoqarin zame masa saboda yanda yayi matan yasa ta fara jin wani yanayi a jikinta da bata so ya tsananta dan a yanzu abubuwa sun fara rikice mata, wasannin da yake mata suke bata nutsuwa tana jin kamar sun fara mata kadan jikinta yana buqatar sama da haka tunda kuma ba samu zatayi ba shiyasa take nesa nesa da duk abinda ze motsata.
Ganin tana tutture shi yasa ya tallafo fuskarta ya shiga kissing nata a hankali cikin kwarewa nan da nan kuwa tayi laqawas tana amsar saqon tareda maida masa da martani seda suka bata lokaci sodai dan shima yaji dadin yanayin bata fuskar sha'awa ba a'a kawai yana jin dadin tsotsar bakinta a kullum yana addu'ar ubangiji ya qare shi da lafiyar da jiyar da ita dadin data rasa ya sani tayi haquri tana kuma kanyi musamman a yanzu da ta qara girma jikinta ya bude yana lura da duk wasu sauye sauye tare da ita ya tabbatar tana buqatar sama da abinda yake mata shiyasa ya qara miqewa da gaske gurin neman magani dukda shekara uku kenan be zauna ba, duk inda yaji wani me maganin matsalarsa se yaje ya yarda warakar daga Allah take kuma idan yana da rabo ze samu.
A hankali ya zame bakinsa daga nata ya kalli idonta da suka rikice alamar tana kusa yace
"Toh idan ba fushi kikeyi ba muje ni ki bani abincin tunda kin qoshi".