← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 267

Sashe 150

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tas ta tarar da bangaren nata dan hatta da dakinta an zuba sababbin furnituresda suka fi wanda ta fasa kyau da tsada dukda ba'a gaya mata ba. Ruqayya ta kwalawa kira ta hau saman cikin rawar jiki ta sake gaisheta, Umaimah ta tambayeta yaushe aka saka kayan nan tace dazu da safe.
Sosa kai ta shigayi cikin son amayar da gulmae dake cikinta tace
"Ai tun jiya da Alhaji ya sanarwa Hajiya yau zaki dawo muna daga dakin Furera na jiya tana ce masa se ya saka a kawo miki sabon gado a saka. Yace baze siya ba, kinga rigimar da suka kwasa kuwa? Kai gaskiya Hajiya kinyi sa'ar uwar Mini matar nan tafi sonki ma inaga akan dan nata har cewa fa tayi zata saka azo a kwance nata gadon a saka miki tunda baze siya ba shine fa Alhaji hankalinsa ya tashi ganin tana neman tayi kuka yace ze siya. Wallahi Gadon ma ita ta zaba dan da safen tare mukaje wani kanti aka siyo kusan Miliyan nawa in gaya miki qarshe ma ita ta cika kudin dan abinda ya bayar be isa ba tasa aka zuba miki su".

Hannu kawai ta dagawa Ruqayyan akan taje ta zauna bakin gadon tana shafa katifar kamar wadda bata taba ganin ta ba se yau zuciyarta fal tunanin irin wannan Qauna da Hajiya takeyi mata. Turo qofa akayi da qarfi ta zabura dan a zatonta Khalil ne sega Mu'ayyad ya shigo da gudu Bibi na binsa a baya suka fada jikinta gaba daya suna ihun murnar ganinta.
"We missed you Mummy kullum muka cewa Daddy ya kaimu gurinki se yace gobe zaki dawo har na gaji da irga gobe" Mu'ayyad ya fada yana nuna matan goben daya irga da hannunsa. Qara jansu jikinta tayi tana murmushi dan itama tayi kewar yaran nata sosai tace
"To gani na dawo ai shikenan?"

"Yes Momy, meya samu face dinki it looks scary?" Ya sakw fada yana shafa fuskar tata da duk ta fita a kamanni ta swta riqe hannunsa kawai tayi murmushi dan bata san me zata ce masa ba,
"Where you involved in an accident?" Ya sake jefa mata wata tambayar, se kawai ta daga masa kai dan Mu'ayyad wayo ne dashi idan bata amsa ba ya ringa tambayarta kenan, saurin dagowa tayi jin muryar Khalil a dake yanayiwa yaran magana akan suje su kwashe kayan da suka zubda a falo. A firgice ta kalle shi dan bata ji shigowarsa dakinba kodan qofar a bude take shi yasa. Seda yaran suka fita kafin ya taka a hankali har ya isa gabanta, zuciyar Umaimah dake bugu kamar zata daka tsalle ta fito saboda tsoron yanayin fuskarsa. Tunda take dashi bata taba sanin ya iya hada fuska irin haka ba gaba daya se taga ya sauya mata ma tamkar ba Khalil dinta da koda yaushe idanunsa suke cike da bege da shauqin soyayyarta ba.

KHALIL
Kallon yanda ta firgita da ganinsa yakeyi daga inda yake tsaye yana jiyo yanda take fizgar numfashi tana dawo dashi da sauri da sauri kamar wadda Miciji ya ritsa. Kallon salihar fuskarta yake wadda take yaudarar mutane da ita ciki harda Hajiyarsa da ya rasa me Umaimah take mata da ta kasa ganin laifinta. A cikin fa wannan marrar data ja masa muguwar Asara Hajiyar ta tursasashi siya mata Gadon Miliyan daya, akan yace baze siya ba Hajiyar ta nemi zubarda hawayenta. Batayi masa kuka bama yana ganin ta kansa a hannun mace inaga tayi dolensa ya zare kudin ya bayar baqin ciki kamar ze qumeshi ya mutu. Wato tukuicin Asarar data janyo masa ya bayar yanda gobe idan ta tashi zata jijjigo wanda yafi wannan toh wallahi bataci banza ba, Hajiyar na fita ya dauki motar da Umaiman take hawa ya fita da ita ya siyar ya mayar da kudinsa garda riba. Da batayi masa baqin ciki ba ba Gado ba ko gida take so seya gina ya mallaka mata acikin abinda ze samu daga aikin da zeyi amma yanzu kuwa gadai gidan nan ta dawo ta zauna zata gane shayi ruwane za kuma tasan ba Lusaranci bane yasa yake dauke kai akan duk abubuwan da take masa a baya, tunda haka ta zaba yanzu zaman ze chanza zata san cewar shi Khalil ba kanwar lasa bene ba.

Juyawa yayi ya fice daga dakin Umaimah ta saki ajiyar zuciya ganin ya kullo mata qofa kafin ta miqe dakyar ta shiga bandaki saboda fitsarin daya matsota na tsoro, jan qafarta kawai take danhar sannan basu gama sauka daga kumburin da sukayi ba. Shirin bacci tayi gaba daya, seda ta leqa ta kira Ruqayya ta tambayeta ina yaran tace sun tafi gurin Hajiya da Yallabai kafin ta koma dakinta ta kwanta bayan ta jaddada mata ta tabbatar ta kashe komai kafin ta kwanta. Bata zaton zataji dadin me aiki ba se yanzu, haka ta raba dare tana sake saken sanda ya dace ta bawa Khalil din haquri har bacci ya kwasheta a sabon gadonta.

Washe gari kafin ta yi wanka ta shirya ma Khalil ya fice daga gidan, dan haka data fito kai tsaye dakinsa ta wuce da niyyar zuwa ta gaida shi tunda tasan a yanzu dai baze shiga dakinta ba kamar yanda suka saba. A kulle taji qofar dan haka ta shiga kwankwasawa ko daga ciki ya rufe, Ruqayya data hawo saman da kayan share ta gaisheta kafin tace
"Aiko ya fita Hajiya"
"Ya fita?" Ta maimaita a zuciyarta tareda tsurawa Ruqayyan idon tana mamakin ya akayi tasan Khalil din ya fita, kamar tasan me take tunani tayi saurin cewa
"Ina kitchen naji an bude qofa dana leqo se naga shine na koma, ga abin kari canna gama hadawa nan za'a hawo miki dashi ko na bari a qasan?"

"Ki kawo mun nan" ta bata amsa kafin ta juya dakinta. A nan falon saman ta karya kafin Ruqayyan ta gama gyaro mata dakinta ta dawo falon ita kuma ta koma ciki. Tun zuwanta daman Anty Laure ta zayyana mata ayyukan da zata ringayi, gyaran gidan gaba daya banda dakunan Khalil, Anty Lauren ke musu girki yau kuma da bata nan yasa tayi karambanin yi tunda kusan tasan me suke karyawa dasu da rana ko dare ne taga tana tambayar Umaiman abinda za'ayi.

Umaimah ko kan gado ta koma ta miqe gaba daya bata jin dadin komai, so takeyi ta kira Mama ta bata haquri amma bata san inda wayarta take ba dan haka ta tashi ta fito daidai Ruqayyan ta fesa Airfreshner ta dakata tana tambayarta ko akwai abinda take da buqata ne?
"Dakin da na zauna a qasa zaki duba mun ko wayata tana nan" ta fada mata se Ruqayyan tayi saurin cewa

"Tana nan kuwa, jiya da mukayi gyaran gidan na ganta se nasaka miki cikin drawer bari a dakko" da rawar jiki ta sauka qasa, Umaimah ta bita da harara, bata zaton zasu shirya gaskiya dan da ganinta zatayi tsugudidi ga shegen rawar jiki. Abinda yasa ma ta yarda da zamanta dan ta iya aikine kuma tasan ko mi maitar Khalil babu abinda zeyi da wannan kallo ma bata ishe shi ba sannan a yanzu tanada buqatar mataimaki kafin ta haihu ta komo hayyacinta sannan ne zata tantance tana da buqatarta ko Aa.

Wayar ta kawo mata harda chaja ta koma cikin dakin ta jonata a chaji dan a kashe take, bayan ta kunnata ta fara dubawa, ta tarar da tarin missed calls na Jama'arta, Safinah ta kirata yafi sau a qirga ga Text messages tana tambayar lafiya idan ta kira bata dauka da alama duka kafin wayar ta mutu ne akayi ta kiran da messages din.

Maman ta fara kira, yanda ta amsa mata ya qara sanyaya mata jiki bata ma bata damar yin wata magana ba daga gaisuwa ta dakatar da ita tace se anjima. Seta maida kiran kan Abba, shikam ya amsa mata a dan sake har yana tambayarta Khalil tace ya fita. Nasiha ya qara dora mata kafin sukayi sallama yana saka mata Albarka wannan yadan sanyaya mata rai ta qudurce zatayi ta kiran Maman kulkum har se itama ta haqura ta sakko. Maman Asad ta kira, missed calls hudu tayi mata amma taqi dagawa na qarshe ma rejecting tayi hakamya tabbatar mata da tana kallo dagawar ne batayi niyya ba seta aje wayar kawai dan ta tabbata tunda Hajiyayye bata dauki wayarta ba to gaba daya sauran ma bazasu dauka ba alamar labari yaje musu kenan daman kuma har ta gama jinyarta babu wadda tazo gidan a cikinsu ai shikenan babu dai yanda suka iya da ita duk fushinsu dole suyi su gama su sakko.

Khalil dai dagaske yake shareta a gidan dan daya dawo da yamma ma tana zaune a falon saman tayi masa sannu da zuwa bata zaton ya amsa dan bataji ba ya wuce dakinsa ya bude ya shiga, data bishi ta kwankwasa kamar su da wani suke zaune a gidan yake tambayarta wai waye, abin ya qona mata rai amma ta daure tace Umaimah ce. Seda ta kwashi minti biyar a tsaye tana jira ya bude amma shiru, bata haqura ba ta sake kai hannu da niyyar bugawa se gashi ya bude yayi bake bake a bakin qofar tareda tsareta da ido. Duk seta duburburce ta kasa ce masa komai ganin tana bata masa lokaci yasa ya juya ciki ya sake rufe qofar tana ji ya murza muqulli wani abu ya tokare mata wuya, ta tsani wulaqanci a rayuwarta koda ace laifi ta masa ai be kamata yayi mata haka ba se ya bari ta shiga yaji abinda ya kawota ko yana nufin a bakin qofar zasuyi magana.
Chapter 150 · 0% Book details