← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 267

Sashe 70

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Biki mukazo kaga ni bamu sani ba har dare yayi ashe mun rasa motar tafiya gida duk wanda muka tsayar se yace mana ba hanyar zeyi ba ga lokaci yana ta sake tafiya dan Allah idan babu damuwa ka taimaka ka kaimu gida mana" Budurwar ta sake fada dayar tana zungurinta akan tayi shiru amma taqi.
Kallonsu yayi sama da qasa, a haka dai basuyi kalar watsatstsun yammata ba kuma ya ga dagaske bikin sukazo amma me yasa sun san unguwarsu ana wahalar samun mota zasu kai dare a gurin har qarfe sha daya na dare shi ya rasa ma wannan abu da zaace biki ba zaayi shi a cikin gida ba se an tafi yawon guraren shaqatawa kuma ita Amaryar ya za'ayi ta tafi bata tabbatar da duk jama'ar data tara kowa ya isa gidansu lafiya ba?

"Dan Allah ka taimaka mana idan kuma ba zaka iya ba mu nemi wani dare yanayi" yarinyar ta sake fada taba marairaicewa, se Khalil ya kalleta kamar yace bazashi ba se kuma tausayinsu ya kamashi, Mata ne idan be taimaka musu ba besan gurin wa zasuje ba shin zasu samu na gari ko kuma mugu a yanda rayuwar nan ta lalace haka, muqullinsa da wayarsa ya dauka yayi gaba ba tareda ya musu magana ba suka bi bayansa, har sun isa jikin motar suka waiwaya,

"Hadiza bazakizo mu tafi ba" suka hada baki gurin fada se ya waiwaya ya kalli wadda suka kira da Hadizan, tana sanye da irin kayansu sedai ita ta dora hijabi daya kai mata guiwa akai. Su ukun suka shiga ya dauki hanyar Na'ibawa kamar yanda suka gaya masa sunan unguwarsu, seda ya kaisu har qofar gida, a lungu suke cikin ransa kamar ya dake su ganin yanayin unguwar tasu sannan hat su iya kaiwa dare haka dole su rasa motar dawowa ai.

"Bazaki bari ya qarasa dake gida ba Hadiza?" Mw rawar kan cikinsu ta sake fada ganin itama Hadizan ta sauka bayan su biyun sun fita seta girgiza kai tace
"Aa nan ma yayi, na kira Musa nace ya jirani a nan mu qarasa gida kin ganshi can ma" ta fada tana nuna dan matashin saurayi da suke tsaye su biyu daga gefe, Khalil yabi shi da kallo kamar su daya da ita hakan ya nuna qaninta ne ya tabe baki ya tada motarsa sunayi masa godiya be ko bi ta kansu ba ya juya mota yana jin dayar na cewa
"Kunga be karbi lambar ko daya daga cikinmu ba babu wadda tayi masa ai shikenan".

Kafin ya kai gida sha biyu tayi, haka ya lallaba yasha ruwan lemon tsami ya kwanta, kafin bacci kuwa ya dauke shi yayi wanka yafi sau goma haka yayi bacci a wahale.

A can gida kuwa fada Mama ta rufe Umaimah dashi kamar zata daketa seda Anty ta shiga tsakani,
"idan kika kashe auranki Umaimah ki nemi gurin zama badai a gidan nan ba tunda ke shaidaniyar yarinya ce mara jin magana. Yanzu daman abinda kika je kikayi kenan sannan kika hada musu rigima a cikin family saboda bakya tsoron Allah kici gaba Umaimah idan daidai kikeyi zaki gani" Mamq ta fada muryarta na rawa kamar zatayi kuka Anty ta shiga bata haquri ta fice ta barsu.

Fada Antyn ta ringayi mata se kuma jikinta yayi sanyi, tun a daren ta fara neman Khalil amma bata samun wayarsa ita kanta bata iya bacci me dadi ba a ranar har washe gari kuwa yaqi amsa mata waya seda aka kwana biyu sannan ta same shi shima amsa daya ya bata bayan data gama surutunta yace ta zauna ta qara hutawa sosai karta dawo yanzu. Kuka wiwi ta dasa musu akan se su nemo shi su bashi haquri daman Abbansu baya gari lokacin da ta qulla tsiyarta, koda ya dawo aka mayar masa da yanda akayi be ce mata komai yace a rabu da ita ai Bari ba shegiya bace idan taji jiki da kanta zata maida kanta gidanta shiyasa koda tana tanbotsan haukanta babu wanda ya kulata, data ishesu da iface iface Mama tayi mata biji biji dole ta shiga hankalinta.

Binbini da kiran waya kuwa babu irin wanda bata yiwa Khalil amma kullum amsar daya ce ta zauna ta qara hutawa dukda dauriya ce kawai yakeyi dan ya fuskanci idan ba ya zama namiji akan Umaimah ba iskancinta kullum qara ta'azzara yakeyi.
Seda aka shafe sati uku a haka, ganin fa dagaske Khalil ya fita a sabgarta dan daga baya dena daga wayarta yayi ko idan ya daga yace mata yana aiki ze kira kiran da bazeyi ba kenan seta komawa fakewa da Mu'ayyad. Haka kawai zata kirashi tace suna son abu, ranar farko yazo har qofar gidan ya kaqo mata siyayya tuli abinda ta nema da wanda bataa nema ba be shiga ba ya bawa yara ya hada mata da kudi cikin envelop yace akai mata.
Ranar akan yan aiken ta huce ta ringa rashin mutunchi da tijara a cikin gidan kwana biyu a tsakani ta dorawa Mu'ayyad ciwon qarya nan ma bezo ba ya turo mata Khalifa dan bama ya gari a sannan yayi tafiya.

Kuka wiwi ta kirashi a ranar tanayi masa ta bashi haquri yace mata yanzu dagaske ze haqura amma da sharadi, sharadin kuwa shine se taje ta gayawa Hajiya da bakinta duk abinda ta fada mata qaryane saboda yanzu haka akan wannan dalili gaba me qarfi ta qullu tsakanin Hajiyar da Goggo Zara'u haka cikin dangi sun kasu biyu kowa da wanda yake goyon baya.

Hankalin Umaimah ya tashi da jin wannan sharadi nasa toh ta ina zata fara zuwa ta cewa Hajiya qarya takeyi yanzu? Amma da yake neman shiri takeyi tace masa ta yarda washe gari kuwa babu wanda ta gayawa inda zata da sassafe ta wanke qafa tayi gidan Hajiya, Mamakin da Hajiya ta nuna na ganinta da kuma tambayarta da takeyi na yaushe suka dawo ya sakata chanza plan ashe Hajiya batasan da cewar har sannan tana gidansu ba daga baya ne ma da taji shiru kwana biyu ta tambayi Khalil yace mata ta tafi Minna gurin Yaya Naziyya da suka koma can da Mijinta dan ko haihuwar Umaiman bata samu zuwa ba shine taje gaisheta.

A maimakon ta gyara abinda ya kaita seta zauna ta sake zuba sabon lalen gurmi, kuka ta fasa wa Hajiya akan Khalil yayi fushi da ita tun akan waccen maganar dan har yanzu tana gida yace ba zata koma ba seta je ta bawa su Badariyyah haquri, ran Hajiua ya baci ta dauki waya zata kirashi Umaimah ta hana

"Idan kika kirashi Hajiyavze qarayin wani fushin yace na hadaki dashi, nidai dan Allah karki gaya masa na fada miki wani abu, kawai ki nuna masa kinsan ina gida har yanzu ya barni na koma dakina dan yanzu wallahi Hajiya gidanmu kowa fushi yake dani babu meyi mun magana" Umaimah ta fada tana matsar hawaye, Se Hajiya taja kwafa tace

"Da kin barni na kirashi ai naci masa mutunci mutumin banza kawai yanzu shi har idan yana da zuciya ze saka daga ido ya kalli Zara'u da duk wani natane mutanen da suka qishi saboda abin duniya shine yanzu zasu dawo masoyansa, ze dawo ya sameni ita kuma Hajiya Malika da zata ringa biye masa itama zanje har gidan na sameta ai haba shikenan se abi a tsangwameki kuma akan gaskiyarki" haka ta ringa fada daga qarshe tace ta koma ta hada kayanta ta koma dakinta shi kuma Khalil din zata hadu dashi idan ya dawo suka rabu Umaimah na sake roqon karta gayawa Khalil komai, a daren ranar kuwa se gashi da kansa ya kirata yace ta shirya washe gari ta koma shi se jibi ze dawo, Roqonsa tayi akan ya bari ta koma jibin da safe dan gobe zatayi kitso da sauran shirye shirye haka kuwa akayi washe gari ita kadai ta ringa hidimarta daman Anty ce me tayata ita kuma bata nan Ankwantar da yayarta a Asibiti ita take jinyarta.

Bayan komawarsu tayi zaton zeyi mata fada ko ya tado da maganar sedai taji shru, tun tana dari dari harta sake suka ci gaba da rayuwarsu tamkar babu abinda ya faru. Sabon  babi suka bude na rayuwa me cike da qauna da tattalin junansu, Tsakanin Khalil da Umaimah kullum cikin rige rigen kyautatawa junansu suke tareda tattalin tilon dansu da suke ji dashi kamar tsoka daya a miya. Qarin hidimar Mu'ayyad da rashin sabo ya saka aiki ya kan kacamewa Umaiman musamman da Mu'ayyad din ya koyi rigima ya koda yaushe yafi son yaji shi jikin mutum dan haka idan dai ba yana hannun Khalil ba to sedai ta goyashi idan tanaso tayi ayyukan gida, saboda rashin sanin yanda zata tsara ayyukanta se ya zamana wani lokacin har Khalil ya dawo daga aiki bata samu ta kammala abinci seya jirata haka wankin yaron duk takarar da Mama tayi mata a gida akan karta ringa tara wanki tayi qoqari da tayi masa wankan safe ta wanke kayan daya bata amma bata iyawa gajiya takeyi dan lokacin hutun nata idan yayi bacci sannan take samu ta leqa social media dukda yanzu ta kiyayi duk wata da take shishshige mata dason yin qawance da ita qarqarinta hira a group shikenan.

Qarin abinda Yafi damunta a yanzu shine yawan tafiye tafiyen da Khalil yakeyi kuma yace dole da ita ze tafi dan idan har tafiya ta wuce ta kwana biyu tofa qafarsa qafarta wanda sam ita abin beyi mata ba bata so kullum cikin qorafi take da wuya kuma suyi tafiyar aje a dawo lafiya basu bata ba, ta ringa mita kenan da fadar maganganu da azatonta zasu saka yayi zuciya gaba ya qi tafiya da ita kamar yanda Rufaida ta bata shawara amma ko a jikinsa, yi yake kamar besab tanayi ba.
Chapter 70 · 0% Book details