← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 203 OF 267

Sashe 203

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon Abban yayi yana so yayi magana amma ya sake katse shi da cewa
"Bana so naji komai sannan maganar nan ta tsaya tsakanin nida kai ko Mahaifiyarka karka fada mata nida kaina zanyi mata bayani babu abi da za'a jira kuma yarinya zata tare a dakinta ita kuma Allah ya kaimu ta tashi zanyi maganinta in Allah ya yarda.

Se Magriba suka watse daga Asibitin aka bar Mama da Anty Hafsa har sannan kuma Umaimah bata kuma farkawa ba sedai likita yana shiga ya dubata ya kuma tabbatar musu babu damuwa zuwa dare zata farka suna fatan kuma kafin sannan komai ya daidaita.
Guraren goma Khalil ya koma Asibitin dan tun bayan da suka gama magana da Abba ya wuce gida Adaidaita ma ya hau ya kaishi be zata ze iya bacci ba nan da sati daya ma se gashi da taimakon maganin daya sha yayi bacci sosai har bayan Isha sannan ya tashi bayan yayi wanka ya rama salloli ya leqa Dakin Humaira yaga barnar da Umaimah tayi, gaba daya gidan Qamshin Humarar da suka malale a qasa yakeyi ya maida qofar ya rufe yana tunanin abinyi ya wuce bangaren Hajiya a canya tarar da Jalilah ta kafa daba sun dawo daga gidan biki dan duk wannan tashin hankalin da aka sha seda taje da mutanenta Jamila ce kadai bata je ba suna Asibiti tare dasu Hajiya sunje sun sha bidirinsu dan basu gaya musu abinda ya faru ba suma kuma yan jeren da yake ba masu surutu bane basu fadi abinda akayi ba Mama kadai Sumayyan ta gayawa ita kuwa da dama tasan za'a rina batayi mamaki ba.

A daki suka qule da Hajiya take gaya masa zancen kawo Amarya gobe da Baban Umaimah yayi,
"Babana ina jin tsoro, nayi nayi Alhaji ya fahimceni amma yaqi ya kum samu goyon bayan Baban ku Abubakar sun kafe akan gobe zasu dakko Amarya dan har ma sunyi magana da Kawun nanta su kuma sun sanar da Hajiya Hauwan dazu ta kirani take ce mun babu komai hakan ma yayi ai suma iyayenta ne daga baya duk me son zuwa yaga daki se yazo, nidai ban gaya mata halin da ake ciki ba gaskiya dan bansan ta inda zan fara mata bayani ba" Hajiya tayi maganar cikin jimami, se Khalil yace

"In sha Allahu babu abinda ze faru se Alkhairi Hajiya"
"Toh Allah yasa" daga nan yayi mata sallama ya koma Asibitin. A canma dai maganar suka sakeyi da Mama da Anty Amina suna sake qarfafa masa guiwa, har gurin sha biyu yana can kafin yayi musu sallama ya tafi har sannan kuma Umaiman bata farka ba.

Kamar yanda Abba da Baba Abu sukayi Alqawari washe gari aka kawowa Khalil Amaryarsa, sedai basu je da kansu ba kamar yanda suka tsara daga baya suka canza shawara dan haka Aka wakilta Mata guda uku daya daga bangaren Mahaifinsa daya qanwar Hajiya se Aminiyarta daya suka dakko masa Amarya ta iso da rakiyar nata iyayen guda hudu suma. A bangaren Hajiya aka tarbesu kuma anan suka barta suka wuce suna yi musu fatan zaman lafiya.

Khalil na Asibiti aka kawo Amaryar dan wunin ranar gaba daya acan yayi shi kuma tun jiya da rana da suka rabu akan zeje ya canza kaya ya koma suyi hoto basu sake yin waya ba wayar tasa ma a motar ya barta be dauka ba har sannan, a bakin Sammani da sukaje kai abincin dare yaji cewar Ankawo Amaryar. Seda Mama ta matsa masa kafin ya bisu gida suka koma tareda Khalifa da Sammani.
*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

Page 72

Ko minti goma Khalil beyi da fita Abba da Anty suka isa Asibitin. Abban ya tsaya akanta yana kallo ta kafin juya yana tambayar Mama har yanzu bata farka ba Maman ta sauke numfashi tace
"Bata farka na Alhaji amma sunce da vi gaba tunda gashi numfashinta ya daidaita sun cire mata Oxygen bacci takeyi kowanne lokaci kuma zata iya farkawa"
"Toh Allah ya tashi kafadunta ya kuma sanyaya mata zuciyarta ta karbi qaddara a yanda tazo mata tunda me afkuwa ta rigada ta afku yanzu haka yarinyar ma tana cikin gidan, ni ina ganin koda ace an sallameta daga nanzamu wuce da ita can gidane zuwa wani lokaci seta koma, Allah dai ya qara rufa Asiri". Haka suka ci gaba da zama a Asibitin basu ankare da lokaci ba se gani sukayi sha biyu tayi, Abba da Anty suka tafi gida suka bar Mama da take kwana da ita kafin ya tafi seda ya sake magana da Likita ya tabbatar masa da komai lafiya sannan idan bata farka zuwa Safiya ba zasu farkar da ita da kansu.

A hankali ta sauke dogon numfashin data riqe tun zuwan su Abban ta farka daga baccin wahalar da take tayi tun jiya tana farkawa kuma duk abinda ua faru ya dawo mata a kwakwalwa tamkar a lokacin yake faruwa. Hirar da Abba da Maman sukayi kaf a kunnenta, sanda taji yana gaya mata Amarya ta tare seda tayi da gaske kafin ta hana kanta fasa Ihun da ze sa susan idonta biyu, taci gaba da kwanciya tana saqe saqen abinda ya kamata tayi a zuciyarta, a haka Nurse did da take dybata ta shiga ta sake mayar mata da ruwan da ta cire mata dazu ba tareda tayi aune ba bacci ya sake awon gaba da ita.

KHALIL
Cikin mutuwar jiki ya shiga bangarensu, Dakin Humaira ya fara shiga an guara shi tsaf dan tunda safe ya saka su Sammani suka gyara aka kwashe duk abinda ya lalace a ciki kijerunta kadai ta tsira dasu baya ga haka babu wani abu da ze moru a kayan falon sedai ko Carpet idan an wanke shi. Seda ya gama duba gurin kafin ya kulle ya wuce Dakinsa. Wanka ya shiga, ya dade yana wankan shikansa bazece ga dalilin wannan wankan da ya zauna ya ringa dirje jiki kamar wanda ya shekara beyi ba. Kansa ya kalla a Mudubi yaso ace yayi Aski jiya se kuma wannan tashin hankalin ya bullo.

Haka ya fito ya shafa mai da turaruka a jikinsa gaba daya a sanyaye yakeyin komai. A gurin zabar kayan da ze saka ma seda ya bata lokaci, Sky blue sabuwa ce be taba sakata ba ya zura kayan sun zauna masa a jikinsa irin dinkunan da Umaimah take so Abuja style Riga Jumper me gajeran hannu kayan sunyi matuqar yi masa kyau kamar a jikinsa aka dinka su. Seda ya sake feshe Jikinsa da turaruka ya dakko Hular data dace da kayan ya kafa ya daura Agogo, harya zura takalmi ze fita se kuma ya dawo da baya. Wardrobe ya bude ya dakko sabon Bedsheet babba dan Turkey, Umaimah ce ta siya masa da kudi bata taba shimfida musu ba ya cire wanda yake kan gadon ya mayar da sabon, seda ya sake bin dakin ya kawar da duk wani abu da ba'a muhallinsa yake ba dukda babu tarkace a dakin saboda shi baya ajiye kaya a ko ina duk abinda yayi amfani dashi ya gama ze mayar dashi gurin zamansa, ya jona Bunner ya zuba turaren wuta sannanya saisaita sanyin Ac daya kunna kafinya kashe fitila ya fice daga dakin.

Missed calls din Hajiya ya gani a wayarsa dana Anty Amina, qarfe goma da minti biyar ya ringa mamakin lokacin daya bata dan haka cikin hanzari ya tafi bangaren Hajiyar dan yaji kiran da take masa. A bakin qofa suka hadu da yan uwansa da alama tafiya zasuyi. Jalilah ta dauke kai tayi gaba Anty Amina ma fuska babu yabo babu fallasa ta amsa gaisuwar da yayi musu kafin tace
"Ai mun zata can zaka kwana tun dazu ake kiranka ga yarinyar mutane can ka barta ita kadai".

Kansa ya sosa ba tareda yace mata komai ba Jamila ce ta dan saki fuska tace
"Zaka sha rarrashi yau dan Amaryar nan taka da gani rigimammiya ce tana can ko ruwa taqi sha tunda aka kawota, na aiki Khalifa dai ya siyo muku dan abinda zaku buqata dan nasan dakyar in kayi tunanin nemo mata abinda zataci"

"Backs yar uwata you are the best" ya fada yana rungumeta ta gefe Jamila ta tureshi tana dariya tace
"Toh Allah bamu Alkhairi", a fusace Jalilah da har tayi nisa ta dawo tana kallon tace
"Idan ba zaki tafi bane muyi gaba kin zauna kina bata wa mutane lokaci da wanda basu san darajar kansu ba, be tanka mata ba kamar yanda itama Jamilan binta kawai tayi yasan jarabar Jalilah yanzu se a shekara tana wannan fushin to shi dan Allah meye laifin sa a nan? Idan bata tausaya masa ba ai be kamata ta qullaceshi ba.

Da sallama ya shiga falon Hajiyar suna zaune ita da qanwarta Hajiya Maimuna Mamansu Lubna suka amsa masa a tare ya samu guri a qasa ya zauna yana gaishe su suka amsa gaba daya tareda tambayarsa yame jiki se ga Khalifa ya shigo da manyan Ledoji guda biyu ya kalli Khalil yace
"Yaya gashi Anty Jamila tace na siyo"
Ba tareda ya kalli Khalifan ba yace
"Ka shiga dasu can gurin" se Khalifan ya juya ya fita.

Bayan yar gajeriyar Nasiha da Hajiya da yar uwarta suka sakeyi masa Hajiya Maimuna ta miqe tana cewa
"Yaya bari naje dare na qarayi"
"Mama ina kuma zakije a daren nan?" Khalil ya fada yana kallonta seta yafa mayafinta tace
"Gidan Alqasin zanje na gaji da ciwon bakin da yake muk akan duk sanda nazo Kano ina kwana gidan kowa banda nasa yau can zan kwana gobe in Allahya kaimu muyi Asubanci mu koma gida kuma mu huta haka"

"To bari nazo na kaiki" ya fada yana miqewa se tayo saurin dakatar dashi ta riqe baki tace
"Waya isa ya fitar da Ango a daren nan? Kaga tafi ka rarraso Amaryarka tana ciki tana kuka kaga ni Khalifa na can waje yana jirana shi ze saukeni daman su Lubna sunyi gaba tun dazu" daga haka tayi gaba Hajiya ta miqe danta rakata.
Chapter 203 · 0% Book details