← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 267

Sashe 34

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wai bakya gajiya da kuka ne" ya fada murya a cukule, Umaimah taja doguwar sheshsheqa kamarme shirin shidewa tace

"Ba kaine kayi fushi dani ba, dan Allah kayi haquri bazan sake ba. Wallahi kasa controlling kaina nayi shiyasa amma na gane nayi kuskure bazan kuma maimaitawa ba" ta fada tana shirin cigaba da kukan.

"Kullum haka kike cewa ai amma idan kika tashi se kinyi abinda yafi na baya. Dambe fa kikayi niyyar yi a cikin mutane, kina zaton da kunyi da yanzu video ki be gama zagaye Social media ba yanda qiris mutane yanzu suke jira su fara recording abu wane irin kallo kike so mutane suyi mun ace matar da zan aura aka gani a titi tana dambe? Saboda kinga ina kyaleki ne yasa kike abinda kika ga dama ko? Shi kenan zan dauki mataki" Khalil ya fada a hankali amma a muryarsa zaka karanci bacin rai.

Marairaicewa tayi sosai tace "Ai bamuyi ba ma zan tabayi ba in sha Allah kayi haquri, na yarda in dai na sake yin wani abu irin wannan ka dauki kowanne mataki na yarda"

"Haka kikace ko? Kinsan irin matakin da zan dauka ne?"
"Koma wanne irine na tabbata ma bazan sake ba balle kayi wani abun" ta tareshi a shagwabe kafin ta sake cewa

"Ka haqura toh?"
"Da ban haqura ba bazan amsa wayar ba ai, wayar waye wannan? ina taki wayar ma da kika kirani data mutane?"

"Ba ka tafi da jakar a motar ka ba wayar Rumasa'u na ara nasan ma koda ace wayata na nan idan na kira bazaka dauka ba.

"Oh ashe akwai wadanda kika yarda dasu haka da har zaki iya kirana da wayar su?"

"Ruma ce fa Aminiyata, nasan ko kowa zeci Amana ta a duniya banda ita amma ai ba barin number zanyi muna gama magana zan goge, yaushe toh zaka kawo mun tawa wayar? Nasan mutane suna ta kirana" Umaimah ta fada, se Khalil yace

"Nayi seizing dinta se kinzo gidana sannan zan baki nima zan duba ciki na gani yanda kike mun bincike a waya"

"Babu abinda zaka samu a wayata, amma ka taimaka ko Sim din ne ka kawomun na saka a qarama saboda qawayena da zasuje Kamu gobe zasu kirani"

"Zan duba na gani" ya bata amsa daga nan sukayi sallama.

"Gaskiya zan Hada Umaiman nan da Nusyta ta rakata inda takai sunanka nima a shawo mata kaina, jifa yanda ka gama masifa kana fadar maganganu kai zaka fasa, ka shigo fuska kamar wanda ya fada cikin kashin shanu amma daga jin muryarta ta kalallame ka duk kububuwar daka hau ka sakko kana wani kashe murya dole da abinda yarinyar nan ta taka shi yasa take iskanci son ranta" Mansur da tunda suka fara wayar ya saki baki yana kallon ikon Allah ya fada.

Se Khalil ya saki murmushi yace
"Inason yarinyar da yawa Mansur ko nayi fushi da ita baya dorewa tana da shiga rai yanda baka tunani"

"Naga alama" Mansur ya fada kafin yaja kwanon funkasonsa yaci gaba daci.

Umaimah kuwa ajiyar zuciya ta saki a fili tace "An rufe wannan case din saura na cikin gida".
Dakin ta koma ta tarar da Halima na shirin wucewa itada Fannah.

"Aa ina kuma zakuje" Umaiman ta fada bayan data miqawa Ruma wayarta se Haliman ta amsa ta da cewa

"Gidana zamu wuce ta huta se gobe idan mun hadu a gurin Kamu"
"Kedai ki wuce amma ita ai biki tazo dan haka babu inda zata je, yi haquri Fannah bari na kawo miki ruwa da abinci wallahi wata wuta na kashe ne se yanzu na samu nutsuwa" Umaimah ta fada tana mayar da Fannan ta zauna.

Haka Halima ta tafi ita kadai bayan da suka daukowa Fannan akwatinta daga mota. Cikin gida Umaimah da Ruma suka shiga karbo abincin, Anty ta samu da wasu qannen Mama biyu a kitchen suna hidima suka dibi wanda ze ishe su ga ruwa da Zobo masu sanyi, sabulun wankanta ta tuna yana dakinsu dan haka ta cewa Ruma tayi gaba gata nan zuwa.

A dakin ta tarar da Mama tana zaune akan gado Nuratu na durqushe a gabanta tana kuka.
"Zonan, ina kika tsaya tunda kuka dawo baki shigo gida ba?" Maman ta fada tana kallonta idonta da alamar itama kukan tayi ko take so tayi se Umaimah ta qarasa kusada Nuratun ta zauna a ranta tana cewa

"Bata bada labarin abinda ya faru ba kenan".

"Kamar yanda na fara gayawa yar uwarki daga yau ba zamu sake samun lokaci irin haka nida ku mu zauna ba, duk abinda ya kamata ku sani kun rigada kun gani a aikace tsahon shekarun da mukayi tare daku.
Kuna shirin shiga wata sabuwar rayuwa ce me cike da qalubale kala kala wadda idan kukayi haquri kuka jure sakamakonta me girma ne wato Aljanna.

Aure ya wuce duk yanda kuke zato, duk abinda kuke hange a cikin rayuwar gidajen wasu zahiri ne amma badinin aure bazaka sanshi ba se randa ka tsinci kanka a cikin sa. Abinda nake so ku saka a ranku shine Aure ibadar Allah ce, kamar yanda zakuyi sallah dan lada to ku tabbata duk wani abu da zaku aikata a cikin gidan aure kuyi shi domin samun lada.

Banida matsala da Nuratu amma dukda haka zanja kunnenku gaba daya shi Miji shugabane ubangiji ne ya bashi wannan girma da darajar dan haka a matsayin mace da take qarqashinsa dole ta girmama shi in har tana so ta gama lafiya.

Umaimah duk wata rashin kunya da fitsara da kikeji dasu ki tattara su ki ajiye a cikin gidan nan domin idan har kika tsallaka da daya zuwa gidan aurenki ki tabbata da cewar kin qulla guzurin kai kanki wuta da qafarki Allah ya kiyaye. Girmamawa tsakanin ku da Mazajen ku dolece haka iyayensa da duk wani da yake gaba daau dole ku girmamashi tamkar yanda kuke girmama na gaba daku sannan kuso qannensu kamar yanda kuke son naku.

Karku zama masu yawan qorafi da kai qara, Banda fitar da sirrin gidan auranku, matsala idan ta faru ku zauna ku warwareta a tsakanin ku indai ba tafi qarfin ku ba shine zaku sako na gaba daku a ciki.
Ku zama masu tattali da kula akan duk abinda Mijinku ya kawo kuma ku zama masu godiya da nuna jindadi idan sunyi muku abu komai qanqantar kyauta ku gode koda kuwa abun beyi muku ba ko bakqmwa so hakan yana qara musu qarfin guiwar suyi muku.

Umaimah banda jajibe jajiben qawaye, Kullum addu'ata Allah ya rabaki da qawayen banza Allah ya karbi Addu'ata ina fatan zaki dore kici gaba da rayuwarki a haka tunda babu abinda ya ragu a jikinki saboda kin dena tara qawaye sema qarin samun nutsuwa da kika samu a rayuwarki to kiyi qoqari ki dore a haka.

A qarshe ina so ku dauki rayuwar gidannan data sauran yayyenku dan ta zame muku madubin dubawa. shekarata Talatin da Tara a cikin gidan nan tareda Mahaifinku amma daidai da rana daya ban taba fita da sunan yaji ba, da dadi babu dadi nayi haquri mun zauna gashi har na haife ku kun girma ina shirin aurar daku da kuka rage a gabana kunga bani da abin cewa sedai na godewa Allah na kuma qara gode masa kuma ba komai bane jigon zamana se haquri da Addu'a sune manyan makaman da in har bawa ya riqe su baze taba tabewa ba a rayuwarsa.

Allah yayi muku albarka, Allah ya albarkaci gidajen auren ku yasa mutuwa ce zata fito daku, Allah yasa ku zama sanyin idaniyar abokanan zamanku ku ya basu ikon riqe ku da Amana".

Kuka Nuratu takeyi Hajiya Umaimah kuwa jiki dai yayi sanyi se qifta idanu takeyi. Muryar Mama taji tana cewa Nuratun taje taci gaba da sabgoginta se itama ta miqe Maman ta dakatar da ita tace

"Zauna ban gama dake ba" seta nemi guri ta zauna a ranta tana cewa
"Ashe da saura na zata bata fada ba wallahi kuwa in har aka mun fada itama se ranta ya baci sedai muci bikin kowa da bacin rai".

"Umaimah" Maman ta kira sunanta sam babu wasa a muryarta kafin taci gaba da cewa

"Bana buqatar jan wani dogon bayani, Allah ya gani a cikin yaya bakwai daya bani ban banbanta wani da wani gurin bayar da tarbiyya ba, na raine ku akan turba daya na koyar daku abu daya amma kin fita daman da sauran ta kowacce siga.

Ina so ki sani daga yanzu zaki koma cin gashin kanki ne kuma zuwa nan da wani lokaci kema zaki zama uwa me bada tarbiyya dan haka kisan abinda kikeyi. Ki nemi guri ki zube duk wani shirme da rashin hankali da kika mayar dabi'a ki gane ainihin rayuwa da inda ta saka gaba.

Aiki da ake sakaki kiqi yi ko kiyi abinda kika ga dama, girkin da kike cika mana gishiri ko yaji a ciki da duk wasu sauran Iyashege da kikeyi a cikin gidan nan tamkar karatune yanzu ne zaki fara zana jarabawar abinda kika koya, idan kinyi da kyau ki wuce lafiya idan kin fadi kece a ruwa dan ni babu ruwana Allah shine shaidata duk abinda ya kamata Uwa ta koyawa yarta na koya miki.

Ina sake jaddada miki batun qawaye babu ke babu su, ki tattara kowa da komai a gefe ki fuskanci gobenki Umaimah, wannan Azabar kishin da kika sakawa ranki ki cire idan kinqi ke zaki sha wahala dan karki taba zaton yanda yake biye miki a waje kici mutuncinsa ki bashi haquri daga baya ya haqura ki zata haka zata ci gaba a cikin gidan, bana miki fatan ya zama daga cikin mazan da suke shanye wulaqancin Mace a waje idan ta shiga hannunsu su rama amma koma me ya biyo baya ke kika siya da kudinki dan abinda kika shuka ne zaki girbe".
Chapter 34 · 0% Book details