← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 267

Sashe 129

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

...*KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ƳAR'UWA, WATA-ƘILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.*
Ƴar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassaƙe da garin magunguna na gargajiya, waɗanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu.
*Ina matan da basu taɓa haihuwa ba?* Ko kuma sun taɓa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa ɓari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? Ƴar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata ɗaya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari.

*Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haɗa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari.

*Ƴar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haɗa miki magunguna kala biyar, waɗanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daɗewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haɗi *Bye bye infection.*

*Mijinki ne bai da kuzari a shimfiɗa?* Ƴar'uwa ko ki faɗa ko kar ki faɗa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan ɗaya wanda zai dinga shan ƙaramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ƙara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda.

*Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huɗu da za ku fatattaki daji daga jikinku.

*Ingantaccen haɗin sabaya😍* Haɗin sabayarmu duniya ne ƴar'uwa. Baza muyi miki ƙaryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga sheƙi, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haɗin sabayarmu.

*Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk ɗauri ɗaya 500.

*Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuɗin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuɓeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo😍😍😍*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

Page 50

Washe garin ranar dukda Asabar ce ya fita saboda qarasa wani paper work da yakeyi na wani aiki. Dukda kwararrunma'aikata daya dauka sau da yawa duk wani shi yake tsayawa yanayi dakansa dan baya so a samu akasi, mutane sun yarda dashi sun bashi amanar ayyukan da beci ace qaramin company irin nasa yanayi ba dan haka yake gudun duk wani akasi.

Yana office Hajiya ta kirashi cikin fadan da ko bata fayyace masa ba yasan Umaimah ce taje ta hada wani gurmin. Hajiyar na kashe wayarta ya kira Yaya Aminu, ya gaji da yanda take zuwa tana hadashi da mahaifiyarsa amma shi baze kai qararta gurin nata iyayen ba dan haka ze hadata da Yayanta yaja mata kunne duk abinda zasuyi ya tsaya tsakaninsu karta sake kai qararsa gurin Hajiya.

Tsaf ya labartawa Aminun komai ya ringa fada ya kuma dora kacokan laifin akan Khalil kamar koda yaushe sabodaa ganinsa shi ya sakar mata take duk iskancin dataga dama.
"Kuzo da ita dan ubanta tunda bata ji nima na dena handling case dinta ni kadai gara mune gaban Abban ko kuma Baba Abdullahi ai tasanshi kamar yunwar cikinta ubanta zeci tunda ita batajin magana" Aminu ya fada suka rabu akan yau da daddare zasuje gidan sa da Umaiman.

Sanda ya koma gida bata nan kenan gidan Hajiyar ta koma dan da yayi zaton ko a waya ta kirata. Yana Alwalar sallar Magriba ta shigo gidan ita kadai dan daman tun tafiyarsu Aikin Hajji ta yaye Bibi tana can gidansu ba'a dawo da ita ba kallon ta yayi ganin yanda take tafiya kamar wadda akawa dukan tsiya jikinta a mugun sanyaye daman kuma ya lura a kwanakin kafin ta bullo da wannan fitinar jikinta ya canza kullum cikin snayi take. Hada ido sukayi ta dauke kai gefe tana qunquni be kulata ba ya fice ransa na masa zafi haka yayiwo sallarsa har Isha kafin ya dawo gidan ya tarar da ita a palour tayi wanka ta zaka wata Red Rubber gown me spaghetti hand tabi jikinta ta lafe surarta babu abinda ya buya ta dora qafa daya kan daya tana taunar chewing gum.

Kallo daya yayi mata ya wuce dakinsa, dab da ze shiga ya tuna da batun zuwa gidan Yaya Aminun seya juyo ya kalleta fuska a daure yace
"Ki shirya yanzu zamuje gidan Yaya Aminu".

UMAIMAH
Wata muguwar faduwar gaba ce ta sameta sanda ya kira sunan Yaya Aminun take mafarkin da tayi dashi a daren jiya ya fado mata. Qirji ta dafe da hannu biyu tana cewa
"Me ya same shi?"
"Babu abinda ya same shi, qararki na kai gurinsa kuma yace kije yana nemanki koda magana ne?" Ya fada yana tsareta da ido, seta zumbura baki gaba tana wani banqaro Qirji a ranta tana cewa
"Ai wallahi ko gurin Abba zamuje ba tsoro zanji ba, tunda dai Hajiya na bayana duk kaje inda zakaje ai dai ita ta isa dai" daga haka ta moqe ta shiga dakinta har sannan kuma can qasan zuciyarta tana jin wani tsoro data rasa na menene.

Ta kwana biyu tana jin wannan rashin jin dadin dan har tunani take ko Abba ne ze mutu saboda yayi ciwo sosai lokacin suna Saudiyya kamar baxe tashi ba kafin Allah kawo masa sauqi kuma. Tana cikin shiryawa Mama ta kirata, ta dauki wayar cikin Mamaki dan da wuya Maman ta kirata idan bada wani abu ba sedai ita ta kirata toh ko har an kai qarar tata gidan ne?
Wayar ta daga yanda taji muryar Mama se taji hankalinta ya tashi cikin murya me cike da Rauni ta amsa gaisuwar da Umaiman take mata kafin tace
"Lafiya kike Umaimah ko akwai abinda yake damunki?"

"Lafiya ta qalau Mama wani abu aka ce miki ya sameni?" Umaimah ta bata amsa cikin mamakin abinda yasa Maman yi mata wannan tambayar, se Maman tace
"Toh Alhamdulillah tunda kina lafiya daman abinda na kira naji kenan Ya Mijin naki ina fatan dai babu wata damuwa ko?"

"Duk lafiya muke Mama, kodai kema kina jin yanda nake ji ne? gaba daya bana jij dadi ji nakeyi kamar zan rasa wani abu?" Umaimah ta fada muryarta na karyewa kamar zata fasa kuka se Mama tayi saurin tareta da cewa
"Aa babu abinda ze faru in sha Allahu kawai na kwana biyu ban kiraku bane shiyasa duk na kira yan uwanki Yayanku ne kadai ban samu ba na kirashi be daga ba amma nasan idanya gani ze biyo ni"

"Yanzu ma kuwa gidan sa zamu je da Abban Mu'ayyad" Umaimah ta fada
"Toh shikenan ku gaida shi idan kunje, Allah yayi muku Albarka gaba daya aci gaba da haquri dai" Maman ta fada daga nan suka yi sallama jinin Umaimah na qara tsinkewa. Kodai Mama ce zata mutu ta kira su suyi sallama? Se kawai taji Hawaye sun bin kumatunta. Khalil dake tsaye tun dazu yana kallonta yace

"Tashi muje dare yanayi" ya juya ya fita.
A mota suna shiga ta kalle shi har sannanda hawaye akan fuskarta tace
"Dan Allah mu fara zuwa gida naga Mama"
"Idan mun dawo se mu biya" ya bata amsa ba tareda ya kalleta ba. Tafiyar kurame sukayi har zuwa gidan Yaya Aminun, sun tarar dashi cikin shirin fita an kirashi operation emergency, wani target ne da suka dade suna bibiya suka samu information akan ya shigo gari hat anyi masa talala ana jira suje su kamashi abinda ya tashi fitar tasa babu shiri kenan.

Yana. Gyara Bulletproof jacket din daya saka ya kalli Umaimah dake kallonsa itama ta rasa abinda yake damunta dan ko gaishe shi kasayi tayi yace
"Wati Umaimah ba zaki dena halinki ba idan kinyi sanyi an dauka kin shiryu se ki dawo da sabon salon fitina ko? Yanzu idan baki taimaka masa ya rabu da mahaifiyarsa lafiya ba me yasa zaki zama silar samun sabani a tsakaninsu?

Toh karki bar abinda kikeyi kinji duniya ke rudarki kuma gaki gata nan kina kallo dai mutuwa akeyi, idan yau an kawo qararki gobe be zama lallai kina da wanda za'a kaiwa qararki ba ke zakiyiwa kanki fada ga yara nan kin fara tarawa a haka zasu tashi suga kin wannan shashancin su me za suyi kenan?
Kiji tsoron Allah ki bar mijinki ya huta yaji da damuwar waje idan ya dawo cikin gidansa ya samu nutsuwa".

Dukda ba wani fadan azo a gani yayi mata ba haka kawai takejin maganganunsa har cikin zuciyarta nan take ta ringa shatato hawaye kamar an kunna famfo. Kallon Khalil yayi yace
"Kai kuma a karo na qarshe da zan gaya maka ka tashi ka zama namiji a gidanka, kai ka bata kuma kai zaka tashi ka gyara daga yau karka sake kawo mun matsalar gidanka tunda dai ka zama solobiyo se ka zauna yarinya qarama ta ringa caza maka kai".
Chapter 129 · 0% Book details