← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 157 OF 267

Sashe 157

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khalil kuwa seda ya fita daga layinsu kafin ya samu guri ya tsayar da mota. Wayarsa ya dakko ya sake komawa WhatsApp din ya bude status dinta. Hoton ya tsurawa ido kamar wanda yake son goge Emoji din ya samu damar ganin fuskar wanda aka boye din har wani huci yakeyi saboda yanda zuciyarsa take tafasa kai kace Umaimah ce ta dora hoton wani Namiji bashi ba ta kirashi da haskenta. Kiran wayar Anwar ne ya katse masa kallon status din, suna gama magana ya tada motar yaci gaba da tafiya ita kanta motar tasan yau ran me ita a bace yake saboda yanda yake fizgarta kamar ze tashi sama.

Sama sama ya ringa amsawa masu gaishe shi, a office dinsa ya tarar da Anwar dake jiransa zasu fita ya jefar da jakarsa kan kujera Anwar ya bishi da kallo ganin yanda yake abubuwa kamar wanda yake fada da kayan office din.
"Khalil lafiya kuwa?" Anwar ya tambayeshi ganin yayi wurgi da Chajar wayarsa da yake qoqarin jonawa amma taqi hawa alhalin ba laifinta bane shine be kunna socket din ba yake ta danna chaji.

Tsaki yayi ya zauna akan kujera ba tareda ya amsa shi ba. Anwar yaja daya daga cikin kujerun gaban Table din shima ya zauna yana fuskantar sa, yasan matsalar sa daya ce bazata wuce Umaimah ba amma ya zata sunyi magana tun kwanaki kuma Khalil din da bakinsa yace baze sake bari lamarinta ya dameshi ba ballantana har ya shafi aikinsa yanzu kuma me tayi masa haka da ya zuciya yake qoqarin yiwa abubuwa rotse.

Gyaran murya Anwar yayi yana kallon Khalil da shi kuma yake kallon wayarsa, status din yake sake kallo dan ta qara wasu hotunan guda biyu, daya dai Hasken nata ne se na qarshe ita da Mama da Nusaiba matar Mansur a Harami da alama Umarar da Mama take da Mauludi tare suka tafi kenan.
"Khalil" ya kira sunansa, se ya dago daga kallon wayar ya dubi Anwar,
"Meya faru?"

Tsaki Khalil yayi kamar bazece komai ba se kuma cikin qufula yace
"Wata yarinya na siyawa waya saboda ta raina mun hankali yanzu kawai naga ta saka hoton wani gaja da caption wai Haskenta" ya fada muryarsa na nuna zallar takaicin da status din Humairan ya qunsa masa shi dai Anwar kasa riqe kansa yayi seda ya fashe da dariya harda kyakyatawa yana kwanciya akan Table dan maganar ba qaramin shiharsa tayi ba. Yanzu wannan fushin duk akan mace yakeyinsa lallai Khalil yayi nisa sedai fatan Allah ya taro shi.

Kallonsa Khalil ya ringayi har yayi dariyarsa ya gaji takaici kamar ya shaqoshi ganin irin kallon da yake binsa dashi ya saka Anwar dakatawa da dariyar yana cewa
"Allah ya baka haquri, maganar taka ce ai dole ta sakani dariya. Wai ka siyawa yarinya waya ta dora hoton wani a Status, kai dole ma na kai labarin nan NH yau gayu suji su dauki darasi" ya sake sheqewa da wata dariyar da tafi ta da abin haushi.

Tashi Khalil yayi ya shiga hada abubuwan da zasu fita dasu din ransa a bala'in bace kamar ya rufe Anwar da duka.
"To amma tsaya, Ina Umaimah da har aka siyawa wata waya kuma kake fushi dan ta saka wani a status? Kai bama wannan ba da alama mayyar data kama ka ta sakar maka kurwa kenan har ka iya yin budurwa ka siya mata waya lallai Khalil ka shahara wuyanka ya riqa ko ince Alqadarin Umaimah ya karye tunda gashi ka dena tsoronta kai tsaye kake abinka yanzu" Anwar daya tsaida dariyarsa dakyar ya sake fada. Shidai Khalil be kulashi ba ya gama tattara abinda yake da buqata ya fita Anwar dinya rufa masa baya. A mota ma haka ya tasashi da magana shidai yayi masa shiru dan abinda ke cin ransa ya ishe shi haka suka gama zagayen duba ayyukan da zasuyi ransa a dagule babu dadi.

A wani restaurant suka tsaya cin Abinci bayan sunyi Sallar Azahar. Anwar ya sake kallonsa ganin gaba daya ranar bashida walwala gashi bini bini ya dauki waya ya duba ya riga Khalil din cinye abincinsa dan haka ya jirashi ya gama, ganin sauran da suke tare basu qarasa ba ya saka shi amfani da damar ya kalli Khalil yace
"Mutumina kasan abu na farko da zan fara ce maka shine duk abinda zaka yi a rayuwa kayishi tsaka tsaki. Idan zaka so abu ka so shi daidai Misali haka idan zaka qi abu ka qishi saisa saisa saboda wata rana duka abu biyun nan suna iya rikida su koma akasin Asalinsu.

Kaga kai babbar Matsalar ka a rayuwa ita ce zurfafa Soyayya. A duk sanda kaso abu kana daukarsa ka bashi muhimmanci sama da kowa da komai a rayuwarka bana buqatar tunatar da kai Matarka kadai ta isheka isha idan haka ne zamantakewarku kadai ta isheka karatu akan duk wata mace da zaka sake mu'amalanta anan gaba. Duk abinda ya faru dakai Soyayyar ka tayi amfani da ita ta yaqe ka, nayi zaton ka koyi darasi se gashi yanzun ma kana qoqarin sake afkawa a ramin da yafi wanda ka baro Zurfi da duhu.

Ni nasan Wannan Mayyar da ka ringa iqirarin ta kamaka babu wata mayya se Maitar Soyayya, ka sake fadawa tarkon Love at first site din daka saba ne shine kazo kana mana wata Drama wai Wata Mayya ta kamaka ashe ban sani bama har abu yayi nisa kun daidaita harta kai ga ka siya mata waya. To nidai abunda zan iya gaya maka daya ne zuqa biyu, yanzu dai gashi da Idonka ka gani cewar ba kai kadai take kulawa ba kamar ma shi wancan yafika fawa a gurinta tunda da wayar daka siya akeyin status dashi ana kiransa da Haske kai ko Arziqin duhu baka samu ba. Ita Mace daka ganta a sanda kake nacinta kana nuna mata So da kulawa ba takai take ba,se kaga zuciyarta tana ga wanda be kaika ba, sedai ka qare a wahalta mata ita kuma tana Wahalta masa tunda shi take so".

Yanda kasan me daukar karatu haka yasa kunnuwa yana sauraron Anwar, fashin baqin da yayi masa yasa ya shiga tunanin kenan da gaske Son yarinyar yakeyi? Saurin qaryata hakan zuciyarsa tayi se kuma daya bangaren ya jefo masa tambayar
"Idan ba sonta kakeyi ba ina ruwanka da sabgarta har kake kishin ta saka hoton wani a status?"
"Tab da kuwa an fadi babu nauyi ace ina son wannan yar yarinyar da bata wuce na haifi Sa'arta ba" ya fada. Be ankara da cewar a fili yayi maganar ba seda yaji Anwar yace

"Ai babu wani aibu idan kaso qaramar yarinya abu daya ne dai A yanzu idan aure zakayi Khalil kamata yayi ka nemo matar da take sonka ba wacce kai kafi so ba, bani da buqatar gaya maka dalilin haka dan ka fini sani. Bance karka so koma wacece ka samo ba amma ka zauna kayiwa kanka Hisabi shin ta dace dakai? Zata share maka hawayen da kake fata ko kuwa? Idan ta gaza cin wadannan Test din ka haqura da ita ka nemi wata cikin manyan yammata da suka gogu da rayuwa kuma su suke sonka ba wai kai kake sonsu ba na tabbata se sunfi binka sun baka nutsuwar da kake nema sannan ka sani duk macen da zaka aura a yanzu dole ya zaman cewar tayiwa matarka zarra ta kowanne fanni shi kadai ne ze samar maka da zaman lafiya a cikin gidanka dan ka fini sanin da wadda kake zaune, amma idan da ita wannan din zuciyarka ta aminta, ka nemi zabin Allah ka bar masa komai a hannunsa duk kuma hukuncin daya yanke maka kar kayi Jayayya da hakan ka karbeshi da kyakykyawan Yaqini".

"Bafa tasan ina sonta ba, ni dakaina ban yarda cewa Sonta nakeyi ba. Haka kawai tun daga randa na fara ganinta na rasa nutsuwata. Yarinya cefa Qarama Anwar, she is just 18 me zan tsinta a jikinta kawai Shaidan ne yake nema yayi mun wasa da hankali amma ni ba wani abu game da ita a raina" Khalil ya fadawa Anwar din iyakar gaskiyarsa. Murmushi Anwar yayi yace
"Lokacin daka fara Son Badar haka kace soyayyar yan uwantaka ce, se gaka harda kwanciya a gadon Asibiti da tace ba zata aureka ba. Umaimah kuma Friendship ita kuma wannan Tausayinta kake ji halan tunda kace yarinya ce?"

"Exactly, tausayinta naji. I learnt that she is an orphan babu uwa babu uba, shine ma har yasa na siya mata wayan saboda tace bata dashi. Cousin din Mansur ce, a gidansu take. amma ni ba wani sonta nakeyi ba kawai haushin da naji akan me daga na siya mata waya zata ringa saka hoton wani saurayi bayan ni purposely saboda tayi karatu na siya mata" Khalil ya sake fada, se Anwar ya miqe yana murmushi yace
"Abokina ka nemi zabin Allah kawai kaji idan kaji ta kwanta maka daga nan ka nemi yardarta ka dage kuma da Addu'a Allah yasa qarshen wahalarka ne yazo".

Har ya koma gida maganganun Anwar nayi masa yawo a kai, sam baya so ya yarda da cewar wai Son Humaira yakeyi to ta Yaya ma? Amma kuma duk wasu Shika shikan soyayya sun gama bayyana a tare dashi. Wannan faduwar gaban da yawan tunaninta da yakeyi harya dora mata Maita ashe duk na kamuwa da Soyayya ne be sani ba amma kuwa idan haka ne So be kyauta masa ba daya rasa inda ze sauka se akan wannan yar tatsitsiyar yarinyar da Yasan kwakwkwarar tsawa idan Umaimah tayi mata zata iya suma. Kai bama wannan ba ya tabbatar babu yanda za'ayi Mansur ya yarda ya barshi ya aureta dan yace matarsa bata da hankali dukda shine babban zagin da kullum yake Addu'ar Allah yasa ayi mata kishiya to dai dara taci gida Addu'a ta karbu kuma akan Qanwarsa sedai fatan Allah ya taqiata dan idan har ze qara aure dagaske to babu wata Mace da ze aura idan ba Humairan ba, ita kadaice tayi masa irin shigar da Umaimah tayiwa zuciyarsa.
Chapter 157 · 0% Book details