← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 267

Sashe 20

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsaki taja tareda gyara kwanciya, tana so ta koma dakin ta bata haquri amma tasan muddin wancan zalimun na gidan ta kai kanta mahallaka ne gara ta bari se ya tafi, haka ta ringa juyi a gado hankalin ta sam yaqi kwanciya, yanzu fa idan Maman tana can tana ci gaba da kuka ai se tashin hankulan su mata yawa, ga abindatake ciki ga Hawayen uwa ita ina zata saka ranta?

Miqewa tayi ta bude qofar,gara taje idan ma kashe ta Aminu zeyi sedai yayi din amma seta je gurin Maman, tana zare sakatar kuwa ta jishi yana yiwa Anty sallama, dakatawa tayi har tajiyo qarar bude qofar fita kafin tayi wuf ta shige dakin Maman

Nuratu na durqushe gabanta tana ci gaba da bata baki bayan Aminu ya gama nasa ya tafi ta shiga, kallon banza suka aikawa juna kafin ta tattare fuska tana kallon Mama tace

"Yanzu Mama kawai dan anzo an gaya miki qarya da gaskiya shine zaki ringa zubda hawayenki a kaina bayan kinsan abinda hakan ze iya janyo mun? Duk fa qaryace kawai baqin ciki ake mun dan an ga na samu wanda nake so yake sona anga kwana biyu muna zamab lafiya dake babu wani abu shine ake so a hada mu"ta qarasa tana Harara Nuratu da ta dauke kai dan yanzu tayiwa Maman Alqawarin bazata sake biye mata suyi fada ba amma badan haka ba seta sake gurje bakin yarinyar nan ta nuna mata banbancin dake tsakaninsu.

"Idan daidai kikeyi Umaimah kin sani in ma akasin haka ne duka keta shafa, babu abinda yayi mun zafi da sabgarki duk yanda kika ga dama kiyi ba kuma zan sake bata raina akan abinda ya shafe ki ba in Allah ya yarda. Na kuma godewa Allah da ya saka bake kadai na haifa ba kinga idan kin sakani baqin ciki ina da wasunki da zasu sakani farin ciki dan haka kije kiyi duk yanda kimaga yayi miki rayuwarki ce ba tawa ba" tana gama fada ta miqe ta shige bandaki ta barta a tsaye dan daman tuni Nuratu ta fice itama daga dakin.

Jiki a sanyaye ta koma dakinsu, kan gadonta ta kwanta tana tunani. ita da kanta ta san tana jawo mutane da yawa ciwon kai amma ya zatayi haka Allah ya halicce ta bata da ikon canza kanta (kodai kika mayar da kanki ba). Wayarta ta janyo ta shiga neman layin Khalil, badai duk akan auransa ne Mama take wadannan maganganun ba bari ta kirashi, da dai tayi alqawarin se tayi sati bata amsa wayar sa ba idan ma yazo gida bazata fita ba amma yanzu saboda farin cikin Mama da kanta zata kira shi ta bashi haquri, ita azo kawai ma ayi abinda za'yi idan ta kama wannan Juma'ar ma a daura musu aure kawai idan yaso duk randa aka a
Shirya ayi bikin shikenan dai ta wuce gorin Mama da tsoron ko wanne lokaci ana iya fasa auran ta.

Tana can tunani wayar dake ta faman ringin ta katse, sake kira tayi nan ma baa dauka ba seda ta jera masa kira goma amma ko daya be daga ba na qarshe ma rejecting yayi kafin aka kashe wayar ma gaba dayanta kamar yanda Computer ta sanar mata sanda ta sake kira

Tayi sororo da waya a hannu tana kallo, tunda take dashi bata zaton ta taba masa kira biyu, duk sanda ta kirashi kome yake ze dakata ya kirata dan baya dagawa sedai ya kashe ya kira, ba qaramin abu yakeyi ba da ze saka ya kasa daga wayarta.
Idan ma yana da wani uzuri me muhimmanci tun kafin lokacin yana sanar mata dan kar ta kira bata same shi ba amma shine yau tayi masa missedcalls 10 be daga ba bayan tasab babu abinda yakeyi yana Asibiti gurin Hajiya ko ya tafi gida ya huta.

'Qila ma yana can tare da wannan Jamilar har yana jinhaushi dan an tabata wai yar uba amma sun wani daukaketa kamar ciki daya suka fito' ta raya a zuciyarta, a fili taja tsaki dan ita abinda yasa ta qara tsanarta kenan kasancewar ta ba ciki daya suka fito dasu Khalil din ba. Haka kawai ta bata musu lissafi su kuma sun wani jata a jiki kamar uwarsu daya gaba daya ita kam bata ga dan uban da zata hada kai dashi ba, dan Kishiya ne fa.

'Idan kuma da gaske Nuratu take da tace Khalil din yace ya fasa auranta fa dalilin daya saka yaqi daukar wayarta har yayi rejecting tareda kashe waya gaba daya?' Zuciyarta ta sake raya mata, seta miqe zaune babu shiri ta dafe qirji, Khalil ya fasa auranta tabi ina taga haske Jama'a???

PROMO
PROMO
PROMO

BEFORE 4K NOW 2500

3968303018
ZAINAB SHU AIBU
FCMB
KITURA SHEDAR BIYA 👇🏻

08162859027

AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA

INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK DATTIN MARA CIWON MARA CIWON JIKI HANA HAIHUWA RASHIN NI IMA RASHIN JIN SHA AWA FITAR FARIN RUWA KAIKAYI KURAJEN PP DA NA JIKI JIN ZAFI YAYIN SADUWA FITAR FARIN RUWA MAI WARI BASUR KOMAI DADEWARSHI CIWON NONO

SHIRYE NAKE ZANYI MAKU PROMO SABODA WA ANDA BASU SHA BA SU ZO SU DA DANA MAGANIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID DUK LABARIN DA AKE BAKU GASKENA MAGANINA KANKAT NE KOBAKISHA KOMAI BA YA ISHEKI

*DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK*

*(UMMU-MAHEER)*

*MARUBUCIYAR*

*WATA KISHIYAR🥰👹 (ALKHAIRI CE KO SHARRI)*

*RUBUTACCIYAR QADDARAH AND NOW*

*HALIN KISHI*

*HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE NAIRA 500*

*GA DUK ME SO ZE TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*

*MARYAM UMAR FAROUK*

*SE A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*

Free page 10
Last free page

Tun Umaimah na daukar abin wasa har ta fara shiga rudanin rashin sanin abinda Khalil yake nufi da qin daga kiranta. Raba dare tayi tana kiran wayarsa, ya kunna amma haka zata qaraci qara ta tsinke ba tareda an daga ba, ta tura masa da SMS sunfi nawa shima babu amsa, WhatsApp kuwa idan ta tura saqon ma baya tafiya tsabar rudanin da ta shiga bata san ashe Datar ce bata kunna ba.

Kafin safiya idanunta sunyi zuru zuru kamar wadda ta kwana tana zawo saboda rashin bacci da damuwar data kwana a ciki. Tana idar da sallar Asuba ta sake gwada kiran layin, call waiting aka gaya mata. Qirjinta ya buga Dam har seda ta saka hannu biyu ta dafe wayar ta subuce daga hannunta.

Tun haduwar sa dashi a irin wannna lokacin tasan da ita kadai yake waya, ze kirata idan ya tashi sannan idan ya dawo daga masallaci ze sake kiranta zuwa gari yayi haske kafin suyi sallama toh dawa yake magana yanzu? Ta tambayi kanta.

Wayar ta dakko ta sake danna kiran layinsa, still yana waya cikin sa'a ringing biyu taji ya daga da sallama, seda ta saki wata ajiyiyar zuciya kafin cikin karyewar zuciya ta kira sunansa tace
"Khalil, me nayi maka? meyasa kaqi daga wayata tun jiya daga baya ma ka kashe wayar gaba daya?"

"Am kinga Umaimah ina wani important call ne yanzu kiran da kike tayi yana diverting attention nawa shiyasa na daga ki bari idan na gama zan kiraki" Khalil ya fada daga daya bangaren kafin ta sake cewa wani abu ya datse kiran se kawai ta cire wayar daga kunnenta ta bita da ido kamar zata ganshi a ciki, ita yau Khalil ya kashewa waya.

Tagumi tayi hannu bibbiyu gaba daya kwakwalwarta ta cunkushe ta kasa samun damar yin wani tunani, me tayi masa da ze dauki zafi haka? Ita dai a saninta indai akan abinda ya faru jiya ne beci ace yayi fushi me yawa har haka ba indai ba kuma daman yana neman hanyar da ze wulaqantata bane tuntuni amma meye abin daukar zafi anan.

Bata san tsahon lokacin data dauka tana tufka da warwara ba seda ta jiyo muryar Mama daga tsakar gida tana kwala mata kira tayi firgigit ta miqe ta fita. Kallo daya Maman tayi mata bayan data amsa gaisuwarta ta nuna mata inda kwanukan wanke wanke suke tace

"Ga wanke wanke da shara nan, ki dama kunu kafin a kawo markaden qosai, da wuri Abban ku ze fita sannan za'a kai gidan rasuwar can" tana gama fada ta juya abinta ta bar Umaimah a tsaye kamar wadda aka dasa.

Wanke wanke, shara, suyar qosai duk ita kadai? A cire shara da suyar qosan ma dai a duniya abun data tsana yabi bayan wanke wanke kuma kowa yasan da wannan musamman irin na gidansu da yake da mugun yawa kamar kwanukan gidan biki.

Ta waiwaya ta kalli kamfacecen tsakar gidan nasu dayayi kaca kaca da ganyayyakin bishiya da qasa saboda iskar da akayi cikin dare jiya wannan kafin ma ta gama ai bayanta ya karye wai ma ina su Nazifi da Arma da suke aikace aikacen tsakar gidan shine za'a ce ita zatayi yau? Yaushe rabon ma da a raba aikin gidan da ita tunda ta shiga Higher institution dan idan ma an sakata ba zatayi a dadin rai ba daga qarshe ma aka dena cewa tayin sedai idan yan hankalin suna kanta taga Maman na aiki ta karba ta qarasa shine yau za'a dawo da abinda ya wuce.

"Au kina tsaye tun dazu ko babu abinda kikayi? Ai shikenan ki bari Alhajin ya fito baki hada abin karyawa ba zakiyi bayani" Mama data sake fitowa cikin shirin fita ta fada tana kallonta.
Tsintsiya ta dauko ta fara sharar kamar mara laka a jiki ba tareda ta tankawa Maman ba daidai lokacin Anty Saratu ta fito daga dakinta suka gaisa da Maman ta juya tana kallon Umaimah tace

"Aa, Umaimah ce da shara yau kuma ina su Arman tun dazu fa naji motsin shigowarsu, nima yau baccine yafi qarfina wallahi se yanzu na samu na miqe"

"Na basu markaden qosai sukai, bari naje Yusuf na jirana a waje Rabi'a aka kai Asibiti haihuwa yanzu Yaya ta kira take gayamun babu kowa a wajenta" (Rabi'a yar yayarta ce da suke uba daya).
Chapter 20 · 0% Book details