← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 186 OF 267

Sashe 186

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bude ido yayi yana kallonta yace
"Dan Allah fa? Kinsan ni ban taba zuwa Taraba ba nadai je Yola shima a jirgi so ban san nisan tafiyar ba"
"Aiko da nisa ga hanya bashi da kyau shine ma abinda yake qarawa tafiyar nisa" ta bashi amsa. Se ya bude motar ya shiga, Carton din Madarar waken suya ta kwalba daya tsaya ya siya a hanya ya miqa mata yana cewa
"Gashi, kwanaki naga Anwar ya siyawa Matarsa wai yana saka qiba ki gwada sha mu gani ko ze karbeki kinsan Matata qatuwa ce kar kuzo dakuwa tafi qarfinki".

Kallonsa ta tsayayi se kuma ta zumburi baki ta harareshi qasa qasa tace
"Allah ya sauwaqe nayi dambe da Kishiya"
"Me kika ce?" Ya fada yana kallonta seta dauki Carton din ba tareda ta bashi amsa ba ta wuce seda taje Get ta waiwayo ta murguda masa baki irin yanda yara sukeyi tace
"Da zakace matarka qatuwa zata dakeni ai abun ba a qarfin jiki bane kuma ai a qauye ne ake kishin hauka ana doke doke" tayi saurin shigewa ciki Khalil daya saki baki yana kallonta yace
"Ikon Allah" lallai ya yarda da Jamila da tace ba'a raina mace komai qanqantarta gashi kuwa ya gani, in har zata iya maida masa da Magana to Umaiman me?

Tashin motar yayi ya wuce, yanda yake jin qafarsa dole ya wuce Asibiti tun kafin ya isa ya kira Dr Al'amin likitan da Umaimah take gani a yanda ya fada masa yayi sa'a Physiotherapists dinsu is on Sit dan haka zeyi masa booking kafin ya qaraso. Sanda yaje be jima ba ya samu ganin likitan, bayan duk bincike da tambayoyin daya kamata yayi masa akan musabbabin ciwon qafar tasa ya rubuta masa magani nasha dana shafawa da zasu rage masa Ciwon qafar sannan ya gaya masa ya daure dukda yanda yakeji ya ringa motsa qafafun kafin ya bashi X-ray dan su duba da kyau suga ko wata matsala ce ta ciki dukda Khalil din ya tabbatar masa da wayonsa be taba faduwa ko wata buguwa da zata janyo ciwon ya tasar masa yanzu ba kamar yanda Likitan yake tunani. Seda ya koma gurin Dr Al'amin ya gaya masa yanda sukayi ya karbi takaddar X-ray din yace masa ya dawo da safe sannan yayi masa fatan samun lafiya.

Har Khalil ya kai bakin qofa Dr Al'amin ya tsayar dashi yana cewa
"Yauwa kaga na sha'afa, Madam bata zo Antinatal ba jiya ina taso na kiraka wlh aiki ya dauke mun hankali. Daman tun last week na gaya mata ban sani ba ko kunyi maganae idan har ta wuce satinnan bata haihu ba to gaskiya sedai Muyi mata CS kawai a cire abinda yake cikinta dan tun farko data bamu hadinkai ma da yanzu anyi amma ta nuna bata so ita amma kai ina so ka fahimci halin da take ciki da complications din da cikin nan ya samu CS din is the best option dan haka ka lallasheta, if possible within the weekend kuzo kawai a cire Babyn".

Ajiyar zuciya Khalil dake sauraronsa yayi kafin ya tabbatar masa idan ya koma zeyi magana da ita duk kuma yanda sukayi ze kira Dr a waya ya gaya masa, suka sakeyin Musabaha ya fita yana tafiya a hankali saboda duk in ya motsa qafar shi kadai yasan abinda yakeji. Dakyar ya iya kai kansa gida saboda mommotsa qafar da akayi tamkar an qaro masa ciwon da takeyi ne, seda ya dafa Khalifa sannan suka iya shiga gida. Saboda yanda yake be iya hawa Sama ba anan falon qasa yace ya ajiye shi kafin ta lafa masa se ya hau saman, Khalifa ya ringa kallonsa da tausayawa se yake tuna Lokacin da Mahaifinsu ya ringa fama da qafa dukda yana qarami a sannan amma be manta ba kamar haka wata rana idan ta tasar masa sedai Khalil din da Me Gadinsu su kama shi su shigo dashi cikin gida gashi yanzu Yah Khalil ma yayi Gado.

Shi yaje ya gayawa Hajiya a yanda Khalil din yake, yana zaune kan carpet bayan ya samu dakyar yayi alwala a bandakin dake falon yayi sallar Magriba data riskeshi a hanya a zaune yana Azkar Hajiyar ta shiga da sallama ta zauna kan kujerar da yake jingine tanacewa
"Babana qafar ce yanzu Khalifa yake gaya mun se shi ya kamak kuka shigo kaje Asibitin kuwa daka fita"
"Naje Hajiya sun bani magani na sha dana shafawa sannan gobe zan koma ayi hoto" ya bata amsa yana nuna mata ledar magungunan dake kusa da ita. Miqewa tayi ta Kashe Ac da aka kunna a Falon ta sama data qasa ta sake zama tana cewa
"Ko wannan uban sanyin da kuke babalawa kanku ya isa ya sakar maka da ciwon qafa ai, ina Matar gidan da zata samu ruwan Zafi ta dan gargasa maka qafar ka shafa maganin in Allah ya yarda zatayi sauqi kafin goben tayi ayi hoton ko?"

"Ciwon ma ya lafa Hajiya yanzu zan tashi naje nayi wanka sena gasa da kaina" ya bata amsa yana yunqurawa cike da qarfin Hali dan ji yake kamar an qara dora masa duwatsu an danne qafar. Hajiya ta miqe tana cewa
"Zaka iya hawa bene kuwa Ka shiga can dakin ba nan Umaiman itama take yanzu ba?"
"Babu komai Hajiya zan iya kuma likita yace karna zauna na ringa motsa qafar sosai, bari nayi wankan kafin a kira Sallah zan shigo idan na dawo daga Masallaci"

"Shikenan Allah ya qara afuwa je kayi wankan" cewar Hajiya, Khalil ya fara takawa cikin qarfin hali amma kana kallonsa kasan yana jinjiki, ya fara hawa stairs din kenan aka bude qofar falo shida Hajiya dake tsaye har sannan tana jiran ya haye saman suka kalli me shigowar, Umaimah ce ta shigo da qaramar sallama ganin Hajiya tsaye yasa ta danyi turus se kuma ta kalli Khalo daya tsaya shima yana kallonta.
"Ashe bakya nan, to wannan jikin naki ma keda shi din ai duk masu neman taimako ne da se nace kije ki kamashi ya hau saman amma bari na turo masa Khalifa" tana gama fadar haka ta rabe Umaimah dake tsaye tana kallon Khalil ta fita.

Ajiyar zuciya Umaiman ta sauke a sanyaye tana ci gaba da kallonsa ganinya juta yaci gaba da qoqarin daga qafar yana hawa saman Khalifa ya shigo ya qarasa da sauri ya kamashi da yake shima jikin nasa irin na Khalil ne kusan daga shi ya ringayi se gashi ya haye dashi saman seda ya rakashi har bakin qofar bandakinsa ya shiga ze fita Khalil din yace ya jirashi ya nemi kan kujerar dake dakin ya zauna zuciyarsa fal cike da tausayin yayan nasa.

Umaimah kuwa gaba daya jikinta ne yayi sanyi yanda taga Khalil din na tafiya ya bala'in taba zuciyarta yanzu fa ita ce sila me yasa ba tayi tunani ba ta aikata yanzu idan ya rasa qafarsa gaba daya fa ya zatayi?
Dakinta ta wuce ta kullo qofa da muqulli, watsar da jakarta tayi dake cike da tarkacen abubuwandata karbo a gidan wani sabon Malami da Safinan ta sake kaita yau, a cewarta gara ayiwa aikin rubdugu dan a samu biyan buqata da gaggawa. Wayarta ta dauka ta shiga kiran Safinan, tana dagawa tace
"Safina na shiga uku karfa Malamin na ya gurgunta mun Miji kinga yanda Khalil ya koma kuwa a dare daya sefa an kama shi yake iya tafiya"

Tsaki Safina tayi tace
"Ban taba ganin mutum me garaje a duniya ba irinki Umaimah tukunna ma bake kika ce ayi masa abinda ze saka ya fasa tafiyar da yayi niyya ba? Da kinsan ma da zeyi tafiyar ne ba Malam din ne ya gano miki ba kuma dazu kike tabbatar mun da bayan kin koma jiya ya gaya miki da bakinsa zeyi tafiyar meye to abin tayar da hankali a ciki? Malam ya gaya miki aikin ko ba'a karya baqar qarinsa kwana uku ze karye da kansa amma in so kike ya dakatar bari na turo Miki lambarsa kawai ki kirashi da kanko kawai ki gaya masa dukka ayyukan ma da yayi miki ya karya kowa ya huta na gaji da shegun qorafinki da basa qarewa".

"Ba haka bane Safina wlh dan baki ganshi bane daman tunda aka fara ayyukan nan wlh ya fita a hayyacinsa sam bashi da nutsuwa kamar ba Khalil dina ba nifa gaskiya indai haka za'a ci gaba to gara a bari dan ba so nake Mijina ya zauce ba ana zaune lafiya ni aure nace a hanashi yi amma gaba daya ya samu se damalmala masa rayuwa yakeyi" Umaiman ta sake fada se Safina taja tsakin da yafi na farko tace
"Kanki ake ji, in kinga dama ki aikata saqonnin da muka karbo yanzu in kuma baki gani ba ki bari, sannan wannan na Gasashshen naman na gaya miki kiyi dan nayi jiya kuma naga Aikinsa amma in kinga har yanzu zuciyarki na kokonto to ki saki ki dauki qaddara kawai ki zauna da kishiya"

"Allah ya isa tsakanina dake kuma kishiya sedai ki ganta a gidanki banza muguwa kawai" Umaiman ta fada kafinta kashe wayarta ranta ya harzuqa da maganar Safinan ta qarshe. Idan zuciyarta ta karaya taga rashin kyautawa akan abinda takeyi seta tuna da cewar Khalil din shi ya jawa kansa koma menene daya ce zeyi mata kishiya.
Wanka ta shiga har sannan jikinta a sanyaye da yanayin Khalil din tana fitowa tayi sallah, kitchen ta wuce ta cire Kaza da tun da safe ta saka Ruqayya tayi mata Marinating dinta kafin ta tafi gida wai Mamanta aka kira akan bata da lafiya.
Chapter 186 · 0% Book details