← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 253 OF 267

Sashe 253

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sallar Azahar kawai tayi ta karbi aikin Abincin da Anty ta fara tana cewa ta barshi ita data kwaso gajiyar makaranta amma ta dage setayi. Seda ta sauke na dare tayi wanka taci abinci kafinta zauna bitar karatun da akayi musun. Ranar da wuri ta kwanta tunda tasan yanzu hidima ta qarun mata akwai zuwa makaranta a haka lokaci yaci gaba da tafiya harta share sati biyu a makarantar kuma Alhamdulillahi tanajin dadin karatun sosai har sannan kuma babu wanda ya taba ganin fuskarta a ajin, tsakaninta da kowa sallama ce bata magana dan ko Malama Aisha da suke zama benci daya gajiya tayi da janta da zance ta haqura, idan ba Umaiman ce ta tambayeta abu ba itama seta kama kanta. Tana jin yan ajin na gulmar wai tacika girman kai bata kula kowa. Zance har sauran Ajujuwa cewar an kawo wata sabuwar Daliba kullum fuska a rufe kuma bata magana da kowa. Ita dai ba abunda ya shafeta dasu musamman data godewa Allah babu yan unguwarsu da yawa a Bangaren Safen nasu, yara ta yamma sukeyi saurab Matan unguwar kuwa yawanci ta Asabar da Lahadi suke irin tasu Mama.

Wannan Matar data ga ta shiga gidansu Maman Nana mabata sake ganinta ba tun zuwan farko, a bakin Malama Aisha taji cewar Bari tayi bata da lafiya shiyasa bata zuwa dan har yan Ajin sunyi qungiya anje dubata da tace mata ko zataje tace Aa kawai se daga baya ta sake jin maganar a bakin Anty ashe Amaryarsu ce, da yake itama Maman Nanan sun babe tuni tun farkon dawowarta gida ita ta ringa qarawa wutar gulmarta fetur a unguwa har tana fadar ita bata taba dauka ma airan Umaiman ze jima har haka ba'a sakota ba saboda halinta, ta ringa cewa yarinyar da take da fuska biyi, a gidanta take zuwa tayi shigar banzarta idan zata fita yawon barbada inta dawo taje can ta canza labari yayita yawo a unguwa data san Umaiman taji tun daga nan ta dena shiga gidansu kwata kwata ta dauke qafarta shiyasa ma Umaimah bata san an cika she mata kishiya ta uku ba kenan sun zama su hudu.

Anty ta aiki Firdausi takaiwa Maman Nana wata Riga ta gyara mata Zip, Maman Nana na chanza zip din ta shiga tambayar Yarinyar wai Umaimah tana nan kuwa tace mata eh, Samira Amaryar su na daga qofar Kitchen tana duba girkin data dora, sunan Umaiman ya tuna mata da sabuwar yar Ajinsu, bata taba jin sunan ba se a kanta ranar se yanzu da taji Maman Nana ta ambata. cike da son Gulma bayan Firdausin ta fita ta matsa gurin Keken Maman Nana dukda ba shiri suke ba take ce mata

"Niko sunan da nJi kin fada kamar na santa"
Maman Nana ta galla mata harara dan tafi jin zafinta duk cikin kishiyoyin da aka mata. Seda yaga mamorarta ta kusa qarewa yaje ya dauko musu yarinya me shegen kadifiri Sa'ar Nanarta rana daya ya aurar da Nanan ya qaro Amarya shi kuma gashi yanda yake lelenta baya ko jin kunyar idonsu itama ta samu guri tayita zuba musu iskanci a gida shiyasa basa zama inuwa daya. Tsaki Maman Nanan tayi tace
"Kika santa a ina? Matar da tun kan ki isa aure take kulle a gida babu inda take zuwa".
Samirah tayi murmushi tace
"Wlh Maman Nana, wannan data fita ba yar gidan Saratun Alhaji Sabo bace? To itama waccen haka naji sunanta Umaimah Sabo, ajin mu daya a Islamiyya wata doguwa siririya ko zuwana na qarshe tare muka jero kuma gidan naga ta shiga har na ringa tunanin ko Amarya aka musu saboda nasan Yammata biyu ne a gidan ko?"

Maman Nana ta aje Almakashi saboda jin gulma harda gyara zama tana cewa
"Doguwa Siririya? Kai Umaimah ba siririya bace amma qila rama tayi dan na fi shekara uku banganta ba tun ina shiga gidan amma bari na tambayo Nafisa dan ko shekaran jiya ta shiga ta karbo Atamfofi gurin babarsu" ta miqe jiki na rawa ta shige dakin ta biyun su, bata jima ba ta fito tana tafa hannu tace
"Aiko itace, dan Nafisa tace data shiga ta ganta da Hijabin makaranta ta dawo ikom Allah an gama kulletan kenan ta fara fita? Yo ko ta fita ko karta fita dai tambari ta rigada tayiwa kanta wlh, Allah dai ya wadaran dai naka ya lalace".

Samira ta sauke tunkunya ta dawo tana cewa
"Me tayi da ake boyeta? Badai wani ta kashe ba? Dani daman yanda take ta fama da Hijabi nata yafi na kowa tsaho kofa qafarta ba'a gani ga Niqab har aka tashi bata daga shi ba har wani Malami seda ya mata magana duk a wani darare take ina lura da ita kamar mara gaskiya ashe da walakin dan Allah wata kashe Maman Nana?"

"Mijinta ta kashe mana" Maman Nana ta fada, Samira ta saki Ludayin miya ta dafe qirji, Haulatu ta ukunsu dake daki tayi saurin fitowa jin abinda Maman Nanan ta fada tace
"Ke Maman Nana kiji tsoron Allah ta kashe Mijinta a ina?"
"Yo abinda ta masa menene marabarsa da kisa Haulatu? Ta kashe masa kayan aiki meyayi saura bari fa kiji" ta juya kan Samira ta shiga labarta mata qarya da gaskiyar yanda akayi. Samira ta ringa tsuma jikinta na rawa, Allah Allah take litinin tayi taje makarantar da ta kusa wata bataje ba tunda tayi Bari ta fake dashi taqi komawa dan daman Mijin ne ya sakata dole ba so take ba musamman da sauran ta Asabar da Lahadi suke zuwa ita kuma cikin sati.

Watanta daya Umaimah tana zuwa Islamiyya cikin lumana Kishiyar Maman Nana na komawa labari ya canza dan randa ta koma a ranar ta bajewa yan Ajinsu labarin wacece Umaimah wanda ta tattaro daga bakin Kishiyoyta.
Daga yanayin kallon da yan Ajin suka ringa mata daya banbanta dana kullum tasha Jinin jikinta, ta zauna a sit dinsu Aisha bata zo ba danta bashida lafiya haka ta gama darasin ranar a takure tana yin yanda maganganu suke tashi qasa qasa gaba daya seta tsargu dukda babu wanda ya kira sunanta ko ya saka da ita amma ta kasa nutsuwa. A haka ta rarrafa aka tashi ta kama hanyar gida tunda abokiyar tafiyar tata bata zo ba.

Washe gari kuwa ba iya kar yan Ajinsu kadai ta ga suna binta da kallon qurillah ba harda sauran mutante, abin yayi gaba, gani kawai ta ringayi ana shigowa Ajin kamar wani gidan Zoo duk kuma wadda ta shigo saitinta zata kalla ta kama baki ta juya. Wani rukuni da suka shigo a qarshe kafin Malamin da zone musu darashi ya shiga har kanta suka qarasa, wata daga ciki datafi kowa zaqewa taja tsaki tana cewa
"Ai dole mutum ya ringa saka Niqab yana rufe fuska tunda bashi da gaskiya, to se kuyi hankali kudai yan Aji kar abinya motsa ayi muku aika aika a cuceku kun san da tsofaffin yan daba aAjin" ta sake jan tsaki wadanda suke ta qananan maganganu a Ajin suka fashe da dariya. Suka hada ido da Matar gidansu Maman Nana take gabanta ya fadi saboda irin murmushin da tayi mata ta tabbatar da cewar ita ta kawo gulmarta da har tasa ta zama abin kallo kenan.

Ranar bata iya fahimtar abinda aka koya musu ba, Allah Allah tayi a tashi ta tafi gida, sun fito a hanya wasu Mata uku yan Ajinsu suka tareta. Kai tsaye daya ta kama Niqab din fuskarta ta fizge Daya daga ciki tace
"Ke kuwa Barira ya haka? Ya zaki cire mata abu haka kawai?"
"So nake naga fuskar munafuka, nifa tunda na fara ganin matar nan daman jikina ya bani Bata da gaskiya ashe kuwa qasurgumar yar Ta'addace tayi badda kama take rufe fuska to Asirinki ya tonu kaf makarantar nan babu wanda be san aika aikar da kikayi ba kika saukewa Mijinki kayan aiki tir da halin ki wlh" wadda aka kora da Barira ta fada har tana tofar da yawu qasa. Dake cikin hargagi take maganar se gashi hankalin masu wucewa yakai kansu suka fara tsayawa ana tambayar meya faru take kuwa suka shigar fadar abinda suka sani akan Umaiman.

Mata suka zagayeta, wadanda suka santa suka shiga Mamakin jin itace dan da yawa dauka sukayi ko garin ta bari tsahon lokaci tubda ta denaZobo babu Wanda ya san ya take ciki. Abin mata,a maimakon su tsawatar da tozarcin da ake shirin yi mata se suka hadu sukayi mata caaa da yawa so suke suga fuskarta tunda sunji labarin so suke suga idanunta kawai yanzu. Umaimah ta riqe Niqab dinda qamqam tana durqushe a qasa saboda yanda takeji kukan ma ya kasa zuwar mata. Zuwan Malam Najib Malamin Ajinsu ya ceceta, shi ya watsa taron dandazon Matan yace ta tashi se sannan hawaye ya balle mata ta shiga kuka tamkar ranta ze fita ba kuma taga laifin kowa ba sai kanta ita tayi abinda ya janyo har aka tireta haka.

Haka ta koma gida tana kuka kamar me, Mama bata bi takanta ba Anty ce ta ringa lallashinta da tambayar meya faru amma ta kasa ce mata komai. Washe gari bata tashi da niyyar fita makaranta ba amma Mama tace babu fashi setaje. Ta fasa mata kuka amma tayi mirsisi.
"Duk abinda kika gani kekika jawa kanki dan haka seki nemi jarumtar tarar kome zaki gani" Maman ta fada mata tayi ficewarta daga dakin haka ta shirya ba yanda ta iya ta tafi, a Ajin ranar ma seda suka sake tireta suka ringa jifanta da maganganu marasa dadi ta kwantar da kanta a Desk har sukaci suka cinye bata tankawa kowa ba. Kamar yanda Mama ta fada ita ta jawa kanta dole ta nemi qarfin guiwar tarar abinda ze sameta. Haka ta ringa rayuwa a makarantar cikin tsangwama da takurar dalibai, duk kashedin da shugaban makaranta yayi akan abinda aka matan basuji ba danhar suspending Barira da qawayenta akayi amma hakan besa Matan makarantar sun sarara mata ba. Kadan ne suke tausayinta irinsu Malam Aisha da ta tsaya ta zama bakin Umaiman, duk wadda ta fada mata maganar banza ita take maida musu da yake me bakice kuma ta iya tijara se gashi tayi maganin da yawa saga ciki musamman yan Ajin da suka addabi rayuwar Umaiman.
Chapter 253 · 0% Book details