← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 259 OF 267

Sashe 259

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hankalin Khadija ya tashi matuqa dan ita irin mutanen nan ce da basa son damuwa, tun a daren taso Mijin nata ya saurareta amma yaqi, gashi yanzun ma yayi tafiyarsa har yana cewa yasan komai. Bata yarda da wannan ba dan a sanin da ta masa ko a social media ya jiyo labarin irin mata masu bala'in kishin nan sunyi abu ya ringa jimami kenan yana cewa ai babu dole a auransu baze dakko matar da zata zamar masa fitina kota lahantashi ba ta tabbatar yanda yake jida Injinsa idan yaji ta lahanta na wani babu abinda ze saka ya yarda ya aureta. Tunanin wanda zata gayawa maganar nan ya fahimceta ta shigayi qarshe ta yanke shawarar zuwa gidan Yayarsa ta gaya mata, ita ba ta kanta take ba Jihadi zatayo ta tabbata ko masifar ta tashi sakkowa kansa zata fara ruftawa kafin ita tunda shi ya kwasota can zata kashe shi a Abuja ta cuceta ta barta da marayun Yaya.

Abdulwahab din na fita itama tayi wanka ta tafi gidan Yaya Suwaiba babbar Yayarsu Abdul din. Tana kuka ta gama zayyana mata komai dataji, Yaya Suwaiba tayi shiru tana jinta seda ta kai qarshe kafin ta sauke ajiyar zuciya tace
"Yanzu ke Khadija ina kika jiyo wannan maganar kuma kin tabbatar da sahihancinta?"
"A gurin Yaya Ummi, ta santa tare sukayi makaranta kuma shima dana fada masa cewa yayi yasan komai kuma a hakan ze aureta" Khadijan ta sake fada tana share hawaye se Yaya Suwaiba ta gyara zama tace

"Toh nidai abinda zan fara ce miki shine kiyi haquri ki kuma bi komai a sannu. Kinsan namiji idan zeyi aure bayaji baya gani ke kuma duk abinda zaki fada yanzu za'a dauke shi a matsayin kishi kawai kuma tunda kince yasan komai kenan ba'a rufeshi ba kuma a hakan yaji ya gani ze aureta ke meye naki a ciki to tunda ma ba gari daya zaku zauna ba duk abinta ai iyakar kansa can zata tsaya ko?"

"Wlh Aa Yaya Suwaiba dan bakiji labarinta bane shiyasa kike fadar haka. Ni ba kishi nakeyi ba hasalima da yardata ze qara aure amma ni ita wannan dince kawai bana so ya nemo wata ya aura amma banda ita" Khadija ta fada tana kuka, rarrashinta Yaya Suwaiban tayi tareda yi mata alqawarin zata kira Abdulwahab tayi masa magana sannan tace mata itama tayi haquri taci gaba da addu'a idan da Alkhairi a abin Allah ya zaunar dasu lafiya in anyi idan kuma babu Allah ya watsa al'amarin salin alin ba tareda bacin rai ba. Haka ta koma gida hankalinta ya gaza kwanciya. Harga Allah ita auransa be dameta ba wadda ze auro matan ce tashin hankalinta dan ta tsorata da labarin Umaimah dataji ita bata son damuwa a rayuwarta tana zaune lafiya baza'a dakko mata wadda zata tayar mata da hankali ba.

Yaya Suwaiba kuwa kamar yanda ta mata alqawari ta kira qaninta ta gaya masa yanda sukayi da Khadijan, kai tsaye yace mata
"Yaya ki rabu da ita bafa ita zata zauna mun da mata ba bare ta zabar mun wadda zan aura. Kawai halinku ne Mata da daman bakwa rasa qirqiro tashin hankali da zarar ance za'a kawo muku wata cikin gida na tabbatar ko ba Umaimah ba duk wadda ma na ce zan aura seta san abinda zata bullo dashi dan na fasa to plan dinta beyi aiki ba dan kafin tasan wacece Umaiman na rigata sani aure kuma babu fashi dan yanzu haka ma nasan su kawu na hanyar dawowa gida dan tun dazu sukaje kai sadaki" Yaya Suwaiba ta rasa abin ce masa, ta wani fannin yana da gaskiya ko Khadija bata fito ta nuna ba kowa yasan dole tana kishin Mijinta kuma zata iya riqar duk hujjar data samu dan ta kauda maganar auran amma kuma itama zancenta abin dubawa ne a irin yanda tace ta jiyo labarin Amaryar da abinda ya kashe mata aure to amma tunda ma'auri yaji ya gani su meye nasu ciki banda suyi fatan Alkhairi.

Da taje gidansu ma tayiwa Hajiyarsu magana tana farawa ta katseta bata ma saurara taji qarshen bayanin ba tace babu ruwanta. Duk iyakar bincike Alhaji yayi yasan uban yarinyar nan basuda wani abin Ashasha tsatsonsu tsatsone me kyau da kowq zeso hada zuri'a dasu kuma magana ma ta qare tunda har an kai Sadaki an tsayar da ranar aure dan haka ta gayawa Khadijan idan zata kwantar da hankalinta ma tun wuri gara ta kwantar dan kishiya da kudinta ta siyota tunda tace ba zata bishi inda yake aiki ba ko bata da hurumi cikin maganar auransa daga haka zance ya mutu.
A bangaren Amarya kuwa shiri sukeyi babu kama qafar yaro, dukda ita a sanyaye take komai. Gani takeyi kamar bada gaske ba wai zatayi aure ta rayu da wani Namiji daban ba Khalil ba se taga abin kamar mafarki da zata iya farkawa a kowanne lokaci taga ba gaskiya bane.

Miliyan daya ya bata kudin lefe, Maman Asad tace ya turawa daman suka hada da tanadinta da kudin auran suka fara shirinsu dan bata da ko cokali na kaiwa daki kuma Abba bece musu komai ba haka Mama dan haka suka fara siyan abinda ya samu tunda bikin da saura kusan sati bakwai kafin nan dai dolr zasu magantu tunda dai ai ba zasu kaita babu kayan daki ba. Wani weekend su Bibi sukaje a nan suka samu labarin auran da Momyn nasu zatayi, Bibi ta fasa kuka, Mu'ayyad kansa da ba zatace ga alqibilarsa akan rabuqarta da Mahaifinsu ba ranar seda idonsa da jikinsa suka nuna rashin Jin dadin Al'amarin. Yayi shiru yana kallon Bibi dake rusa kuka kamar ance mata an saka ranar sarewa Umaiman kaine, a hankali cikin nutsuwarsa irin ta mahaifibsa ya kallu Umaiman yace

"Momy bazaki haqura ki dawo gidanmu ba?" Ta zura masa ido na wani lokaci, shekarunsa goma sha hudu yana shirin cika ta sha biyar. Yana da nutsuwa da kaifin tunani da basira ta tabbatar da cewar koda ace sanda ta rabu da Khalil akwai yarinta a tattare dashi amma zuwa yanzu kwakwalwarsa ta gane komai daya faru dan haka boye masa ko bagarar da zancen babu abinda ya canza. Seta gyara zama ta kalli Bibi dake gamsheqar kuka tace
"Ko kiyi shiru ko ki fita ki bamu guri". kukan ta rage dan yanzu ta fara kintsuwa tana jin magana shagwaba dai da sangarta wannan sedai idan bata samu dama ba dan yanda uban yake lelenta daukar kanta takeyi kamar wata Jiddah jaririyar wanwarsu. Umaimah ta kalli Mu'ayyad daya sunkuyar dakai qasa tun bayan da yayi mata magana tace
"Mu'ayyad bani zanyi haquri ba, Dadynku nayiwa laifi shiya kamata yayi haquri ya yafemun ko badan na dawo gidanku naci gaba da zama ba Aa ina buqatar ya yafemun duk abubuwan da suka faru a baya tsakaninmu. Ina so na bashi haquri amma na rasa ta hanyar da zanbi ya saurareni, idan na kirashi a waya bata shiga kullum sena tura masa da Text na ban haquri sama da shekara amma be taba maidamun da martani ba. Bana so na sakaku a ciki na qarawa kaina laifi a gurinsa amma inaga ta hakan ne kadai zan samu afuwa da sassauci a gurinsa. Idan ka koma gida yau ka tayani roqonsa kace masa ko minti daya ne ya bani dama na nemi yafiyarsa kota wayane ko bazece mun komai ba ya amsa wayata kawai hakan ma ya isheni".
Shiru yayi yana kallonta kafin ya sauke ajiyar zuciya yace
"Idan ya haqura zaki dawo toh?" Bibi ta fada cikin kuka har sannan seta jata jikinta tana cewa
"Ban sani ba Bibi, duk abinda Allah ya tsara mana ina fatan ya zama mana Alkhairi gaba daya a rayuwarmu. Koda ace na auri wani babu abinda ze canza zaku cigaba da rayuwa cikin walwala kamar yanda kukeyi yanzu kuma zaku cigaba da zuwa gurina ko?"

"Nidai Momy kawai ki dawo gidanmu, shikenan mu se mu tashi Mamanmu da Babanmu basa tare nidai wlh kawai ki dawo" Bibin ta sake fashewa da kuka se Umaimah tayi murmushi tana janyeta daga jikinta tace
"Ke ai matsalar kina girma amma tunaninki na nan kamar na yar baby, to idan kuma mutuwa nayi fa gana daya ya zakuyi?"
"Toh Momy mutuwa ai daban munsan ba zaki dawo ba yanzu kuwa kina da rai. Wlh Dady yana sonki, ko jiya seda naga yana kallon hotonki ni nasan daman kece bakyaso ki koma gidanmu. Momy indai saboda Mamah ne bata da matsala, tana da kirki zaku zauna lafiya da ita dan Allah indai Dady yace ki dawo ki yarda kawai kinji" Mu'ayyad ya sake fada kamar shima ze saka mata kukan. Qirjinta ya ringa bugawa da qarfi jin da tayi yace wai Khalil yana sonta har yana kallon hotonta koda yake ba abin mamaki bane ta sani Khalil na sonta kamar yanda itama take Sonsa amma babu yanda suka iya da qaddara haka Allah ya nufa a tsakaninsu kuma itace sila.
Be sake cewa komai ba itama tayi shiru, haka suka qarasa wunin ranar babu dadi. Zancen auran nata ya cirewa yaran karsashi ita kuma maganganunsu suka sake jefata a dimuwa suka qara sanyaya mata jiki matuqa. Suma gani sukeyi itace bata son zaman lafiya kuma taqi komawa gidansu ne saboda matar Babansu. Abinda ya qara sanyaya mata jiki qalau yanda Iman ko a qafarta zancen auran be shafeta ba uzurin gabata kawai ta ringayi. Daman haka take ita, babu wata shaquwa a tsakaninsu yanda take mu'amalantarta babu alamar ta dauketa matsayin uwa mahaifiya maganarta kullum Mamah kaza Mamah tayi kaza. Da akazo daukarsu kafin su tafi seda ta sake jaddadawa Mu'ayyad kan ya hadata da Dadyn nasu, tana matuqar son magana da Khalil din, bata so ta shiga sabuwar rayuwa da dakon haqqinsa ita ta sani ba zata samu nutsuwar da take fata ba.
A daren ranar suna komawa gida Bibi bata iya jiran Khalil ya dawo gida ba ta dauki wayar Humaira ta kirashi dan tasan be zama lallai Yayannata ya fada masa saqon Momy ba.
Chapter 259 · 0% Book details