← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 267

Sashe 72

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakan da sukayi yasa kwana biyu ta dage ta dena komawa bacci bayan Asuba, da tayi sallah zatayi qoqari tayi shara da mopping ta wanke Bandakuna tsaf ta gyara gida kafin ta hada musu abin kari har tayi wanka Mu'ayyad na tashi tayi masa shima idan Khalil ya fita seta samu ta lallabashi su koma baccin se ya zamana bata da lokacin hawa social media yanzu sosai da rana seda daddare a lokacin kuma suyi ta fada da Khalil da yake cewa tana shiga haqqinsa.

Bangaren tara wanki ne dai ta kasa denawa dan seta hada na kwana uku hudu taga kayan sa na tsakar gidan sun kusa qarewa sannan zata wanke su sedai ba'a kwashe cikakken wata ana haka ba ta sake komawa ruwa a cewarta ayyukan sunyi mata yawa wani lokacin ta zama se a hankali gidan ya fita a hayyacinsa musamman da Mu'ayyad ya fara rarrafe haka ze ta watsar da kaya wani lokacin ta ajiye ruwa ko lemo ya zubar akan carpet din haka gurin duk ze hadu ya ringa warin ruma ko kuma ta barshi babu Diaper duk ya fitsare palour abin na Umaimah dai se Addu'a kawai babu abinda ya dameta idan ta sake shi ya shiga sabgoginsa ita kuma zata harde a kujera ta hau chatting.

Tafiya ta tasowa Khalil zuwa Abuja wani aiki kuma ze dauke shi a qalla sati biyu zuwa sama ya san sarai zasu sha daga da ita akan tafiyar dan haka be sanar da ita ba seda ya rage sauran kwanaki biyu da daddare ya gaya mata, yanda ya daure fuska tamau yayi maganar ya saka ta kasa yi masa musun baza taje ba, a zuciyarta ta ringa juya yanda zata kaucewa tafiyar nan dan ita dagaske ta tsani binsa ko ina, sedai tasan idan tace kaitsaye bazataje ba rigima zasuyi dan haka tayi shiru har washe gari bata shirya komai ba, sanda ya gaji yayi mata maganar bega tana hada kaya ba bata ce masa komai ba ta shiga daki ta hada masa jakarsa tsaf tana cikin hada kayan ya shiga ya sameta, ya kalli akwatin tasa yace

"Ku ina naku kayan naga nawa kadai kike hadawa"
"Zan hada mana so nakeyi na gama da nakan" ta bashi amsa badan zatayin ba, Allah ya sani bata son binsa tafi so ya tafi ya barta a gida ta samu yancin yin yanda take so bayanan bare ya ringa damunta. Be sake kulata ba yayi shirin kwanciya yana sake jaddada mata da qarfe goma zasu tafi kuma karta kwashi kaya da yawa dan jirgi zasu bi yayi kwanciyarsa ya barta tana ganin yayi bacci kuwa ta gyara Mu'ayyad da shima yayi baccin ta kwantar dashi ta bar musu dakin.

Palour ta koma ta dauki wayarta ta hau WhatsApp taci sa'ar samun Rufaida Online nan take gaya mata har yanzu ta kasa samun mafita fa akan tafiyarsu gashi har gobe ne
"Kema dai son wahalar da kai kawai seda nace miki ki fito kawai kice masa ke bazakije ba dan ni haka mukayi da Abban Anam shikenan wai yayi zuciya be Sam cewa ze tafi wani guri dani ba niko ko a Jukina indai z ajiye mun komai ya tafi Allah ya dawo dashi lafiya" Rufaida ta fada, Umaimah taja numfashi kamar tana gabanta tace

"Baki san halinsa bane shi yasa nidai gara ki bani ko wata qaryarce da zanyi masa ya barni amma ba kai tsaye bace bazani ba"

"To ai kuwa se ki tashi ki hada kaya ku tafi tunda bazaki iya ce masa ba zaki ba, nikam bari naje na kwanta dan nima gobe zani Asibiti idan kun tafin to idan kuma kina nan ma hadu in Allah ya kaimu" daga nan sukayi sallama. A palour taci gaba da zama tana chatting da duba Ticktok da IG har bacci ya kwasheta seda Mu'ayyadya farka yana kuka Khalil ya fito ya tasheta yana mitar wannan dabi'ar data samu ta zaman kallo har tayo bacci a tuninsa, ta wuce ta koma dakin daman ko kayan jikinta bata samu canzawa ba taci gaba da bacci.

Da Asuba suka tashi da Alhinin rasuwar Mijin Anty Hafsa sanadiyyar ciwon ciki da yayi a cikin dare kafin Asuba rai yayi halinsa. Sosai suka kidima da jin wannan labari dole suka tafi gidan Jana'izar daga can bayan an gama Khalil yayi mata sallama ya wuce Abuja shi kadai ya barta nan wannan dalili ya rushe tafiyarsu tare sedai sati daya bayan rasuwar ya kirata akan ta shirya ze saka Khalifa ya siya musu Ticket din jirgi zata same shi a Lagos dan daga Abuja can suka wuce anyi canjin Manager bangarensu na kamfani dan haka an bashi ruqon kwarya kafin a gama tantance wanda za'a bawa be san tsahon lokacin da abin zero dauka ba kuma Allah ya sani baze iya ci gaba da zama shi kadai ba ba tareda ita a kusa dashi ba.

Duk da sanin yanayin Khalil din da irin halittarsa ta san baya iya jure dogon lokaci ba tareda ita ba amma tayi biris da maganarsa, daman tana gidan Anty Hafsa tun bayan rasuwar har akayi bakwai da aka watse Mama tace ta koma gidanta tace dan Allah ta barta ta zauna da Anty Hafsan kodan Halin da take ciki dakyar Maman ta barta shima saboda Khalil din baya gari dan haka koda yayi mata maganar bin nasa babu wanda ta gayawa har ana ya gobe ranar da yace zasu tafin tazo a ranar Taje gida dauko musu kaya ita da Mu'ayyad Khalilfa ya kirata akan zeyi booking musu ticket na qarfe nawa take so kai tsaye tace masa sunyi magana da Yayansa yace a barshi.
*SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS*

*Shin yar uwa kina da wata matsala ce data shafi zamantakewar aure da kika kasa gane kanta? Ko kuwa a bangaren megida ne Al'amura basa tafiyar miki daidai yanda kike so*

*Qaiqayin gaba, farin ruwa ko ruwa me qarni yana fitar miki kinje Asibiti kinsha magani har yanzu ba'a dace ba? Ko kuwa kin kasa gane kan mu'amalar auratayya bakyajin dadi ko kina jin zafi a lokacin saduwa*
*Aa damuwarki inda zaki samu ingantattun magungunan mata marasa illah wadanda masana ilimin suka hada ba yan taka haye to ki garzayo nan domin muna da maganin matsalolinki da yardar Allah*

*A Sumayyas_herbal_aprodiasics* *muna bada ingantattun magunguna wadanda masana sukayi bincike suka tabbatar da suna samar da waraka ga dukkan matsalolin da kuka zo dasu*
*Muna da maganin sanyi ko wanne iri da yardar Allah zamu baki bayan munyi miki tambayoyi domin sanin yanayin lakurarki*
*A bangaren kayan gyara muna da ingantattun tsumi, Gumba, Kaza/ciccibi, Sabaya na gyaran Nono, maganin qiba dana rage qiba ingantattu da babu kwaya a cikinsu*
*Sannan munada tsari na tattaunawa da mata domib musan matsalolinku mu kuma baku shawarar yanda zaku magance su da yardar Allah*
*Adreshin mu Zaria/Abuja muna kuma aika kaya ko ina a fadin qasarnan cikin Amincin Allah kutuntube mu akan*
*07031876677*
Ko a IG *sumayyas_herbal_aphrodisiacs*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

Page 32

Hankali kwance taci gaba da sabgoginta musamman da daman ya aiko mata da kudade masu nauyi da sunan ko zatayi wani shiri na tafiyar ta tasa su gaba siyi banza siyi wofi rantawa qawaye da zubin Adashin Maman Hauwa da Rufaida ta sakata shiga dole duk a haka ta rabar da kudin Khalil nacan tun yana zuba idon ganinsu har hankalinsa ya fara tashi musamman daya kira wayarta a kashe se ya maida akalar kiran ga Khalifa wanda nan take ya shaida masa yanda sukayi da Umaiman.

Sosai ran Khalil yayi baci lokacin daya kira Khalifa yake tambayarsa zancen tahowar tasu ya gaya masa ai tace sunyi magana an fasa. Bece masa komai ba ya kashe wayar, ya gwada wayar Umaimah yafi sau a qirga amma a kashe daya gaji ya sake kiran Khalifan yace yaje gidan ya gaya mata ta kunna wayar ko ya bata tasa suyi magana dukda a lokacin dare ya farayi haka ya tafi ya tararda gidan kulle da kwado abinda ya sake harzuqa Khalil din kenan ya qudurce aransa baze sake kiranta ba, duk ranar da ta kirashi da kanta a sannan zeji ba'asin abinda tayi masa.

Kamar wasa kuwa seda ya kwashi kwana uku a Lagos ba tareda sunyi magana da Umaimah ba, duk yanda yaso akan ya shareta karya kira wayarta ya kasa jin kuma har kwana ukun wayar a kashe se ya fara tunanin kodai ba lafiya ba amma idan da wani abu ya faru da za'a kirashi a sanar dashi dan haka ya yanke shawarar kiran Mama tunda dai bata gida ya tabbatar da idan ba gidansu ba babu inda zataje dukda be bata izinin hakan ba.

Cikin mutuntaka suka gaisa da Mama bayan daya kirata ya sake yi mata gaisuwar Mijin Anty Hafsa ta amsa tana tambayarsa aiki tareda godiyar Kayan Sadakar da aka ringa kaiwa daga gidan Hajiyarsa. Shiru sukayi gaba daya a ransa yana tunanin idan Umaimah bata gidan fa tsahon wannan lokacin ya za'ayi, Kukan Mu'ayyad da yajiyo ta cikin wayar da Ashar din da Umaimah take korawa wata da be san ko wacece ba ya warware masa damuwarsa dan haka kawai ya cewa Maman daman ya kira su gaisa ne yayi mata sallama ya kashe ransa na masa suya, kenan tana sane ta kashe wayar tunda tasan batayi daidai ba tunda Koda ace wayarta ce ta lalace ai yaci ta ari ta wani ta kirashi sannan da izinin wa ta bar gidan kuma meye dalilin qin binsa da tayi.
Chapter 72 · 0% Book details