← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 267

Sashe 26

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka suka kwana Anty dole tayi gum daga sannu se idan zata tambayeta ko akwai abinda take da buqata ne, nan Umaimah ta samu yanda take so, kwana tayi tana tsara yanda cikin ruwan sanyi zata saka su nemo mata Khalil su sasanta ba tareda hankalinta ya sake tashi ba dan ta rantse ita da Khalil mutu ka raba, badai yace ya fasa auranta ba wallahi.

A haka ta shafe kwana uku a Asibitin kafin aka sallameta, sau daya Mama taje dubata dan ita dai tace kallonsu kawai takeyi amma bata yarda da wannan rashin lafiya ta Umaimah ba, Anty data sha zaman jinya har qaramin ciwo tayi itama bayan an sallamosu saboda fi'ilin datasha gurin Umaimah.

A gidan ma bata haqura ba sabon salo ta fito dashi na zaman daki bata leqowa ko qofar dakin tana ciki duk kuma sanda za'a leqata kuka takeyi seda ta kwashe kwana hudu tana wannan halin abinda ya fara damun Mama kenan dake daukar abin nata da a matsayin wasa gashi har sannan basuji wata magana daga bangaren Khalil ba, a lissafi kuma biki yana ta qaratowa dan saura sati uku ne da kwana biyu.

A kwana na hudun ne Maman ta kasa shiru da safe ta samu Abba yana shirin fita tace masa
"Alhaji yanzu kana gani haka zamu zubawa Umaimah ido tana nema ta illata kanta? Bafa ta fitowa ko tsakar gida tana cikin daki, abinci kansa se Saratu tayi da gaske sannan take ci babu abinda takeyi se aikin kuka gaba daya ta lalace a yan kwanakin nan ta fita hayyacinta".

"To yanzu Malika me kike so ayi? Na kaita Asibiti an bata magunguna likita ya kafa mata dokoki da sharuda ai ita ba qaramar yarinya bace da za'ace se anyi mata tuni akan muhimmancin lafiyarta, tunda abinda ta zabawa kanta kenan taga ya fiye mata se tayi duk wanda zeji mata babu dadi ai ba kamar ita da ciwo yake a jikinta ba" Abban ya bata amsa cikin halin ko in kula.

"Haba Alhaji be kamata kace haka ba mafita dai za'a nema tunda dai ko yaya Umaimah fayar muce muna kuma son farincikinta. Damuwarta dai gaba daya akan yaron nan Khalil take, kaga tun waccen ranar bana tunanin ya sake zuwa kuma basu turo wani babba akan maganar tana nan ko sun fasa din da gaske ba.."

Katseta Abba yayi da cewa
"Toh se ku jira duk daren dadewa ai zasuzo, idan suna ciki za'a sani idan ma fasawar sukayi duk za'aji. Kawai a ci gaba da shirye shiryen ita Nuratu tunda shine magana dahir a yanzu ita kuma zuwa lokacin se muga abinda Hali yayi".

"Baza'ayi haka ba Alhaji kenan haka zamu zuba mata ido a cikin wannan yanayin? Dan fa baka leqawa ka ganta ne Alhaji kai da kanka nasan se tabaka tausayi wallahi" Maman ta fada cikin muryar karaya, se Abba ya kalleta yace

"Ai saboda karma naji tausayin nata ta sakani yin abinda banyi niyya ba ya saka bana leqawar, sannan duk ki dena wani zagaye zagaye nidai bazan kira yaron nan ko iyayensa ba akan maganar auransu a yanzu tunda damab ba tallanta na kai masa ba shi ya gani yace yana so. Akwai iya lokacin dana diba idan basu magantu ba a sannan ni da kaina zan tattara komai da suka kawo a mayar musu shikenan magana ta qare.

Kije kiyiwa yarki fada ki nuna mata muhimmancin tawakkali ba komai da kake so a rayuwa kake samu ba, kuma sau tari abinda kake so be fiya zamar maka Alkhairi ba dan haka ta bawa zuciyarta haquri, ta kuma qudurce koda Khalil ko babu shi zata rayu. Sannan shi aure lokaci ne duk sanda ubangiji ya tsayar mata zatayi" yana gama fada ya dauki jakarsa da waya dake ajiye yayi mata sallama ya fice.

Jiki babu kwari Maman ta biyo bayan sa tana yi masa Adawo lafiya, dakinta ta shige gaskiya a wannan gabar bazata zuba ido yarta ta shiga depression akan Namiji ba. Gara susan abinda ake ciki, idan ya fasa da gaske ya fada da Addu'a da roqon Allah zasu san yanda zasu cire mata sonsa daga zuciyata amma wannan zaman rashin sanin madafar baze kaita ko ina ba.

Gaba daya hankalinta a rabe yake bata ma da nutsuwar da zatayiwa Nuratu nata shirin auran, tana murna Allah ya kusa yanke mata zata aurar da yammatanta gaba daya ashe da wata a gaba toh Allah ya zaba abinda yafi Alkhairi.

Da yammacin ranar Jikin Umaimah yaqi dadi, kuka ta dasa tun rana tun tana na qarya sega abu na neman ya zama na gaske se kokawa take da numfashi kamar me cutar Asthma.
Suna tsaye a tsakar gidan suna jiran Nura dan maqotansu ne Salman ya nemo shi dan akai Umaiman Asibiti a motarsa sega Yaya Hajiyayye.

"Alhamdulillahi gara da Allah ya kawo ki Hajiyayye, Sharifa kamata muje tunda ga mota" Anty dake tsaye kan jiki kan qarfi akan lafiyar Umaimab ta fada. Se Hajiyaye ta bisu da kallo ta shiga tambayar meya faru, ganin halin da take ciki yasa ta bawa Salman key tace ya kaisu kawai su zasu biyo bayansu a Adaidaita aka ciccibi Umaimah aka yi Asibiti da ita.

Tareda Mama da Hajiyayen suka hau Adaidaitan, a hanya take gaya mata dalilin zuwanta Hajiya Maryam Babbar Yayarsu Khalil ce ta kirata akan gobe zasu kawo lefe, tana ta bada haquri na rashin sanar dasu da wuri saboda sun so su bari se cikin weekend Hajiya ta dage akan se an kawo goben,
"Na gayawa Yaya hafsa da Naziyya suna hanyar zuwa gidan yanzu suma nasan saboda mu shirya yanda za'a tarbi baqin ga kuma wata sabuwa ta tashi" Hajiyayyen ta fada.

"Alhamdulillahi, ai da tun a gida kika bada wannan daddadan labarin da ba se munzo Asibiti bama" Mama ta fada cikin tsananin murna, se Hajiyayye ta kalleta da rashin fahimta, a taqaice Maman ta fayyace mata yanda akayi tun zuwansu dubiyar Hajiyar Khalil da dalilin kwanciya ciwon nata.

"Amma Umaimah anyi mara hankalin yarinya, setayi abu kuma tazo ya dameta, tace ta fasa toh duk wannan ciwon na magani da menene takeyi in banda tsabar iskanci. Wallahi Mama har tunani nake kar azo ayi abin nan taje ta zubdawa da mutane mutunci da mugun halinta, dan ma Allah ya rufa asiri ta rabu da wadannan yan iskan qawayen nata da suke qara ingizata tana rashin hankali" Hajiyayyr ta fada cikin jin haushin abinda ya faru,

"Kedai addu'a zamu cigaba da yi mata ina tayi ba dare ba rana Allah ya shiryeta, yasa kuma Auran nan ya zama Alkhairin da kowa se yayi farin ciki dashi, kuma ina ji a jikina in Allah ya yarda auranta da Khalil shi ze kawo qarshen duk wasu fitintunu nata, se kowa yayi mamakin yanda Umaimah zata dawo" Mama ta fada daidai sanda suka sallami me Adaidaita Hajiyayye ta amsa da "Amin".

Sun tarar dasu a Emergency suna zaune babu gado, kusada Umaimah dake ta kuka tana Jan numfashi Yaya Hajiyayye ta tsaya tana kallon Anty tace
"Nifa nazo muku da good news gobe za'a kawo lefen Umai, se gashi ashe ita tana qoqarin sheqawa lahira ma. To bari na kirasu na gaya musu ashe tace ta fasa bani da labari dan in suka rigada suka  kawo fa kaya ya shiga sahun gado mu zamu rabe abinmu".

Kafin wani ya bata Amsa Umaimah ta yunqura ta dire a gabanta tana zare ido tace "lefen wa Maman Asad? Kardai kice mun nawa da gaske Khalil be fasa aure na ba?"

Hararar wasa Hajiyayyen tayi mata tana danne dariyar data taso mata saboda irin alkafurar da Umaimah tayo tace
"Toh in ba naki ba wace za'a kawo lefe, kinsan dai an kawo na Nuratu koda yake yanzu  nake samun labari kin fasa gara tun wuri na sanar musu su san abin yi..."

"Wallahi qarya nake ban fasa ba" Umaimah ta katseta kafin ta miqe tsaye kamar wata iska Feee tayi waje bakin ta a washe yanda kasan an mata bushara da Aljanna mutanen dake zaune a gurin suka bita da kallo, ranga ranga aka shigoda ita gashi ta miqe akan qafarta har tana gudu wannan abin Al'ajabi da yawa yake.

PROMO
PROMO
PROMO

BEFORE 4K NOW 2500

3968303018
ZAINAB SHU AIBU
FCMB
KITURA SHEDAR BIYA 👇🏻

08162859027

AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA

INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK DATTIN MARA CIWON MARA CIWON JIKI HANA HAIHUWA RASHIN NI IMA RASHIN JIN SHA AWA FITAR FARIN RUWA KAIKAYI KURAJEN PP DA NA JIKI JIN ZAFI YAYIN SADUWA FITAR FARIN RUWA MAI WARI BASUR KOMAI DADEWARSHI CIWON NONO

SHIRYE NAKE ZANYI MAKU PROMO SABODA WA ANDA BASU SHA BA SU ZO SU DA DANA MAGANIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID DUK LABARIN DA AKE BAKU GASKENA MAGANINA KANKAT NE KOBAKISHA KOMAI BA YA ISHEKI
*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

PAGE 13

Dole suka tattaro suka koma gida dan ita mara lafiyar ma Adaidaita ta tare zata hau seda Yaya Hajiyayye ta zageta tas kafin ta kama kanta ta rage zumudin murnar da takeyi. A hanya kuwa bakinta yaqi rufuwa, tambayarsu take dagaske ne gobe za'a kawo lefen? Kenan Khalil be fasa ba amma me yasa ya dena kiranta harta kwanta Asibiti beje babu wanda ya tankata se Anty ce me biye mata dan gaba daya haushi take bawa sauran.

A gidan ma haka suka hadu suka cashe mata, sakarya, mara aji sunkirata dashi yafi sau a qirga amma ko a jikinta ita kam hankalinta naga kiran wayar Khalil da tun dawowarsu take gwadawa amma ana gaya mata a kashe take amma taqi haqura.

"Wallahi tun wuri idan zakiyi hankali kiyi dan Maza ba'a yi musu wannan rawar jikin, kinja ajin ma ya Allah ya cika ballantana kin nuna masa duk duniya babu ya shi muna nan wata rana se kinji yace ze dakko wata idan kin nemi ba'asi yace saboda biyayyarki tayi yawa" Naziyya ta fada.
Chapter 26 · 0% Book details