Sashe 214
Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Hajiya nayi la'akari ne da halin da nake ciki ina ganin kamar akwai cutarwa a zaman mu da ita tunda bani da lafiya ita kuma dole tana da buqatun da bazan iya biya masa su ba. Tun ina Asibiti nayi tunanin na sawwaqe mata kamar hakan zefi mana sauqi dani da ita sedai kuma banyi hakan ba. Hajiya kullum qara sonta nakeyi harta kai yanzu ina jin bazan iya rayuwa babu ita ba amma kuma bana so Allah ya kamani da haqqinta shiyasa nake so nayi yaqi da zuciyata na rabu da ita taje ta auri wani me lafiya ni kuma naci gaba da rayuwata a yanda Ubangiji yaso ya ganni" ya qarasa maganar cikin rawar murya saboda abu biyu da suka shaqe masa zuciya, baqin cikin abinda Umaima tayi masa ga kuma fargabar rabuwa da Humaira da yake jinta har cikin jini da tsokarsa.
Jin Hajiyar tayi shiru bata ce komai ba ya dago ya kalleta, a rikice ya sauka daga kan kujerar da yake ya durqusa a gabanta yana cewa
"Kiyi mun afuwa Hajiya idan a cikin maganata da akwai wadda ta bata miki rai har tasa kike zubar da hawayenki ki yafe mun zubar kwallar ki ba Alkhairi bace a gareni".
Ganin yanda ya rikice din jikinsa har yana rawa ya saka Hajiya qoqarin tsaida hawayen nata tana cewa
"Bakayi mun komai ba Babana ba kuma kaine silar zubar kwallata ba. Ina tuna irin Halaccin da mukayiwa yarinyar nan a rayuwa amma ka dubi da abinda ta saka mana. Umaimah ta cutar damu sedai mu barta da Allah ya bi mana haqqin abinda tayi mana" Hajiyar ta fada tana sake rushewa da kukan daya fi na farko, dakyar Khalil ya lallabata tayi shiru cikin yanayi na rashin dadi tace
"Maganarka gaskiya ce Babana tabbas zamanka da Humaira a halin da ake ciki da akwai cutarwa amma ai bama fatan ka dawwama a haka, ba zama zamuyi ba zaka ci gaba da neman magani har Allah yasa a dace saboda bazan so ace ka rasa nagartacciyar yarinya kamar Humaira ba ka rabu da waccen alaqaqai sharrinta be rabu damu ba yana nema ya sake rabaka da Alkhairin da a kullum nake roqa maka gurin Allah nayi imani da cewar Allah ze karbamin ya maida maka da madadin Alkhairi. Kar kayi gaggawar yanke hukunci ka fara tuntubarta kuyi magana duk abinda ta zaba se muyi fatan ya zama mafi Alkhairi dukda in har rabuwar ku ce ta kasance wadda bana fatan toh tabbas bazan yarda nayi Asarar suruka kamarta ba, zan umarci Khalifa ya nemi auranta qila abinda Allah ya...."
"Haba Hajiya wace irin magana kikeyi haka a gabana kike kiran Khalifa ya auri matar dana tara da ita da raina ban mutu ba haba Hajiya" Khalil ya katseta cikin wani irin sauti da ya sakata yin shiru babu shiri sannan ta fuskanci katobarar da tayi. Idanunsa suka kada sukayi jajir ya sunkuyar da kansa qasa a hankali ya sake cewa
"Kiyi haquri na daga miki murya amma Hajiya dan Allah karki qara kawo wannan tunanin bazan jure ba zuciya zata iya yin bundiga na mutu kawai kowa ya huta" ya fada tamkar ze rushe mata da kuka.
"In sha Allahu ba zaka mutu yanzu ba Babana yanda ka fara dandana rayuwar farin ciki da Izinin Allah haka zaka qare rayuwarka cikin farin ciki da annushuwa. Kaje ka samu matarka kuyi magana ta fahimta nima zan samu Mariqiyarta domin babu abinda zamu boye musu sannan muci gaba da addu'a Allah ya zaba mana mafi Alkhairi"
"Amin Hajiya" ya amsa se ya miqe da shirin tafiya maganarta ta dakatar dashi ya kasa gaba ya kasa baya jin tace
"Babana naji kace ka tara da ita kana nufin ka dora mata iddarka kenan?"
Dakyar ya iya daga mata kai saboda bala'in kunyar daya lullube shi Hajiya ta zabga tagumi tace
"Allah ina roqonka kasa da dogon zama tsakanin wadannan yara, Babana bansan da idon da zamu kalli iyayen yarinyar nan ba idan rabuwa ta gifta tsakaninku bayan ka maida musu da yarinya bazawara, ashe hasashena ba qarya bane da nake ganin kamar tana da Shigar ciki"
Wani quum yaji a kansa kamar ta buga masa guduma Jin wai kamar Humaira nada ciki, a hankali ya furta 'Hasbunallahu wani'imal wakeel' idan kuwa har ya zamo gaskiya Umaimah ta cutar dasu da abinda Humaira zata haifa tayi sanadiyyar da ze rayu ba a tsakanin iyayensa ba kamar yanda ta janyo wa nata yaran. Haka ya fita daga bangaren Hajiya a salube kamar mara lafiya ita kanta Humaira ganin yanayinsa ya jefata a damuwa ta shiga tambayarsa ko bashi da lafiya ne amma yace mata qalau yake. Abincin ma kadan yaci yace suje su kwanta ta kalli agogo tara ma sannan tayi hakan ya qara tabbatar mata da tabbas bashida lafiya to ko abinda tasa yayi dazu ne ya tayar masa da ciwon sa gashi ita kuma ji takeyi kafin su kwanta ma da ze qara da taji dadi haka ta bishi suka kwanta ya sakata a jikinsa sosai ya rungumeta gaba daya ya rasa ta ina ze fara tambayarta tana so taci gaba da zama dashi ko yaya, idan kuma ya tuna furucin Hajiya na cewar zata nemawa Khalifa auranta se yaji kamar ya hadici zuciya ya mutu wata zuciya ta hakaito masa kenan abinda Umaimah take ji game dashi kenan? tabbas Abune me matuqar nauyi a zuciya amma be kai ta aikata abubuwanda tayi ba inda tana da Iklasi a zuciyarta.
A haka bacci ya fara fizgarsa yana ta tunane tunane ya kasa yi mata maganar, qirjinsa da yaji tana shafawa ya sakashi bude ido ya kalleta base ta gaya masa abinda take buqata ba yanayinta kadai ya fahimtar dashi gabansa ya fadi to me yake faruwa kuma, wace jarabawar ce ta sake tun karo shi? Wata uku kenan yanzu duk idanba shi ya jata jikinsa ba kunya da tsoron ya tabata takeji har seda ta tabbatar da ba abinda take wa tsoron zeyi mata ba kafin ta sake dashi sosai amma a yau tazo da wani sabon Al'amari da yake rikitashi, babu yanda ya iya haka ya sake yamutsata kamar na dazun har seda ta samu nutsuwa kafin tayi wanka suka kwanta zuciyarsa fal cike da tunanin mafita. Tabbas idan har yanayinta ya fara canzawa zuwa ga yawan buqata rabuwarsu ita ce maslaha duk kuwa surutun da za'ayi gara ayi akan ya cutar da ita kota fada wata halakar da baya fata a dalilinsa baze yafewa kansa ba. Dakyar bacci ya daukeshi saboda tunanin da yake ta famanyi.
A bangaren Hajiya ma haka ta kasance da ita ta kasa bacci tana saka da warwara daga qarshe ta yanke shawarar takawa qafa da qafa taje ta samu Mama Hauwa washe gari, hakan kuwa akayi qarfe Goma na safe a gidan tayi mata Mama Hauwa ta tareta da murya a ranta kuma tana mamakin zuwan Hajiyar dan haka kawai bata taba zuwa gidan ba seda kwakwkwaran dalili, ita ce take leqata lokaci lokaci tun ma a zamanin baya daga baya itama ta watsar suka zamana se idan abu ya farun sannan za'a hadu sudai yaransu da Allah ya qulla Aminta a tsakaninsu kullum suna tafe gidajen junansu.
Bayan ta ajiye mata Kunun gyada da Alala me kyau da tayi na karyawa gamawarta kenan tayi wanka tana shirin zama ta karya Hajiyar ta shiga.
"A qoshe nake Hajiya kedai ki karya se muyi maganar data kawoni dan zanfi so kici ki qoshi tukunna" Hajiya ta fada se Mama Hauwa tayi sak kafin ta saukeajiyar zuciya taja kwanukan ta shiga cin abincin a ranta tana addu'ar duk ma abinda Hajiyan tazo dashi Allah yasa Alkhairi ne. Seda taci ta qoshin kuwa ta kwashe komai kafin ta zauna tana cewa
"Ina jinki Hajiya, Hajiya ta janye tagumin data rafka kafin cikin nutsuwa ta shiga zayyanawa Hajiya Hauwa komai game da matsalar Khalil da kuma hukuncin da yake shirin yankewa.
Mama Hauwa tayi shiru kamar ruwa ya cinyeta zuciyarta na bugawa da qarfi tausayin Khalil din ya rufeta kwari ainun, dukda sun san da maganar kwada masa abu da tayi amma basu zata munin abun ya kai haka ba kuma harda Mansur sunyi maganar se yanzu ta fahimci irin jimamin da yaketayi ku ya da nauyi ya hana ya fayyace mata ainihin abinda yake faruwa amma wannan yarinya Umaimah lamarinta se Allah. Numfashi ta ajiye tana kallon Hajiya tace
"Abun babu dadi Hajiya amma duk abinda kaga ya samu bawa da sanin Allah kuma in sha Allahu shi ze warware komai wata rana se kiga komai ya zama labari tamkar ba ayi ba. Sannan Hajiya wannan al'amari a hannunsu yake su zasu yanke wa kansu shawarar abinda ya kamata suyi su da suke yan zamani duk dabarun jiyar da kai dadi wanne ne basu sani ba? amma ina ganin rabuwa ba ita bace Maslaha su zauna suyi magana shi yafi idan anyi haquri da sannu se kiga Allah ya bashi lafiya sunci gaba da zamansu qalau"
Hajiya tayi qasa da kai irin maganar Maman ta bata kunya ita kuwa ko a jikinta taci gaba da cewa
"Allah kuwa Hajiya me ake nema ne dama dai ba wancan abun ake tunani ba dan dai kawai za'ace ita yarinya ce baya ga haka Allah na tuba masu lafiyar ma nawa ke zaune basa samu wasu sun manta ma ana wannan a cikin aure sannan ni ashe ido na ne be gani daidai ba zuwan da sukayi na qarshe ma gani nayi kamar tana da shigar ciki ashe ba haka bane to idan ma Haihuwa ce shi rabo ai lokaci ne in a nesa yake se kiga anja lokacin har lafiyar ta samu a zo a hayayyafa" se sannan Hajiya ta iya cewa