Sashe 243
Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Humaira" ya fada yana girgizata ganin tayi nisa a tunani, ta kalleshi idonta ya kawo kwalla seta sunkuyar dakai yajata jikinsa ya rungumeta yana cewa
"Karki bari shaidan ya lalata zamanmu, karki yarda magauta su mana dariya ki daure ki gayamun menene damuwarki me kike so"
"Kaji rainib wayo bayan yasan menene damuwar tawa kuma zezo yana wani tambayata" ta fada a zuciyarta a fili kuma taja Majina kafin tace
"Ni babu komai".
Rungumeta yayi a ransa yana jin babu dadi, iyakar qoqari yanayi gurin nemawa kansa lafiya a kullum kuma cikin addu'ar Allah ya tsare masa iyalinaa yakeyi shi yasa hankalinsa ya tashi sosai da ganin da yayi mata da wancan yaron, baya zarginta ba kuma ya tunanin zata iya aikata wani abu makamancin wanda shaidan yake yawan kawo masa amma kuma hakan baze sa ya nade hannu ba tareda ya miqe da Addu'a ba da kuma kulawa da lamuranta. Sau da yawa irin wadannan matsalolin da maza sukeyin shakukatun bangaro dasu akan matansu su suke jefasu a halakar da daga baya kowa zezo yana tofin Ala tsine dasu bayan kuma Mijin shi ya bada qofar da barakar ta shigo gidansa.
Sun dade a zaune yana rungume da ita kafin ya saketa saboda bugun qofar da akeyi ya bada izinin shigowa Anwar ya shigo da takaddu. Cikin mutuntaka suka gaisa yana tambayarta yara
"Yan China nan ne suka zo fa yanzu nan kawai Jacob yake gaya mun suna conference room ya musu iso" Anqar din ya fada yana miqa masa takaddu ya karba ya duba yana cewa
"Amma gobe sukace"
"Yau ko gobe dai, sun dai fi qarfafa zuwan goben so kuma tafiya ta kama shugaban kamfanin nasu yau da dare ze tafi shiyasa ya turo su yau dan a gama abinda za'ayi kafin ya tafi dan ze jima" Anwar ya sake fada seya ja kujerar gaban system dinsa ya zauna yana cewa
"Allah yasa na gama hada takaddun bari na tura maka ta Mail dan ban fito da system dina ba tana gida seka projecting mana". Seda ya gama tura takaddun ya kalleta yace
"Na bar miki ita a kunne akwai Korean movies a ciki wannan ne ya saka" ya nuna Anwar,Anwar din yayi dariya yace
"Saboda irin haka kinga bakya zauna boring ba zaki samu abin kallo tunda nasan ku mata daman daga India se Korea kuke kallo".
Khalil ya tashi suka fita yana ce mata
"If you need anything ki kira Secretary se ki gaya mata ba zamu jima ba in sha Allah da mun gama se mu wuce ko?"
"Allah ya bada sa'a yasa a qulla Alkhairi" ta fada suka amsa mata da Amin gaba daya dan Anwar kansa yaji dadin Addu'ar, abinda ya rasa kenan matarsa ta ko ina bata da makusa seta bangaren yi masa addu'a idan ze fita ko godiya idan ya mata abu, qarqarinta tace "Nagode, A dawo lafiya" shikenan.
Kan kujerar daya tashi ta koma ta shiga Media, a maimakon ta bude movies din seta wuce gurin hotuna wata folder guda taga an rubuta
'LIFE' ta bude. Hotuna sun wuce ta irgasu kala kala shida Maman Bibi, wani irin abu ya ringa taso mata zuciya ta ringa tunzurata har ta kasa haquri kai tsaye ta dannawa folder gaba daya delete saboda bacin rai ma ta kashe system din gaba daya ta sauka qara ta dirar ma ragowar naman da bata cinye ba tana huce fushinta a kansa.
Bayan sun koma gida da daddare ma seda ya sake sabon Rarrashi dan yaga abinda tayi daya kunna system din be ce mata komai ba kuma ya bi recycle bin ya maido folder tana ta kumbure kumbure shidai be kulataba har suka je gida seda dare yayi yaga tana neman ta tada sabuwar fitina yasa ya lallabata ta haqura suka kwanta a ransa yana ayya su Mata gaba daya haka suke da Kishi, na Umaimah ne kawai ya fito fili.
UMAIMAH
A sannu a hankali nutsuwa ta fara saukar mata domin nauyin daya danne mata qirji fiye da kaso saba'in cikin dari ya sauka. Tsakaninta da Mama da Abba sun samu daidaito domin ta nemi afuwarsu kuma sunyi mata haka kullum cikin Istigfari take domin tun lokacin da Mama tayi mata tunatarwa akan babban laifin biyewa Safina da tayi ta kaita gidan yan tsubbo hankalinta ya qara tashi. Dare da rana cikin roqon gafarar ubangiji take haka ta rage bacci duk dare seta tashi tayi sallolin Nafila cike da yaqinin ubangiji ya yafe mata tarin laifukanta a garesgi. Ta rasa sallolinta babu adadi sakamakon yawon gidan Malamn tsubbu da suka ringayi da Safina, gaba daya hankalinta yayi nisan da bata taba hango illar abubuwan da ta aikata a baya ba se yanzu. Lokacin da Maman take sake tuna mata da cewar muddin tana so al'amuranta su daidaita seta nemi yafiyar mutanen data musgunawa a rayuwa domin Allah ze iya gafarta mata laifukan da tayi tsakaninta dashi muddin tayi kyakykyawan tuba ta kuma roqeshi amma babu sassauci a cikin haqqoqin data daukarwa kanta na mutane dan haka tilas ta daura damarar neman yafiyarsu amma babban tashin hankalinta ta inda zata fara? A ina zata nemo su?
Tijararta tun tana qanqanuwa takeyinta, bakin Manya da yara babu wanda bata dibarwa kanta ba banda tarin Allah ya isan yaran da take cin zali a Boko da Islamiyya yanzu ta ina zata nemosu ta nemi yafiya wasu ma sun mutu wasu sun bar inda take wasu bata ma sansu ba wannan tunanin ne yake qara dagula mata lissafi ta rasa inda zata tsoma ranta. Cikin manyan kurakuren data tafka a rayuwarta bayan tarwatsa rayuwar auranta da tayi A yanzu ne ta gane girman Al'amarin daya faru tsakaninta da Hadiza. Tana cike da nadama da dana sanin abinda tayi mata ta tabbatar da cewar iyakar haqqin Hadiza ya isa ya hanata nutsuwa a rayuwarta, a yanzu ita komawa gidan Khalil bashine burinta ba, buqatarta ya yafe mata, Hajiyarsa ta yafe mata irin tozarcin da tayi mata haka yan uwansa duk suyi mata afuwa daga baya idan Allah ya qaddara da sauran zama a tsakaninsu zata so ta koma masa idan kuma babu ta haqura ta karbi qaddara a yanda tazo mata sedai hakan yana nufin zata qare rayuwarta babu aure dan babu sauran matsuguni da wani Namiji ze samu a zuciyarta domin ta Khalil ce kuma har abada ba zata dena Sonsa ba.
Tana tsaka da wanke sauran kwanukan da akaci abincin rana dan har a yanzu babu abinda ya canza daga ayyukan da takeyi a cikin gidan, hatta Anty data ce ta karbi girkinta Abba yace ya hana ya kuma tambayeta dalilin da ya saka ta take umarninsa ta tabbatar masa da babu komai. A gaban Mama da ita Umaiman yayi mata tambayar dan Maman tana yawan yi masa tanbihi akan wasu sauye sauye datake gani daga Antyn, tana tsoron zamansu na shekaru ya canza salo a gargara dan ta tabbatar da mawuyacin abu ne su maimaita shekarun da sukayi a baya tare sedai wani iko na Allah. Anty ta dage akan ita babu komai Yayin da Abba ya dage akan seta fada masa dalilinta, cikin wani yanayi tace
"Allah ya sani Alhaji babu wani abu a zuciyata akan Mama ko yaranta. Kuma ni idan ma akwai wani abu dana kasa jurewa be wuce yanda tsayin lokacin nan tun dawoqar Umaimah gidan nan ka rasa walwalarka ba. Baka da isashshen lokacina hira me dadi yanzu bana samunta dakai Alhaji a koda yaushe idan ina tare dakai idan ba tunani kake ba to kana Sallah ko lazumi kuma se naga idan kana tareda Maman Yara kana walwala koda yaushe kana cikin tarairayarta da kwantar mata da hankali wannan abun ne yake damuna kuma zuciya bata da qashi se na ringa ganin kamar ka fifita buqatunta akaina bayan ni bani cw silar bacin ranka ba"
Gana daya sukayi shiru suna sauraronta jin tayi shiru itama Abban ya nisa yace
"Ina jinki Saratu se me kuma?" Seta ci gaba da cewa
"Idan nayi zancen da Qawayena ko yan uwana maganganun da suke gaya mun su suke qara sakani a damuwa amma koma menene yanzu ya wuce tunda kaima fara dawowa Alhajin dana sani shikenan"
"Oh Saratu kenan Saratu iyayen soyayya wato ke kulawar Mijinki da kika rasa itace tasa kika fara Kishi da yarki kina ganin ita ta dagula miki lissafi ko? To kiyi haquri, maganar kuma nafi tattali da bawa Malika kulawa ba abinda kia dauka bane ko Mutane marasa son a zauna lafiya suke gaya miki. Tabbas mun tsinci kanmu a cikin Jarabawa wadda dagani har Malika muna buqatar wanda ze lallashe mu ya jamu a jiki domin halin da muka tsinci kanmu ba qarami bane dole na shanye duk tawa damuwar na qarfafa mata guiwa amma baya ga haka babu wani banbanci ko bangaranci danake nunawa a tsakaninku kuskuren tunani ne kuma nagodewa Allah da beyi nisan da har wata baraka ta shigo tsakanin Iyalaina ba dan haka idan har a tsahon lokacin nan Saratu kina ganin cewar mun cutar dake muna neman afuwarki dani da Malika da kike ganin mun shiga haqqinki ke kuma ga Antynki nan ki nemi afuwarta akan muzguna mata da kikayi kika hanata samun sukuni da Mijinta" Abban ya sake fada gaba dayansu seda suka murmusa da jin maganar tasa se Anty tayi saurin sake cewa
"Haba Alhaji wlh babu komai yafiya kuma tuni ta nema dukda bata mun komai ba ni na yafe mata dama ai Umaimah tawa ce ita take qina kuma komai ya wuce a gurina daman nasan shedan ne kawai da maganganun mutane suka nemi suyi tasiri akaina kuma nima ina neman afuwarku idan akwai abinda nayi na rashin kyautawa ku yafe mun"
"Allah ya yafe mana gaba daya" Abban ya fada daga nan suka tashi kowa ya koma sabgogin gabansa.