← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 199 OF 267

Sashe 199

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

UMAIMAH
Lafiya lau taci gaba da sabgoginta, guraren sha daya suka gama shiryawa su Maman Asad kayan maqulashe wanda Ruqayya tayi ita kuma tana bata Umarni, ta fito daga wanka tana shiryawa suka iso Maman Asad, Nuratu se Anty Hafsa kowacce ta samu kujera ta zauna jugunjugun kamar gidan Mutuwa dan tun jiya da labarin ya riske su kowacce ta rasa kuzari. Hajiya Umaimah ta sako Bubunta ta fesa turare ta fito tana daga qafa dakyar, fuska a washe ta tari yan uwan nata kowacce ta amsa mata da murmushin yaqe, ita dai Ruqayya nata aikin kawo abinci a ranta tana mamakin wannan ziyara da yan gidan nasu Umaimah suke kawowa daga jiya zuwa yau kuma kowanne yazo jiki babu kuzari ta gama ajiye musu abinda zata aje ta wuce dakinta a ranta tana fatan koma menene Allah yasa ya zama Alkhairi.

Ruwa kadai suka iya sha shima bisa tursasawar Umaimah, Anty Hafsa ta dake ta sake nanata abinda Mama tazo dashi jiya ta akai Aya Maman Asad ta dora da nata lallashin tana sake nusar da Umaiman muhimmancin haquri da yarda da qaddara a duk yanda tazo maka. Seda tayi Shiru Umaimah ta kalli Nuratu da bata ce komai ba tace
"Ke kin rafka tagumi baki da abin cewa ne halan?"
"To me zance Umaimah ai sun rigada sun gama magana nidai fatana kiji ki kumayi amfani da abinda suka fada na tabbata zaki ga ribar hakan a gaba" Nuratu ta qara da nata se Umaimah ta gyara zama tana kallonsu su ukun tace
"Toh duk naji ku amma ina so ku sani cewar badan ina ganin mutunchin ku ba da wlh se na muku rashin mutunchi a cikin gidan nan. Ai na gayawa Maman tun jiya kawai dan ita ce shi yasa har nayi shiru bance mata komai ba amma yanzu ku da kuka kwaso qafafu kun yarda da abinda ta gaya muku ku gaku zakuyi mun nasiha ko to iya abinda zance muku Allah yasa kuga irin wannan kishiyar a gidajenku, Ke daman Maman Asad taki tana tafe banga laifinki ba tunda kin karbi rabonki kowa ma ya samu ba damuwar ki bace ke kuma Anty Hafsa me mata uku zaki aura in sha Allahu sannan ke Hajiya Likita kina Asibiti kin tafi Duty zaki dawo gida ki tarar da kishiya keda Naziyya dukda bata nan nasan bakinku daya kuma shawararku daya dan haka tun ina ganin sauran mutunchinku ku tashi kowa ta kama qafarta tayi gidanta kuje can kuci gaba da jaye jayen masifarku kuma ta qare muku akanku".

Yan uwan Humaira basu samu zuwa yin jere ba ranar litinin kamar yanda suka tsara saboda qaryar da Khalil yayi musu akan ana sake fentin gurin dan haka suka bari se ranar Laraba ranar da Amarya zata tare suyi gaba daya saboda talata Mama zatayi wunin biki. A bangaren Khalil kuwa babu wani fenti da ze sake ya dakatar dasu ne kawai saboda har sannan be samu gamsuwar da yake da buqata daga Umaimah ba ta tabbacin ta karbi auran, hankalinsa be qara tashi ba seda sukayi waya da Nuratu ta gaya masa abinda Umaiman tayi musu daya samu Hajiya da Maganar Jalilah Amara na zaune nan take ta fitittike ta hana hajiya cewa komai, fadi takeyi duk Umaiman ta gama haukan qarya da nuna bata san abinda akeyi ba aure dai an daura Amarya kuma zata tare babu kuma abinda ta isa tayi dan suma ba zuba mata ido zasu hakanan tayi yanda take so ba. Ita ya zame ta sake kiran Baba Abu ta gaya masa Khalil ya hana azo ayiwa Amarya jere ya kuwa kirashi yayi masa tatas yana sake jaddada masa muddin be bari an kawo Amarya ta lallami ba to kuwa za'a kawota ta tsiya dan haka washe gari Talata tun safe yacewa Umaimah ta shirya zasuje Asibiti, ya gama tsara ze kaita kawai su kwantar da ita. Idan ma da akwai Allurar da za'ayi mata a qalla tayi sati tana hutawa bayan anyi Mata CS din ayi kawai shidai su rufa masa Asiri ta rabu da cikin jikinta kafin duk wani tashin hankali ya biyo baya.

Qarfe tara suka bar gidan, suna fita motar masu kayan gado da Kujera ta kunno kai dan danan yasan da suna tafe, shirita Umaiman ta tsayayi har suka kai wannan lokacin basu fita daga gidab ba. Suna hanya Jalila ta kirashi akan ya tura mata da kudin kwalliyar Amarya dan gaba daya ita ta karbe bikin daidai da kayan da Amaryar zata saka yau din na yinin ita ta zabar mata ta kai dinki haka gurin da zasuyi Yinin da kudinta ta kama dan da A gida Mama tace zatayi dukda Khalil ya sallami Amaryarsa ya bata kudi kamar yanda akeyiwa kowa amma ya gaya mata baze samu damar halartar duk wani abu da zatayi ba dan haka Maman tace suyi a gida kawai a huta amma Jalila ta kafe akanba haka ba,shi kanshi Khalil seda suka haura kafi ta sarara masa danda cewa tayi se yaje koda yake ko yaje ko kar yaje duk abu daya ne hakan kuma baze chanza duk tsarinsu ba.

Bayan sun isa Asibitin, duk su biyu Dr Al'amin ya ringa surfawa bala'i damanita Umaimah ya cire ta a layi saboda a cewarsa ya dade bega mutumin ba besanciwon kansa ba kamarta to Khalil dinma yabi sahunta, ciwon qafar da yaje yana yi ma daga cewa ya dawo washe gari ayi X-ray se yau ya sake ganinsa haka yayi tayi musu fada kafin ya bashi form ya cike ya biya duk wasu kudi da ake buqata suka bata daki bayan akan washe gari qarfe goma na Safe za'ayi mata aikin. A office ya tarar da Dr bayan ya raka Umaimah dakinda aka bata wanda a VIP section ma ya biya mata saboda ta fi samun nutsuwa da kulawa sosai.

Dr Al'amin ya kalli Khalil bayan ya gama sauraron duk abinda yake fada na ya girgiza kai kawai yace
"Kasan me, tsakanin kaida matarka na rasa wayafi wani cin kai. Dan Allah Malam kaje ka hado mata abubuwan da zata buqata tunda naga shirin zuwa dubiya kukayo sannan ka taho da wadda zata zauba da ita idan kuma kana buqata muna da Nurses da zasuyi maka aikin se kaje a baka Bill ka biya, ina da abinda zanyi idan shikenan maganar ka zaka iya tafiya" ya nuna masa qofa. A sabule ya fita koda yake hakan ma wani achievement ne ze sake ninka qoqari ta wata hanyar dan tabbatar da komai ya tafi kamar yanda yake fata.

Yana tare da ita har akayi Azahar kafin yace mata zeje yayi sallah daga nan ze biya ya gayawa Mama se ya koma gida ya debo mata kayayyakin amfani. Umaimah daketa mitar ita bata ga dalilin da za'a kwantar da ita tun safe ba, ina laifin ace su dawo da dare? Ita ya bari su tafi tare ta hado kayanta da kanta kawai dan be zama lallai ya dakko mata abubuwan da take buqata ba shidai Khalil ya lallabata ya tafi.

Ko minti goma beyi da barin Asibitin ba itama ta fita ba tareda ma ta bari Nurse din dake kula da ita ta sani ba bare ta hanata. Adaidaita ta tara ta tafi gidan, a hanya sukayi waya da Safina take gaya mata gobe za'ayi mata CS din yanzu ta gudo gida se dare zata koma idan ta hada kayanta. Da akwai wasu kayan Baby data siya gurin maqociyar Safinan bata karba ba ta roqeta ta kawo mata su gida yanzu dan akwai wanda zatayi amfani dasu sannan sukayi sallama.
*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

Page 71

Tun daga compound take mamakin kwalayen data gani wanda take da tabbacin na kayan gado ne saboda gashi nan a rubuce seta tabe baki irin ina ruwanta din nan saboda tunanin daya zo mata Hajiya ake sakewa gado, ita fa can su gane yanda suka dena sakata a sabgar su ba bazata saka kanta ba, tasan dai duk wannan shirin baze wuce na auran Khalifa ba daman yaron ba mutunchi ne dashi ba shiyasa tun da ma ake zancen auran nasa bata taba saka baki ba kuma dalilin daya sa taqi fita taga lefen kenan sanann sisinta bazata bayar ba da sunan gudummawa tunda dai ba'a sakota a ciki ba
(A lissafin Umaimah kenan lefe na Khalifa ne saboda ta san da zancen yayi budurwa abinda bata sani ba babu wata kwakwkwarar magana ma tsakaninsu balle har aje ga batun kai lefe)

Kanta tsaye ta wuce cikin gida sedai mutanen data gani zaune a falonta sunyi daidai suna cin abinci yasa ta tsaya turus ta kasa gaba da kasa baya tana kallonsu kamar yanda suma suka zubo mata ido suna kallonta.
Cikin daga murya ta shiga kiran Ruqayya, ta fito daga kitchen da sauri jikinta na rawa dan tun zuwan Matan da batun da sukazo dashi daman ta firgice. A gaban Umaimah ta tsaya kanta a qasa tace
"Gani Hajiya"

Cikeda bala'i tace "Su waye wadannan da kika barsu suka shigo mun falo kamar nasu saboda tsabar rashin mutunchi ji yanda suka zubar mun da abinci akan carpet?"
Kafin Ruqayya ta bata amsa wata qatuwa daga cikinsu tace
"Aa karki ga laifinta mune mukayi kuskure mun dauka falon na masu gidan ne gaba daya ashe naki ne ke kadai da bamu zauna ba to Allah huci zuciyarki mu kam mun gama abinda ya kawo mu ma wucewa zamuyi".
Chapter 199 · 0% Book details