← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 267

Sashe 5

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amma gayen nan dan yarfi ne,yanzu akan dan abin nan shine zece ya fasa auranki? koda yake kansa yayiwa dan dai nasan baze taba samun hadaddiyar baby kamar ki ba wallahi dan wahala shi yayi Asara. Seki share hawayenki da kyanki da quruciyarki bazaki rasa mijin aure ba. Kuma duk mutumin ma daya kasa haquri da halinka tun kafin ya aure ka ta yaya zaku zauna dashi bayan aure ki manta dashi kawai" Nabila ta fada.

"Amma fa Umaimah kema da laifinki ko nace laifinki ma yafi yawa, kishi ai ba hauka bane amma ke idan naki ya tashi rufe miki ido yake kiyi tayin abu kamar wata me tabin hankali. Jifa yarfin da kika masa ranar a gaban mutane dan Allah, be yi fushi ba ya dauke ki har mukaje gida kina zaginsa shi da iyayensa kika sauka kika kuma qara masa, ina ke kika ce idan ya haifu cikin uwar sa ya je ya auri Siyaman ke ya qyale ki? Gashi kuwa ya nuna miki ya haifu saura ki jira ganin IV auran sa da ita nan gaba kadan" Ruma ta fada iya bakin gaskiyar ta.

"Ai ke daman kina baqin ciki da duk wani farin cikin Umaimah a rayuwa ni na dade da sanin kina baqin cikin tarayyarta da Qasim waya sani ma ko da sa hannunki a ciki? Toh Umaimah dai nan gani nan bari duk mugun abin mutum sedai ya koma kansa saboda ke kin rasa mashinshini shiyasa kike farin ciki dan ta rasa nata" Fauziyya ta hayayyaqo mata, seta miqe tsaye itama tana kallo ta tace

"Dani dake babu meyiwa wani gorin ya rasa mashinshini dan gara ni ana gani ana yabawa ke fa? Cusa kai kike amma mazan yi suke kamar basu san da wanzuwarki ba. Ita gaskiya daya ce daga qinta kuma se fada, the earlier da kika gane laifinki kika gyara the better. Amma idan kinga zaki ci gaba da zama da maqaryata suna dora ki a keken bera shikenan, nidai har a gurin Allah na fita dan na fada miki gaskiya ruwanki ki gyara ruwanki kiqi amma Umaimah babu Namijin da ze aure ki da wannan mugun HALIN KISHIN naki" Rumasa'u ta qara fada idon ta akan Umaimah da tayi shiru.

"Kut baki kike mata na karta auru? Toh wallahi tun wuri Umaimah kisan abinyi dan bamu san irin bakin ta ba, Mune shaida" Nabila ta fada cikin son qara kambama abun.

"Ke kika hadu da ita rana tsaka dab haka ke zamu bincika muji ko kina da mugun baki amma ni ki tambayeta ta sanni ta san asalina, kuma duk wanda ze so Umaimah a cikin ku baya nane dan ni son tsakani da Allah nake mata ina kuma so ta gyaru ta rabauta ba irin naku na son zuciya da sake ingizata zuwa ga Halaka ba" Ruman ta fada a fusace kafin ta juya ta bar gurin, a ranta ta qudurce ko Su ne kadai suka rage da zatayi qawance dasu a rayuwa ta haqura, ita Nabila zata kira Mayya?

Umaimah kuwa zama sukayi a gurin Fauziyya da Nabila na sake yi mata famfo da gaya mata kalam da suke fasa mata kai take ganin takai inda bata kai ba. Basu bar gurin ba seda lokacin shigar su test yayi suka tabbatar da sunyi brain washing nata ta hanyar nuna mata daidai abinda take aikatawa da kuma cewar duk wanda ya rabu da ita shi yayi Asara ba ita ba.

Haka suka shiga test din babu wadda ta karanta komai a cikinsu, daman ita ce me qoqarin da take goyasu to yau itama batayi karatun ba gashi anyi fada da Ruma bare ta basu Amsa. Da suka fito daga practical ma sun so su jata wai suje gidan Halima dan tun safen ta ke musu waya suje ita bata zo yin test din ba se taqi saboda tuna gargadin Abba na dazu, haka suka rabu a get ta kama hanyar gida ita kadai dan Ruma da gaske ta dauki fushi ko sashin da suke bata sake kallo ba.

*DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK*

*(UMMU-MAHEER)*

*MARUBUCIYAR*

*WATA KISHIYAR🥰👹 (ALKHAIRI CE KO SHARRI)*

*RUBUTACCIYAR QADDARAH AND NOW*

*HALIN KISHI*

*HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE NAIRA 500*

*GA DUK ME SO ZE TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*

*MARYAM UMAR FAROUK*

*SE A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*

Free page 3

Sosai take jin ta a takure saboda rashin waya, idan taje makaranta ta dawo sedai ta zauna shiru in ta gaji ta dauki littattafanta ta duba dan har yanzu babu me shiga sabgarta a gidan se Anty ita kuma ba kulata take ba.

Ita bata ga abin da zesa gaba daya su wani dauke mata ba bayan ita abun jaje ya sama kamata yayi ataru a tayata amma duk an tsangwameta hatta da Yayyanta da suke gidan Aure kowa tazo harara da zagi ne yake raba su a cikin wannan yana yi taci sati biyu, sauqin ta ma bata zaman gidan sosai saboda gabatowar jarabawa da zasu fara ta qarshe kusan idan ta fita makaranta takwas se biyar take dawowa.

Tana da buqatar waya saboda harkar karatu wani abun softcopy ne zaa bayar dole seda wayar ko system hakan yasa ta niyyaci tunkarar Abban su da zancen siya mata waya.

Bayan sallar Isha ta same shi a palour sa, sam ta manta da Mama ce da girki seda tayi sallama ta shiga ta tarar da ita tana hadawa Abban shayi, kamar ta juya amma ba hali tunda sun tigada sun ganta haka  ta nemi guri ta zauna ta shiga gaishe su kai a qasa.

"Ya akayi Hajia Umai" Abba ya fada cikin sakin fuska ba kamar yanda yake mata tsahon kwanakin ba hakan ya bata kwarin guiwa ta gyara zama tana cewa

"Daman Abba saura sati uku mu fara jarabawa ne, kuma handouts da yawa softcopy ake bamu, bayan nan wani lokacin ina so na danyi browsing babu dama tunda bani da waya"

"Yanzu me kike buqata" Abban ya tambayeta, seda ta kalli Mama da tayi kamar babu ita a gurin kafin tace

"Waya nake so dan Allah Abba ko taka ce ka ringa bani aro in zan duba abu"

"Tawa kuma Aa salon kiyimun jagwalgwalo, bari dai zanyiwa Yayan ku magana se a samo miki ko qarama ce" Abban ya sake fada. Da alama yau yana cikin yanayi me dadi, kamar tace Aa karya saka Yaya Aminu dan tasan da wuya idanze bari a bata sedaita kanne tayi masa godiya kafin ta miqe ta fita. Daga bakin qofa ta labe tareda kasa kunne ilai kuwa ta jiyo Mama tana cewa

"Haba Alhaji, yanzu kai har ka yarda da wannan lambon da tayi kamar ka manta wacece Umaimah shine zaka dauki waya ka bata"

Murmushi Abban yayi yana kallo ta yace
"Malika kenan, takura da tsanani fa baya gyara sedai su qara kangarar da yaro, iya lokacin da aka dauka ai taji a jikinta idan muka ce zamu ci gaba da takureta kuma tun tana biyuwa har zaa iya kaiwa matakin da zata fito da wata sabuqar hanyar da bamu sani ba.

Zan gayawa Babangida ya kawo mata  wayar, daman ko batayi magana ba ina da niyyar sawa ya kawo dan jiya ina jinta tana yiwa Nuratu magiyar ta bata aro ta hana ta, amma hakanbaze chanza komai ba, sannan ina me sake tabbatar miki ki kuma jaddada mata idan wata biyun nan ta cika bata tsaida miji ba sadakarta zan bayar"

"Sadaka kuma Alhaji se kace wata wadda ba'a so" Mamanta fada tana zare ido, se ya miqe tsaye yana cewa

"Kun dauka wasa ne kenan? Daman Lawan megadin gidan Alhaji Manniru ya taba nuna sha'awar auranta toh inaga shi zanyiwa magana kawai, Allah ya nuna mana lokaci zaku gani" ya shige dakin sa ya bar Mama tana cewa

"In sha Allahu Allah ze fito mata da miji amma wane irin sadaka da ita abu babu dadin ji haka".

Qirji Umaimah dake labe a bakin qofa ta dafe, a fili ta furta "na shiga uku daman Abba da gaske yake ni ze bayar sadaka?" Saurin barin gurin tayi gudun kar su ganta a ranta tana ayyana irin diban Albarkar da zatayiwa Lawan duk randa suka hadu, saboda ya raina mata hankali ita ze kalla yace yana so harma ya samu Abban su? Ai kuwa seya gane kurensa, ze san ita ba sa'ar wasan sa bace.

Tana barin gurin Abbaya fito daga daki yana murmushi yace "Ja'ira, Allah dai ya shirya Umaimah yasa ta dena abinda takeyi"
Mama dake jimami ta amsa da "Amin dai, amma Alhaji zancen nanda watan nan daka qara daga qafa. Aurefa ba abin gaggawa bane, dole seta samu wanda suka daidaita ya ga ze iya da ita tukunna dan kasan bazaayi abu a gurguje ba ba tareda an fahimci juna ba ba fata ba daga baya ta falle halinta mutum yazo yana cewa an rufe shi".

Seda ya zauna yaja shayin data saisaita masa kafin yace " Nasani nima na fada ne kawai saboda na qara tsoratar da ita dan tana tsaye ta labe ba tafiya tayi ba, dukda haka da gaske nake ta mayar da hankali ta tsayar da Miji dan naga sako sakonda taga ana mata ya saka take duk iyashegen da takeyi, dan haka karma ki kuskura ta gane ba haka bane".

Umaimah kuwa Haka ta kwana tana juya maganar fito da miji a wata daya, toh ta ina zata fara ma bayan tunda Qasim ya fasa kamar wanda ya tafi da duk farin jininta ko a hanya wani be sake tare ta da sunan soyayya ba.
Idan ta tuna wai Lawan yace yana sonta kuwa wani takaici ne yake taso mata, ta quduri niyyar qare masa tanadi tsaf duk randa sukayi ido hudu kuwa.
Chapter 5 · 0% Book details