← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 267

Sashe 73

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A bangaren Mama kuwa yana kashe wayar ta dakawa Umaimah dake zagin Munawwara yarinyar maqotansu dake shiga tana daukar mata Mu'ayyad din, ta tasata a gaba tana zagi saboda ta riqeshi ya zille ya kifa da baki,
"Wai ke baki san tsautsayi ba tana sane zata bar shi ya fadi ne ko yaya da zaki tasa yar mutane a gaba kina zagi, ki kiyaye ni kuma wannan zaman naki ma ya ishe ni haka yanzu Mijinki ya kirani daga yanayinsa na karanci akwai magana a bakinsa amma ya kasa fada, daman ina an kare dake tunda kika zo gidan nan banji ko sau daya kunyi waya dashi ba idan ma wata tsiyar kika tafka ya koroki gida tun wuri ki sanar damu a san yanda za'a magance ta"

Zumbura baki gaba tayi ta kalli Maman tace
"Ni me zanyi masa ya koroni tafiya yayi baya gaya miki bama shine yace mu dawo gida, wayata kuma ta lalace na fi so se ya dawo ya kaita gyara da kansa dan kar a batamun" ta fadi haka ne kawai amma gaskiyar magana kashe wayar tayi kamar yanda Rufaida ta bata shawara bayan ta qufuri aniyar bazata bishi ba.

Mama ta wuceta ba tareda ta kulata ba amma jikinta yana bata qarya Umaiman takeyi dan a saninta tafiya kota kwana biyu ce tare sukeyi dukda wani lokacin se an yi sulhu kafin tafiyar ta yuwu shine yanzu kusan sati biyu ace baya gari ta taho gida gaskiya akwai lauje cikin nadi.

Khalil kuwa bayan ya ajiye wayar sa shiru yayi yana tunanin ta inda ze hukunta Umaiman, rainin dake tsakaninsu ya fara yawa har ya zamana kenan be isa ya bata umarni tabi ba se abinda ranta ya ayyana mata koh dole kuwa zeyi maganinta.
Tun da ya bar Kano haquri kawai yakeyi musamman da yanda Umaiman ta sake chanza masa tun bayan data haihu saboda ingantaccen jego da kuma gyaran data samu ko tunaninta yayi se hankalinsa ya tashi, a lokacin ma abinda ya faru dashi kenan lokaci daya jikinsa ya farayi masa babu dadi shikadai yasan yanda yake bacci yake tashi ya gama saka ran zuwan nata shine tayi masa wannan cin kan yanzu besan ya zeyi ba, yanzu dole yayi qoqari yaje Kano a weekend din nan dan bashi da inda ze kai lalurar sa idan ba canba.

Wunin ranar gaba daya haka yayi shi sukuku harya tashi daga aiki ya koma gida, flat ne me daki biyu da duk wani abun buqata a ciki aka bashi yake zaune sanda aka kaishi masaukin a ransa har yana cewa anyi maganin mitar Umaimah da take cewa ita ba tafiya dashi ne bata so ba Aa haushinta zaman Hotel kullum tana kulle a daki kamar kaza yanzu ga gida nan ta samu kuma taqi zuwa.

Ruwa ya fara watsawa kafin yayi sallar Magriba data riskeshi a hanya, fridge ya bude ya tarar da babu wani abin kirki naci da ze qosar dashi yaja tsaki ya rufe, a yanda yake jin yunwa baze iya tsayawa dafa komai ba dan ya siyo kayan abinci duk a shirin zuwan Madam din tasa se kawai ya zari key din motarsa ya fita, a bakin Get din compound din sukaci karo da Sa'id Abokin aikinsa ya fito shima a shirye da alamar fita zeyi, gaisawa sukayi ya shiga qoqarin tada motarsa Sa'id din ya tsayar dashi, be fiya son doguwar magana tana shiga tsakaninsu ba saboda sam halinsa dana Sa'id din basu zo daya ba. Sa'id nada rawar kai ga shegen kule kulen Yammata kullum da macen da zaka ga tazo gidan gurinsa shi yasa sam Khalil baya bashi fuskar da wata magana me tsayi zata hada su data wuce gaisuwa.

"Mr Bayero fita zakayi ne, ur face shows that you are tired and
Famished, nima fita zanyi naci abinci idan babu damuwa muje tare motana na barta gurin gyara"
Badan ran Khalil yaso ba suka fita tare, a hanya se surutu yakeyi masa shi dai amsar sa Eh ko Aa ce dan gaba daya ransa a dagule yake, a gurin cin abincinma seda yaji kamar ya tashi ya bar gurin saboda shegen surutun Sa'id da yanda yammata suke ta zuwa yana gaisawa dasu.

Magana yaji daga gefensu, haka nan yaji kamar ya taba Jin muryar kuma jin suna hausa kuma kamar gulmar wani sukeyi haka kawai ya samu kansa da juyawa ya kalle su karaf idanunsu suka hadu, ya kalleta na tsahon seconds uku kafin ya dauke kai kwakwalwarsa na qoqarin tuna inda ya san fuskarta.
"Na gaya miki wallahi shine, ai bazan taba manta fuskar Guy din nan ba dan yayi bala'in burgeni" ya sake jin muryar data sakashi waigawar tana fada nan take ya tuno da inda ya sansu, yammatan daya taba taimakawa ya kaisu gida ne wata rana da daddare amma me sukeyi a nan? Ko daman yan duniya ne kawai raina masa hankali sukayi ranar da sukace biki suka zo.

Sallamar daya ji a saman kansa ta dawo dashi tunanin, me shegen rawar kance tana tsaye tana masa murmushi tace
"Sannu Malam, ka gane ni kuwa"
Kallon banza ya mata ita kuwa ko a jikinta se uban murmushi takeyi masa Sa'id ne ya mayar mata da martani yana cewa
"Zauna mana yammata kin tsaya kuma" seta ja kujera ta zauna har sannan tana kallon Khalil kamar zata lashe shi.

"Tunda kuka shigo na gane fuskarka, na cewa Hadiza kai ne tayi mun musu gashi ashe daman zamu sake haduwa tun waccen ranar nake Addu'ar Allah ya sa na sake ganinka dan ko godiya bamu samu damar yi maka ba waccen ranar" yarinyar ta fada tana yauqi kafin ya samu damar yin magana ta ci gaba da cewa
"Ni sunana Khausar, kai dai na san sunanka Khalil dan na gani a motar ka tun waccen ranar"

Tissue yaja ya goge bakinsa dan gaba daya abincin ya fita a ransa saboda surutun da tazo tana yi masa akai, shi daya sani ma Cornflacks yasha ya kwanta kawai da wannan fitowar da yayi haka kawai zata qara masa ciwon kai, tsaki yayi ya dauki muqullin motarsa tareda ajiye ATM card dinsa yana kallon Sa'id yace
"Gashi nan idan ka gama ka biya ni na wuce seka taho" yana gama fadar haka ya juya abinsa yana jin dayar yarinyar tana cewa
"Seki tashi mu tafi ai tunda kin gama zubarwa da kanki mutunchi aikin banza kina ta rawar jiki kamar kinga wani autan Maza".

Waiwayowa yayi ya kalli me maganar, waccen dayar ce wadda ta saka Hijabi ranar ya gane fuskarta ne saboda duk ta fisu haske fara ce sosai se yayi murmushi kawai wai Autan Maza.
Washe gari yana zaune a office aka kirashi da baquwar number, be dauka ba dan ba kasafai ya fiya amsa number da be sani ba musamman idan ya duba true caller yaga be san sunan me kiran ba.
Yana kallon wayar seda tayi masa kira biyar kafin message ya biyo ba ya dauka ya duba
"Khausar ce, ina fatan ka tashi lafiya" iya abinda ta rubuta kenan yaja tsaki bayan ya gama karantawa ya goge ya tabbatar Sa'id ne ya bata number sa nan take ya dannan ta a blacklist, to shi ko bufurwar zeyi me zeyi da ita babu abinda ta ajiye se shegen rawar kai.

Umaimah ce ta fado masa a rai kawai ya hasaso ace sun hadu ita da Khausar din wayaga yaqin duniya na uku ya tabbatar da haukarsu zata zo daya.
Wasa wasa Khausar ta mayar da kiran sa a waya dayi masa text kamar ibadah, data fuskanci yayi blocking layinta seta canza lamba, zata kira sau daya sannan ta tura masa da saqo safe da yamma, a cewarta idan da rai da rabo wata rana ze kulata abinda ta gayawa Hadiza lokacin da takeyi mata gorin rashin zuciya.
Aiki ne ya kaisu Lagos din qarqashin qunyar su me rajin kare haqqin mata da qananan yara, a qa'ida sati daya zasuyi amma tunda Khausar ta hadu da Khalil seda ta san yanda tayi aka qara musu lokaci saboda tace bazata tafi ba har seta samu soyayyarsa.

Sa'id ne yake qara mata kwarin guiwa akan hakan yana kuma bata tabbacin zata samu Khalil din indai tayi haquru, kuma shi ya gaya mata yana da Mata daya da Yaro hatta da irin sin da yakeyiwa matarsa da baqin kishinta daya samu labari ya gaya mata tace taji ta yarda kuma a shirye take data tunkari kowacce ya mace akan Khalil.

A bangaren Khalil kuwa be san ma tanayi ba dan ko messages din nata datake faman aikawa ba dubasu yake ba, shi yanzu hankalinsa gaba daya yana kan aikinsa ne saboda ayyukan da yake kula dasu suna da yawa tuni kuma ya yakicewa kansa Umaimah da tunaninta dan ya fuskanci idan ya daka ta tata baze moruba,lalacewa zeyi da ciwon bacin ranta kawai dan har yanzu da ake kusan kwana goma da zuwansa bata kunna wayarta ba kuma nemi wata wayar ta kirashi ba.

Da yammaci yana kan hanyar dawowa daga duba ginin wani company da sukeyi, a hankali yake tuqi saboda yanda gaba daya jikinsa bayayi masa dadi. Damuwa da buwatuwar mace a kusa dashi sun hadu suna neman saka masa ciwo a yankwanakin qarfin hali kawai yakeyi ya kuma yi rantsuwar seya koyawa Umaimah hankali abinda ya dakatr dashi daga tafiya Kano kenan dan a jiya harya hada kayansa ze tafi ya fasa. Tuqi yakeyi sam hankalinsa yayi gaba Allah ya taqaita ya tsayar da motar yayi gefe cikin wani ruwa daya kwanta saura qiris ya bige budurwar dake qoqarin tsallaka titi.

Dafe kansa yayi yana mamakin zurfin da yayi a tunani da har beganta ba, seya kashe motar ya fita ganin ta tsaya tana duba jikinta da alama ya watsa mata ruwan daya fada.
A fusace ta kalle shi daidai sanda yake bata haquri tace
"Dama se anyiwa mutum ba daidai ba ake bashi haquri ai, tun daga nesa dana hango motar nasan koma waye a ciki ba a daidai yake ba, duk yanda nayi qoqarin kauce maka amma ji sda ka batani da ruwan kwata haka kawai".
Chapter 73 · 0% Book details