← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 155 OF 267

Sashe 155

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon Khalil tayi da sam beyi kama da wanda yake tareda su ba, seda ta taba hannunsa kafin yayi firgigit kamar wanda ya farka daga bacci yana zare iso dan gaba daya wani tunani yakeyi da idan an rutsashi bazece ga abinda yake tunanowa ba.
"Lafiya dai Abban Mu'ayyad, ko wani abu yana damunka?" Umaiman ta fada tana tsare shi da ido. Gefe ya kalla ya ce mata

"Lafiya lau. Me kika gani?" Se ta sake zura masa ido tana qoqarin gano dagaske lafiyar yake ko akasin haka. Tun da Asuba ta lura kamar baya cikin nutsuwa haka daya koma bacci yanda ya ringa juyi har yana wasu surutai da bata gane abinda yake fada ya sake gasgata mata cewar bashi da lafiyar dan haka takai hannunta jikinsa tana cewa
"Yanayinka ya nuna baka jin dadi, ko zazzabi kakeyi? Ya kamata kaje Asibiti kasan dai ciwonka yanda yakeyi maka babu dadi gara ka tareshi tunda wuri".

Hannun da take taba wuyansa ya janye yana miqewa tsaye yace
"Keni lafiyata qalau fa wane irin zazzabi ana zaune qalau" seda yayi gaba se kuma ya waigo yana kallonta yace
"Yaushe ne naga kuna hayaqi keda yara kika ce na miyagune? Idan yana kusa dan kawo mun nima na turara".

Dariyar da bata shiryawa bace ta kwace mata ta shiga qyaqyatata babu ji babu gani har tana zamowa daga kan kurar da take. Khalil ya shaqa yayi fam yana kallonta, to meye abin dariya kuma daga cewa ta bashi hayaqin Miyagu se kace wanda yace wani abu daban. Cikin bacin rai ya kalleta yace
"Meye haka daga tambaya zaki tasani gaba kina mun dariya kamar wani mara hankali".

Seda ta hadiye dariyar dukda haka bakinta a washe tace
"To ai kaine da abin dariya, yau kuma da bakinka kake neman maganin Miyagu a ina kukayi arangama Allah sa ba a yawon zuwa Jeji Site suka qwamusheka ba. Ashe shiyasa jiya ka ringa surutai a bacci ai dana sani tun a sannan zan banka maka hayaqin suyi ta kansu" ta qarasa tana fashewa da wata dariyar. Tsaki yaja saboda takaici ba tareda ya sake ce mata komai ba ya shige daki abinsa. Tunani yakeyi da tace yayi surutai gaskiya ne ko wasa take masa? Amma dai koma yayin da gaske yasan ba abinda yake gani a mafarkin ne ya fada a zahiri ba dan idan haka, da yanzu ba dariya takeyi ba qila tashin hankali suke kwasa.

Ranar haka suka wuni tana zolayarsa daya gaji ya fice ya bar mata gidan. Ta isheshi da magana ga uban hayaqi data bulbulo ta kawo masa harda dakko bargo wai ya rufa abin yafi ratsa shi. Haka ko ya biye mata yayi hayaqin dan harga Allah ya gama yarda da cewar Humairan mayya ce dan wallahi har gizo take masa yana ganin suffarta na giftawa a gidan. Sau kusan uku yana daukar waya da niyyar kiran Mansur akan yaji salsalar wacece ita ya kuma tambayeshi ko yasan suna da alaqa da Maita se ya kasa. Tsoro yake kar magana ta koma mata ta qarashi cinyeshi a dare daya qila ta hada harda Mansur din dan dai shi ya tabbatar da ba yar uwarsu bace wannan be kuma san inda suka kwasota ba. Yasan kusan dangin Mansur kaf na uwa da Uba, Bare barine baqaqe ita kuma wannan gata nan kamar Zabiya daman tunda yaga kyanta yayi yawa yasan da walakin wai goro a Miya.

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

Page 58

Wasa wasa tunanin Humairah ya samu gurin zama a zuciyar Khalil. Haka kawai take fado masa, dan shi hayaqin da Umaimah ta samu nayi tana faman banka masa a maimakon ta sakar masa kurwa ma qara damqe ta tayi. Cikin qasa da sati biyu tsabar tunaninta har rama yayi abinda yasa hankalin Umaimah ya fara tashi kenan harta kasa daurewa ta sanarwa da Hajiya halin da ake ciki dan da gaske ta yarda da cewar Mayun ne suka kama mata Miji. Hankalin Hajiya ya tashi itama, babu shiri ta bazama karbo masa rubutu dasu hayaqi a cewarta babu wasu Mayu sedai Mahassada da masu kambun baka ne suke neman sakashi a gaba saboda daukakar da Allah ya kawo masa.

Khalil kuwa jinsu kawai yakeyi dan zuwa sannan lamarin tsoro yake bashi da gaske. Babu ranar Allah da ze kwanta ba tareda yayi mafarkin Yarinyar ba, kuma mafarki me nutsuwa dan wata rayuwa yake ganin suna shimfidawa irin wadda ko a sanda yake zirgillin Son Umaimah be hasaso musu irinta ba wannan dalili yasa ya qara mata Matsayi daga Mayya zuwa Aljana. Ya yarda kawai waddaya gani a Gidan su Mansur ba itace ainihin mutum dinba. Aljana ce ta bishi gidan ta samu damar dabaibaye tunaninsa ta jikin Humairan.

Da wuri ranar ya tashi aiki dan baya jin dadin jikinsa da baze fita bama to da akwai wasu takaddu daya taho dasu gida jiya kuma a ranar zasu aika dasu wani waje shiyasa ya fita. Yana tafe akan Titi kamar bayason tuqin da yakeyi, gaba daya tunaninsa ya rabu gida biyu. Da niyyar tafiya gida ya kwanta ya baro office amma kuma se gani yayi ya dauki hanyar gidansu Mansur. Wani mugun Azalzalarsa zuciyarsa takeyi tun kusan kwana biyu yakejin yana son sake ganin yarinyar. Magana yake so suyi dan ya fuskanci wace kalar mutumce ita kafin ya dauki Matakin gaggawa saboda nema take ta zauta shi. Sau biyu yana kuskuren kiran Sunan wasu da nata gara yayiwa tufkar hanci ya roqeta ta fita daga rayuwarsa tun abu be tabarbare ba.

Seda ya kai qofar gidan kafin ya tsaya kuma yana tunanin idan ya shiga me zecewa Maman? Bama wannan ba yana iya cewa gaidata yazo to ita kuma yarinyar ta yaya har ze samu damar magana da ita dan bayaso Maman tasan abinda ya kawo shi. Rasa mafita yayi wata zuciyar na gaya masa ya juya kawai yaci gaba da binta da Li'ilafi inda zuciyar dake mararin ganinta ta hana faruwar hakan dole ya saduda ya balle murfin motar ya fita Habibu dake zaune da Abokanan sa a Majalisa yana hangoshi ya taso dan daman tun tsayuwar motar yake kallonta kamar ta Khalil din amma beyi gaggawar tashi ba.

Cikin girmamawa ya gaida shi ya amsa yana tambayarsa makaranta yace masa yazo kawo SIWES letter nr gobr zero koma Dutsin Ma din. Tare suka shiga gidan. A falon Mama ya zauna Habibu ya wuce dakinta da niyyar ya kirata sukaci karo da Humairah dake shirin fitowa itama taci kwalliya kamar me shirin zuwa Biki.
"Ke ina Mama?" Habibun ya fada yana kallonta, cikin nutsuwarta tace
"Ta shiga gidan Hajiya Asabe, Anty Ummi ce ta haihu an dawo da ita gida nima can zanje tace idan na gama abinda nakeyi bata dawo ba na bita".

Kallonta yayi sama da qasa kafin yace
"Shine kika ci uban kwalliya haka ke zaki gidan surukai ko?"
Mayafin jikinta taja ta rufe fuskarta tana murmushi irin taji kunya kafin tace
"Kai Yaya wanka fa kawai nayi ko so kake na fita busu busu dani?"

"Yarinya in ma zaki dawo daga rakiyar wannan Cima zaunen tun wuri kiyi ga mutanen kirki nan suna Sonki kin zauna kina batawa kanki lokaci akan wanda bashi da Future" Habibu ya fada yana juyowa ya dawo gurin da Khalil ke zaune.

Humaira ko yanda kasan wadda Habibun ya durawa Iyayenta Ashar haka ta bishi da kallo kafin kace me hawaye sun fara zarya akan fuskarta. Khalil da tun fitiwarta yake kallonta yana kuma sauraran duk abinda suke cewa wata irin faduwar gaba yaji sanda Habibun yake zancen tana bata lojacinta akan wani bayan ga masu sonta da gaske, ji yayi kamar an kwada masa guduma maganar ta dake shi sosai kafin ya farfado kuma hawayen da ya gani suna sunturi a fuskarta suka sake jefa Zuciyarsa cikin wani yanayi.
"Yah Ilahi me yake shirin faruwa dani ne akan wannan yarinyar?" Ya jefawa kansa tambayar da babu me bashi amsa.

Maganar Habibu daya ajiye masa ruwa da Lemo ta dawo dashi daga kallon daya raka Humaira dashi se sharar hawaye take kamar wadda Habibu ya mara.
"Mamakin shagawabarta kake ko Yaya? Haka take fa yarinyar nan kallonta kayi idan taso sharri seta saka maka kuka dan ma Mama bata nan da yanzu ta hau sababi an taba mata Marainiya se kace akanta aka fara rasa Iyaye".

Maida kallonsa yayi kan Habibun yace
"Wacece ita?" Se Habibu ya zauna akan kujera yace
"Yar gidan Baba Sani ce Qanin Mama na Jalingo, kasan ya dade da rasuwa da Mamanta tayi aure ta maida ta gurin Hajiya ita kuma kasan ba Lafiya ta cika ba shine Mama ta dakkota bata fi shekara biyu a nan din bama itama Maman tata ta rasu, shikenan fa Mama ta dauki Son duniya ta dora mata ni da nake Autan ma ta kwace mun Matsayi se yanda tace a gidan nan Mama takeyi idan kuwa kana so kaga bacin ran Mama ka taba Humairah shiyasa ta daure mata gindi take son ranta a gidan nan".

A duk surutan Habibun babu abinda ya tsinta se Kalmar Marainiya data rasa uwa da Uba. Wani Tausayinta yaji ya masa rubdugu ya kanainayeshi. Tun Asalinsa shi daman me tausayin Marayune, ya taso cikin gata ya rasa Mahaifi sannan ya dandana dacin wannan rashin Mahaifin shiyasa idan yaga Maraya yake tausaya masa to sedai ita tausayin nata a na daban ya fado masa. Surutu Habibu yaci gaba dayi shidai jinsa yake amma babu tabbacin yana fahimta dan zuciyarsa tana ga son sanin Halin da Humairan take ciki, ta dena kukan ko tana ci gaba dayi?
Chapter 155 · 0% Book details