← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 165 OF 267

Sashe 165

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sauke kansa qasa yayi yana murmushi yace
"Shekararta Sha bakwai fa Hajiya, in zan tuna su Jalila sanda aka musu aure ai duk basu wuce haka ba muna gama secondary kika ce aure za'a musu kowa taci gaba a dakinta to itama hakan ne bana ta qare makaranta zata ci gaba a nan idan tazo".

"Toh Allah ya tabbatar mana da Alkairi yasa zamuga lokaci, amma ka zauna da Matarka ka sanarwa mata ta lumana dan Allah bana son wannan tashin hankalin kodan Halin da take ciki" Hajiya ta fada ganin Khalil na nemanya baro mata aiki. Miqewa yayi ya dauki hularsa yayi mata sallama ya fita ransa fes, ita ce zata iya kawo masa cikar a cikin tafiyar tunda kuma ya gyarota duk wani wanda ze zo da matsalarsa me sauqi ce.

Dakinsa ya koma seda ya cire shaddar jikinsa kafin ya shiga kiran Humairan dukda bashida tabbacin zata dauka. Yana jin alamar ta daga yayi murmushi, kusan minti biyu yaji batace komai ba amma yanajin fitar numfashinta kamar irin na wanda take a tsorace ko wani abu
"Yammatana babu ko kira kiji ya naje gida ko?" Ya fada yana zama a bakin gado. Shiru tayi bata ce komai ba, ya ringa janta ta da magana har seda ta fara amsa masa da Eh ko Aa, wato tunda ya kallafawa kansa soyayya da ita ya koyi yanda ake tafida masu qananun shekaru kamarta shiyasa be sha wahala ba gurin shawo kanta harta bude baki suka shiga hira kamar babu abinda ya faru, cikin dabara yake sake jaddada kansa a gurinta tareda yi mata alqawarurruka na yanda ze kula da ita ya riritata idan har ta bashi dama ta zama tasa.

"Amma Yah Khalil Anty Umaimah fa? Na tabaji Anty Nusaiba tana fadar kishine da ita sosai, ni daman tun Asali ina tsoron Kishiya...."
"Aisha" ya kira sunanta da dole tasa tayi shiru da maganar da takeyi, jin tayi shirun ya sakashi ci gaba da cewa
"Ki fadamun tsakani da Allah kina so na kuma zaki aureni?"

Shiru tayi saboda yanda tambayar tayi mata girma, dukda har zuciyarta amsar tambayarsa 'Eh' ce amma bata jin harshenta ze iya furtawa saboda kunya
"Kinyi shiru ki bani amsa" ya sake katse mata tunani, kamar tana gabansa ta shiga mutsu mutsu tana so tayi maganar amma ta kasa se ji tayi yace
"Idan ba zaki fadamun a waya ba zan dawo yanzu se ki fada mun face to face"

"Aa karka dawo, ni wlh kunyarka nakeji" ta fada kamar zatayi kuka. Se ya saki murmushi ya ce
"Toh ina jinki ki gaya mun, kina sona? Kuma zaki aureni?"
Seda taja numfashi ta ajiye, ta kasa hana kanta cikin sanyi kamar me rada tace
"Ina son Ibrahim, kuma zan aure shi".

Kamar wanda ta kwararawa ruwan qanqara haka yaji wani sanyi ya ratsashi, qasa yayi shima da muryarsa sosai yace
"Dagaske kike? Kin yarda na turo neman auranki ko wanne lokaci?"

"Eh, amma ba yanzu ba ai sena gama makaranta na qara girma nan da shekara hudu" ta bashi amsa cike da sakalci se ya saki dariyar da be shirya ba yace
"An gama yarinya tunda har kika fada da bakinki kin Yarda ai kin gama mun komai insha Allahu kuma ba zakiyi dana sanin zabata a matsayin abokin rayuwarki ba" daga haka sukayi sallama ya kashe wayar. Cike da doki da murna ya fita daga gidan, seda yayi sallar Magriba kafin ya sake kiran Mansur yana dagawa kuwa ya shiga yi masa masifa akan ya dameshi.
"Kai qyaleni Mama tana kira idan mun gama waya zan kira ka?" Mansur din ya fada jin Kiran Mama na shiga wayarsa.

MANSUR
A rude yake cewa
"Mama Khalil? Khalil dai Abokina kike nufi ko wani daban?"
"Khalil nawa kake dasu Mansur da zaka wani kidime se kace wanda aka gayawq Sharri. Zancen aure fa nayi maka abin Alkhairi Amininka nason yar uwarka ai abin ka runtuma da gudu ka shiga Harami kayi sujuddushshukur ne amma ka tsaya kana wata barbarar baki. To shidin dai Ibrahim na gidan Alhaji Bayero, daman na gaya maka zaryar daya tsira a gidan nan duk zatona ma Qaninsa yakewa kamu ashe shi ta kansa yakeyi to yau dai yazo har gidan nan ya gaya mun da bakinsa yana sonta kuma sun dade suna soyayyarsu itama na tambayeta tace mun tana sonsa to me yayi saura kuma in ba muji daga gareshi yaushe yake son Auran ba kawai ayi a gama kowa ya huta. Daman na gaji da wannan yaron dake mana zarya, yau fa har Marinta yayi a qofar gida saboda ya ganta da Khalil din idan aka daura mata auranta ta tafi ba shikenan kowa ya huta ba yaje canya qarata da Rashin hankalinsa da zafin rai" Maman ta tare Mansur,

"Gaskiya Mama in dai Amincewata ake da buqata toh ban yarda ba. Mama Khalil fa? I mean ba shine me matsalar ba Mama kinsan Mahaukaciyar da yake zaune da ita a matsayin Mata kuwa kinsan wacece Umaimah da ita kike so a hada Humairah kishi?
Toh wlh ko Unaizatu bata isa tayi zaman kishi da Umaimah ba balle Humairah da a haihuwar Qauye ta kusa haifarta sedai idan kun shirya saka yarinya a masifa da bala'i to wannan kuwa idan ba haka ba tun wuri ki gaya mata ta kama kanta babu ita babu shi yaje can ya nemi mata amma ba'a gidan mu ba".

"Toh naji abinda kace amma ni sam banga wata hujja da za'a ce za'a hana Khalil auran wannan yarinyar ba. Kai da kanka kace mutumin kirki ne tun yarinta har girma tare kuke halinsa babu Wanda baka sani ba sedai ka gayawa wani to me kuma ake da buqata bayan haka tunda an samu kyakykyawar shaida akan Ma'auri ina ruwanmu da wata matarsa ita zata aureta ko akanta zata zauna?" Mama ta fada cikin Halin ko in kula. Mansur ya dafe kansa, yasan Mama da bala'in kafiya akan abinda tayi niyya sannan ba tun yau ba tun kafin qannensa su gama aure take nuna sha'awar Khalil dinya nemi wata daga ciki tasha yi masa magana akan shi ya samu Khalil din da maganar ya bashi daya daga cikinsu amma yaqi, yakance mata
"Ai Mama duk ya sansu idanda akwai wadda takr burgeshi a ciki da kansa ze magantu base na kai masa tallansu ba"

Gashi yanzu ta samu cikar burinta kuma akanyar da take da ita kamar tsoka yasan kafin a shawo kanta ta gane illar da hadin yake tattare dashi za'a sha wahala. Haba Umaimah fa, babu ta yanda za'ayi ya bari a cuci rayuwar Marainiyar Allah a hadata da wannanmara tunanin da tsaf zata salwantar da ita a banza kuma shikansa Khalil din babu uwar abinda ze iya yi akai.
Magana Maman take masa amma yana canya lula duniyar tunani seda ta sake cewa
"Duk abinda Zakayi sedai kayi shi amma dan kaji aure ne babu fashi da yardar Allah gara ma ka saki ranka kayi fatan Alkhairi"

"Shikenan Mama, Allahya zaba mata mafi Alkhairi" ya fada saboda ya datse maganar se kuwa tayi saurin cewa
"Ai yama zaba mata sedai kace Allah ya tabbatar musu da Alkhairi"
"To Allah ya tabbatar musu da Alkhairi" ya sake fada daga nan sukayi sallama.
Layin Khalil ya shiga kira harta qaraci Ringing be daga ba ta katse ya sake kira nan ma haka dole ya haqura yasan idan ya gani ze kirashi zasuyi magana kuma dole ya janye qudurinsa dan inya kasa fahintar da Mama ta hana aurannan tota qarfin gaske ze saka Khalil dinya janye shi ai dole ta haqura.

UMAIMAH
Ganin da tayi zagayen dakin baze bata Mafita ba ya saka ta zura dogon Hijabi a jikinta ta zari muqullin mota ta fita. A karon farko tunda tayi aure ta nufi gidan Maman Asad da niyyar kai mata damuwarta ta kuma nemi shawararta. Kusan suma tayi a bakin qofa sanda ta shiga gidan, kunnuwanta suka jiyo mata Maganar Baban Asad din yana gabatarwa da Hajiyayyen wata yarinya dake ta faman sunne kai a matsayin qanwarta wai tazo duba Asad daya samu Tsautsayin karaya. Kasa qarasawa ciki tayi ta kafe a bakin qofar tana binsu da kallo daddaya, mamaki ya kasheta ganin ita Maman Asad din ko a jikinta tanata jan yarinyar akan tasha ruwa da lemon da aka kawo mata, tana qoqarin zuba mata ne ta lura da Umaimah dake tsaye, seta dakata tana cewa
"Aa ke kuma daga ina haka kika cakare a bakin qofa? Ki qara so ciki ki zauna mana".

Qarasawar tayi cikin kamar yanda tace ta nemi kujerar data fi kusa da qofa tanzauna har sannan tana kallon baquwar. Baban Asad cikin barkwanci ya kalleta yace
"Aa me ciki ce da yamma sakaliya haka?" Banza ta masa idonta qur akan yarinyar data dago tana gaisheta, itan ma dai bata tanka mata ba Maman Asad ta hade rai tana kallonta tace
"Bakiji tana gaisheki bane Umaimah?"
"A matsayina na qanwar uwarta kota ubanta da zata gaidani? Nace ina buqatar gaisuwarta ne ko yaya ko kinji na kulata dana shigo gidan?" Ta hayayyaqowa Hajiyayyen se Baban Asad ya miqe baquwarsa ma ta mara masa baya yana kallon Maman Asad yace
"Sweetheart bari na mayar da honey gida, akwai abinda kike da buqata ne na taho muku dashi?"
"Babu komai Habibi Allah ya dawo da kai lafiya, qanwata nagode kwarai ko gaida mutanen gida Allah ya bada ladan ziyara ku jirani ina zuwa" Maman Asad ta fada tana shiga dakinta. Ita dai Umaimah baki kawai ta bude tana kallo ikon Allah da wannan yammaci. Hajiyayye ta fito da wata leda fara me tambarin wani company a hannunta ta miqawa yarinyar taqi karba tana ta barshi Baban Asad ya karbar mata harda cewa wai kunya take ji
"Se Anjima, Anty ki gaida gida" yarinyar ta sake fadawa Umaimah kafin ta juya ta nufi qofa
Chapter 165 · 0% Book details