← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 167 OF 267

Sashe 167

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wallahi aikinsa yasha banban dana sauran Malamai da kika sani, aiki yake sadidan gashi kamar yankan wuqa musamman irin nakin nan me sauqi farraqu kawai za'ayi masa da duk wasu yammata su dena burgeshi ke kuma a qara miki tasiri a zuciyarsa ta yanda baze ga wata mace da qima ba idan bake ba kuma ki mallakeshi shikenan fa ba wani abu me yawa za'ayi ba" Muryar Safina ta katse mata tunani seta saki ajiyar zuciya ta na kallonta tace
"Safina babu wata hanya dole se wannan?"
"Babu Umaimah wai ma meye ne ke da zaki ce ba zaki gidan Malam ba? Duk fa macen da kikga ta isa a gidanta yanzu tana yanda taga dama to tana da Malamin daya tsaya mata. Allah na tuba mu ina muka leqa ma hamshaqan mata da suke bin Bokaye fa wasu Niger ma da su chadi suke fita dan neman biyan buqata ai ki saki ranki kawai in har kina so Ki samu khalil ke kadai wallahi se kinyi abinda akeyi ita wadda ze kawo din kika san nawa ta kashe kafin ta samu kansa balle ace ta shigo gidan ai se kin zama sorry Umaimah".

"Bari naje Safina kaina sarawa yake yo zamuyi magana" ta fada tana miqewa dan bata ga mafita a zancen Safinan ba. Har Get ta rakata tana sake jaddada mata da tazo suke gurin Malam zata sha mamakin yanda abubuwa zasu tafi tace mata toh se tayi shawara. Tana tafe a mota tunani barkatai sun cika mata kai ta rasa ina zata kama, idan ta tuna Khalil ne da bakinsa ya gaya mata maganar nan se taji kamar ta kurma ihu. Abu daya da ta sani dashi ko a cikin wasa baya mata qarya dan haka yanzu ta tabbatar da abinda ya fada gaskiya ne kenan sannan abinda Hajiyarsa tayi mata ya sake tabbatar mata da hadin bakinta ake komai.

Hannu ta saka ta share hawayen da ya zubo mata kafin ta gangara gefen titi tayi parking. Ita yanzu gurin wa zataje? Yan gidansu duk bakinsu daya haquri za'a bata kai bama taso su sani dan tsafgoya masa baya zasuyi ba zasu hana ba ga Safinan da take zaton zata sama mata mafita tana kawo mata wani zancen shirme. Wayarta ta dakko ta shiga numbobi tana dubawa, akan lambar Rufaida ta tsaya, tafi minti goma tana tunanin ta kirata ko yaya kafin daga qarshe ta runtse ido ta kira

"Allah ka nuna Annabi, yau Umaimah da kanki kike kirana" Rufaidan ta fada cike da murnar ganin kiran tsohuwar Aminiyar tata.
"Rufaida kina gida ne?" Ta tanbayeta ba tareda ta tsaya wata doguwar magana ba se Rufaida tace
"Wallahi bana gida, muna garinsu Habibi Mahaifinsa ne ya rasu yau akayi sadakar bakwai se zuwa jibi zamu taho lafiya dai wani abun ne ya faru?"

"Babu komai, Allah ya jiqansa dan Allah idan kin dawo ki gaya mun ina so mu hadu ne"
"Babu damuwa da mun dawo zanzo gidan in sha Allah, amma lafiya naji muryarki da damuwa haka idan abun sauri ne muyi magana a waya mana?"

"Uhm, ki bari kawai idan kin dawo mayi maganar" ta fada daga nan ta kashe wayar. Gida ta koma, babu wanda ta kula harda yaran dake ta mata sannu da zuwa da suka bita daki ma fafarosu tayi ta korosu waje. Ranar kwanan zaune tayi tana saqe saqen mafita, ba zata iya jira har se Rufaida ta dawo ba kuma bata jin zata dauki shawarar Safina dole ta nemawa kanta mafita kota wanne hali.

Cikin dare ta kasa bacci, juyi kawai takeyi gaba daya ta kasa tunanin ma, a hankali ta miqe ta fita daga dakin, cikin sanda ta haye saman, a jikin qofar dakinsa ta jingina tana jiyo shi yana magana da alama waya yakeyi
"Nayi maka Alqawari Mansur zan kula da yarinyar nan babu kuma abinda ze sameta, ina sonta ni kaina bansan yanda akayi ta shiga zuciyata har haka ba kuma bana zaton akwai abinda ze ciremun wannan son nata daga zuciyata kadai san yanda nake akan abinda nake so toh dan Allah ka ajiye komai da duk wata magana a gefe kayi mana Addu'a in sha Allahu nida Humaira auranmu har Aljanna".

Guri ta samu ta zauna tana jera numfashi, wato Mansur ne, seda ya tabbatar da abinda yake fada na cewar se an mata kishiya ko kuma Humaira idan zata tuna daidai yarinyar da Mamansu Mansur din take ruqo ce. Daman haka nan taji jininta be hadu da yarinyar ba tun a karon farko data fara ganinta saboda Kyan yarinyar yayi yawa gata da wata siffa me daukar hankali da dik in ka ganta se ka sake kallonta. Daman zuwan da yakeyi gidan yace saqon Mansur ze kai abinda yake zuwa kenan ko gara da Allah yasa taji komai ashe ma ta gida ce toh wlh zataje har gidan, se tayiwa Hajiya Hauwa Tijarar da ko me suna Khalil ya sake zuwa neman auran yarinyar bazata bari ta kula shi ba. Haka ta qarasa daren cikin shirya irin rashin mutunchin da zataje tayi a gidansu Mansur kafin daga bisani ta dawo kan uban gayyar dan ba raga masa zatayi ba.

Washe gari fuska a washe ta farka abinda ya matuqar daurewa Khalil kai ganin da kanta ta shirya masa abin kari kai bazaka ce wani abu ya faru jiya ba. Kallon abincin ya ringayi ya kasa ci, kwanaki yaji an ce wata ta sakawa mijinta maganin bera a abinci sabida ze mata kishiya wannan tunanin ya hanashi taba duk abinda ta ajiye din har seda ta zauna ta zuba nata ta zubawa yara suka fara ci kafin ya sauke Ajiyar zuciya ya shiga shima.

"An jima zamu fita, yau zumunchi nake ji zamuje mu gaida Hajiyar su Mansur wlh na manta rabon da naje gidan tun jiya kawai take fado mun a rai" ya ji maganarta a tsakiyar kansa ai be san sanda ya kware ba ya shiga tari baji ba gani Umaimah na tsaye kansa harya lafa zagi ta dura masa su a zuciyarta sunfi kala dubu, ya dago ya kalleta da idonsa da sukayi ja saboda kwarewar da yayi yace
"Gidansu Mansur kuma yau? Sau nawa nake ce miki kije ki gaishetan kike qi se yau zakije zakije?"
"Toh dai qorafi ya qare yanzu dai yau zanje kuma daga yanzu in sha Allah zan ringa leqawa ina gaidata ai Mama nada kirki nice ma da naqi Sakin jiki da ita" ta bashi amsa tana komawa gurin zamanta. Shiru yayi, yasan dai baze yuwu ace tasan wadda yake nema ba amma kuma baze so taje gidan ba saboda gujewa sammatsi yanzu idan ya hanata nan na ya saka kansa a matsa dole tabi ba'asin dalilin hanawar to shi yaya zeyi yanzu?

Haka ya qarasa tuttura dankalin data zuba masa ya fita tareda yara da ze sauke a makaranta bayan ya bata kudi akan ta bawa Maman idan taje.

Ko Awa daya beyi da fita ba itama ta fice bata kuma zame ko ina ba se gidan su Mansur. Mama na zaune A tsakar gida ta kunna Radion ta tana ji Humaira na kitchen tana hada musu abin karyawa Umaiman ta fada musu kamar dirar Kirsimeti.
"Subhanallahi waye haka?" Mama da yanda a bugo qofa ya tsoratat ta fada tana miqewa, ganin Umaimah tsaye yasa ta saki ajiyar zuciya tace
"Au kece tafe da safiyar nan qaraso ciki mana kika kafe a bakin qofa".

"Ba zama ya kawo ni ba baqar Annamimiya mara tsoron Allah, wato saboda tsabar son zuciya da kwadayi dan kinga Allah ya horewa Mijina abin duniya shi yasa kike so ki laqaba masa wata shegiya da ba'asan Asalinta ba ko ku dandali arziqi? Bautar da Ubansa yayi muku da wadda shima yayi da Danki duk bata isheki ba se kin hadashi aure da yarki? To bari kiji Hauwa na rantse da wanda yake busa mun numfashi babu wanda ya isa yayi wannan hadin, idan kuma kince se anyi to ki tabbata kin hado ta da Likkafani da duka sauran kayan jana'iza dan kuwa daren da aka kaita cikin gidan Khalil a kabari zata qarasa shi".

Qarar kwanuka da suka zube ta saka Mama da Umaiman waiwayawa suka kalli Humaira dake tsaye qofar kitchen ta zubar da kwanukan data fito dasu saboda tsorata da ganin yanayin Umaimah da kuma maganganun da take fada jikinta se rawa yake kamar wadda Sanyi yake kadawa.
Wani banzan kallo Umaimah ta bita dashi sama da qasa kafin ta tabe baki tace
"Da alama wannan kazar kike shirin liqawa Mijina? To ki bar murna aikin Bokanki yaci dan nasan idan ba Asiri ba babu abinda ze burge Khalil a jikin wannan abar me kama da Muciya a tsaye ina tabbatar miki da duk abinda kikayi sena warwareshi, ke kuma idan kina son kanki da lafiya wallahi ko a mafarki karki qara tunanin Mijina dan idan ba haka ba ni nan se na zama Ajalinki, sena lalata na balbalta rayuwarki ta yanda har ki mutu kina danasanin sanin Khalil a duniya kiji da kunnenki ni nan Umaimah na isheki" tana kaiwa nan taja wani matsiyacin tsaki ta juya zata fita Mama ta tareta da cewa

"Mungode kwarai da ziyara, amma ina so ki sani shi aure lamarin ubangiji ne duk kuma wanda yace ze dakatar da faruwarsa rabo yana iya kashe shi ayi ko bayan ransa, ke yarinya ce har yanzu baki gama sani inda yake miki ciwo ba a rayuwa dan haka kibi a sannu" tana gama fadar haka ta kalli Humaira da Hawaye su ke mata zarya a fuska tace
"Wuce muje ciki" nan suka bar Umaimah tsaye kamar wadda aka dasa kafin taja qwafa ta sake ficewa fuuu tana shan alwashi kala kala akan Maman da Yarinyar, abun da yazo mata a rai shine fuskarta ta rudeshi dan haka dole ta dauki matakin lalatata ta haka ne zata sake kareshi daga dukkan wasu Mata ko Iyayen yara masu kawo masa tallan Yayansu.
Chapter 167 · 0% Book details