← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 256 OF 267

Sashe 256

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tun daga nan ta sake janye jikinta akan lamarin Khalil amma bata fasa tura masa da saqonnin ban haquri ba dan wannan ya zame mata dole, tana buqatar Afuwarsa data sauran Ahalinsa amma Khalil din ya shareta funfurus kamar baya ganin saqonnin Alhalin kullum ta turo seya duba ya karanta sannanya goge. A haka taci gaba da aikinta, Al'amarin zawarawa kuwa abin tun baya damunta har ya fara bata tsoro. A lissafe cikin qasa da wata biyu tayi Zawarawa sun kai Goma amma babu guda daya daya tsaya daga zuwa dayan nan basa dawowa. Dama duk wanda taga take taken ze zo mata da wata maganar blocking dinsa kawai takeyi ta dena biye musu tayi masifa tunda ta fahimci Al'amarin Mazan yanzu ya qazanta sedai kawai ace innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Fasadi yayi yawa a doron qasa, babu kunya babu tsoron Allah mutane sun maida zina Ado musamman ga Mazan aure da matan auran ma dan abin ya zarce yammata yanzu masifar ta girmama kuma babu tsoron Allahn daya halicci mutum qiri qiri suke zuwar mata da buqatarsu, ita dai batayi kalar yar iska ba haka nan bata shiga da take bayuynar da jikinta Hijabine kullum take bulalawa har qasa dan da yawan zawarawan seda suka mata qorafin shogar tata wai tana rage mata kyau sannan bata da sakin fuska ko sakin baki da ze saka suga lakwa lakwan da zasu zo mata da maganar banza amma a hakan dai bata tsira ba.

Da Hadiza kadai ta iya tattauna maganar wadda yanzu sun dinke sun zama Qawaye har gidansu take zuwa itace dai sau daya ta taka gidan Hadizan tana kuma bala'in jin dadin tarayyarsu saboda yanda take qaruwa da ita ta fuskoki da dama. Kasancewar Hadizan Lawyer gomnati Umaiman najin labarin kesa kesai a gurinta da suke qara sakata tsoron Allah ta kuma tsoraci duniya. Idan taji wani abun se taga ashe ita a iskancin ma ba abinda ta iya manyanta na gaba ta kuma godewa Allag daya bata ikon gano kuskurenta ta kuma gyara tun gabanin lokaci ne qure mata ba. Sanda take yiwa Hadiza zancen matsalarda take damunta game da rashin tsayawar Maneman nata sa kuma irin abubuwan da suke bijiro mata dasu dariya kawai tayi take ce mata

"Ki godewa Allah ki kuma cigaba da neman taimakonsa dan a dukkan al'amuranki, ba wayo bane ba dabara ba Umaimah muna cikin wani zamani da ubangiji ne kadai ze shige mana gaba. Karki sakawa ranki damuwa duk wanda kikaga yazo ya tafi ba mijinki bane babu kuma Alkhairi a tare dashi, in sha Allahu da sannu zaki rabauta da tanadin da ubangiji yayiwa bayinsa da sukayi kuskure kuma sukayi tuba na haqiqa karkiyi sauri a rayuwa labari na kadai ya isheki Misali, kina kallon abubuwan dana fuskanta a rayuwa qila badaban faruwarsu ba bazan dace da irin Mijin da kalar rayuwar dana samu a yanzu ba".
Jikin Umaimah yayi sanyi laqwas da kalaman Hadizan, koda ba da wata manufa ta fada ba amma maganar ta shafeta saboda duk idan za'a bada tarihin Hadiza da gwagwarmayar data sha tabbas seta fito a shafin mummunar qaddadararta.

Data sakeyiwa Rumasa'u Farar Aminiya maganar itama dai kamar Hadizan ce mata tayi ta share komai taci gaba da Addu'a in sha Allahu Alkhairi yana gaba da wannan tadan samu nutsuwa amma kwarzabar Mama tasa dan kumarin data farayi ya nemi guduwa, data dawo gidan zata kafa mata mitar wance ta haihu wance tayi kaza, tun ba da Hajiya ta kira Maman take gaya mata wai Bibi ta fara Al'ada ba ranar kam taga abu, Mama harda cewa seta jira su jera ita da Bibin suyi aure rana daya tunda taqi tsayar da Miji to ga yarta nan ta girma ko yanzu za'a iya kaita daki. Akayi katari ranar wani ya aiko sallama da ita ta fatattaki Yasir dayazo fada mata saqon Mama ta qara samun nayi seda Abba ya saka baki kafin ta barta ta shaqi iska me dadi a gidan. Kodan abinda Mama take mata da zata samu Miji ko wanene zatayi aure amma ta rasa, abinda bata sani ba duk wanda yazo da yan Majalisar qofar gidansu sun qyalla ido sun ganshi zasu bi baya su lalata komai ta hanyar bashi labarin qarya da gaskiya daya faru su kuwa daga nan su gudu se su zagayo mata da zancen iskanci.

Ire iren wadannan abubuwan suke qara jefata cikin damuwa idan ta tuna zamanta da Khalil a lokutan data ringa wukaqantashi da gayya tana hankadawa Matan waje shi. Me yasa bata taba yin wannan dogon tsinkayen ba, mata na waje suna farautar Maza wasu ma basuji ba basu gani ba matan ke jansu tana kallo irin haka na faruwa a gurin aikinsu ballantana irinsa a lokacin da yake cikin buqata badan tsarewar ubangiji ba ai da tuni Khalil yayi tambari a neman Mata amma ya kame kansa duk saboda ita magana me tsaho bayayi da mata hatta wanda suke ciki daya a gaban idonta se yayi mata wannan Alkunyar dan kar ranta ya baci duk irin halaccin nan da yayi mata amma ta kasa yi masa uzuri akan abinda ba haramci ba to da ace Khalil Matan banza yabi da qila idan ta gano take zuciyarta zatayi bindiga ta mutu dan ba zata iya hasaso irin tashin hankalin da zata shiga ba. Tayi Adawa da matar sunnah wadda suke da matsayi daya da ita har a gurin Allah ita kam wai ina hankali da tunaninta suka tafi sanda tana gidan Khalil? Soyayya da Kishin karya hadata da kowa ya rufe mata ido yasa bata tunanin komai se son zuciyarta.

KHALIL
A kullum cikin godewa ubangiji yake bisa ni'imar da yayi masa. Tabbas ya yarda da cewar sakamakon haquri Alkhairi ne mara iyaka. Soyayyar Umaimah, Auranta da rayuwarsu ya dauke su a matsayin jarabawa daga ubangiji haka haqurin da yayi da ita ba sakalci bane kamar yanda da yawa suke dauka dan a yanzu gashi yana dandanar romon dutsen daya dafa. A baya ya kanyi tunanin yanda rayuwarsa zata kasance ba tareda matar da yake tsananin qauna ba se gashi yanzu ya rayu babu ita na tsayin shekaru kuma babu abinda ya canza a rayuwarsa sema tarin alkhairai da suka dabaibaye shi.

Dukda dai lamarin zuciya da abinda take so amma bashida zabi illah yaci gaba da bata Matsayin uwar yayansa bawai Masoyiya ba. Samun Humaira da yanda Al'amura suka daidaita tsakaninsu ya sakeyin tasiri matuqa gurin mantar dashi kewarta da tunaninta dukda a wasu lokutan su kan motsa masa. Kewar Umaiman tana damunsa idan ya tuna wasu abubuwan dadi da suka wanzu tsakaninsu se ya ringajin tamkar yaje gareta musamman idan yaji suna hira da yaransa yanda tayi sanyi qalau da mu'amalarta na matuwar dukan zuciyarsa tana kuma bashi tausayi, idan yaje gidan ya ganta sanyi qalau se yaji wani iri kamar ya tsokaneta tayi buyaginta tafi kyau a haka amma yanzu ta zama wata Umaimah ta daban da ko yatsa aka saka mata ya tabbatar ba zata gatsa ba. Duk sanda yaso shagala a irin shauqin nan daya ya tuno da wasu al'amura da suka gabata tilas yake danne komai yaci gaba da shafa mata fentin da ganinsa tareda ita ne kadai ze hana zuciyarsa karaya ta koma mata a karo na biyu. Allah ya sani yana qaunar Umaimah Al'amarin da yakeji a kanta baze misaltu ha ba kuma ya tsammanin ze jishi tareda wata mace amma ya haqura da ita tunda ya haifu dan Halal ne shi ba shege ba yanda tayi iqirari.

Qofar bandaki aka bude Humaira ta fito daure da Towel babba ta yafa wani qarami akanta, Khalil dake kwance daidai ya lula duniyar tunani qarar qofar ta farkar dashi ya kalleta, a tare suka saki murmushi kowanne da ma'anar nasa a ransa ya miqa mata hannu ta noqe kafada seya fashe da dariya sosai ita kuma ta shagwabe fuska kamar zata fasa kuka tana cewa
"Dole kayi mun dariya mana tunda ka kusa jawomun aiki, ni wlh bazan yarda bama se munje an duba ance babu komai sannan zan yarda mutum babu tausayi daga yin Arba'in dina baka ko duba ni yar yarinya ce kayita cin zalina ai Mala'ikun Allah suna kallonka"

Dariyar ya qarayi har yana shirin kwarewa ya tashi zaune yana cewa
"Ji wata magana fa yarinyar nan, Fushi zumbura baki da qunquni babu irin wanda ban gani ba a gidan nan ke kin rainani sannan yanzu tun ba'aje ko ina ba kin karaya dama ai na gaya miki yatinya lafiyata ta miki yawa baki yarda ba amma yanzu gashi kin fara gani a shekara biyu kinyi yan uku, to ki shirya wasu biyun suna tafe nan da wata tara dan aikin dana sha jiya ba a banza ba nasan nayi babbar Ajiya".
Chapter 256 · 0% Book details