← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 228 OF 267

Sashe 228

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Oh kema tayi nasarar yaudarar zuciyarki kenan to bari kiji lafiyarta qalau tana kuma sane da duk abinda takeyi. Saboda tasan ta sabayi tana sha shiyasa bata shayin yin komai amma ki sani ni tsakanina da ita babu duka babu zagi ba kuma zan mata mugun kalami ba sedai yanda take zuba iskancinta haka nima zan hukuntata cikin ruwan sanyi har seta ladabtu. Har yanzu Umaimah bata san da tayi ba daidai ba balle ta nuna nadamarta kina Jin inkarin da takeyi na mun tsaneta a zatonta tsana ce tasa ake mata abubuwan da ake matan amma kwakwalwarta bata bata lissafin me tayi ko me takeyi da ya saka a tsane tan ba? Tsayin shekara guda tana zaune a cikin gidan nan ko gaisuwarta ba ma amsawa bansani ba ko ke amma nidai rana daya yarinyar nan bata tareni ta bani haquri akan qin amsa gaisuwarta ba saboda abin be dameta ba a maimakon haka ma seta dena gaba daya se yanzu data ke neman sassauci ne ta dawo da gaisheni kinga ashe da hankalinta tunda tasan idan tana da buqata ta kwantar da kai to muci gaba da tafiya a haka daga nan har ran da qasa zata rufe idon daya daga cikin mu muddin bata hankalta tasan tayi badai dai ba ta nemi afuwa akan hakan bazan rangwanta mata ba dan ba ita kadaibace yar banza in fact a gurina ta gaji kafiyar tata kinga bata fini iyawa ba" Abbaya fada daga haka ya dauki ruwan shayinsa yaci gaba da kurba. Kasa ce masa komai Maman tayi se hawaye da take sharewa lokaci lokaci, ita ba wai tana nemawa Umaimah sassauci akan wani abu bane amma maganar abinci takeyi be kamata ace za'a horata da Yunwa ba ai ko ayyukan gidan idan bata qoshi ba ba zata iya ba sannan wani ciwon ze iya kamata.

Yana lura da hawayen da takeyi kuma abin ya dameshi amma baya so ta bari rauninta ya rinjaye ta su kasa Nunawa Umaiman kuskurenta. Cikin yanayin rashin jin dadi yace
"To yanzu da kike wannan hawayen na menene me kike so ayi?"
"Nidai ka janye Allah ya isan da kayi mata akan abinci ka bari taci gaba da cin komai kamar sauran yan uwanta" Maman ta fata cikin kuka kamar wata yarinya se abin nata ma ya bashi dariya ya murmusa yace
"To yanzu so kike na dauki asarar abincin data mun kenan a zubar dashi a shara wannan ai Almubazzaranci ne"
"Ni ba haka nake nufi ba yanzun ma ai tana ci jiya shi taci yanzu ma gashi can taci tana amai ai kaga taji maganarka koda ace zata ci gaba da ci harya qare amma kayi mata lamuni idan ta dafa wani abun taci ba iyakar wancan ba" Maman ta sake fada se ya nisa yace
"Shikenan taci darajarki amma seta biyani kudin shinkafata dan ba zan dauki Asaraba in yaso tayi duk yanda zatayi da ita kirawo mun ita" seta miqe ta fita, Umaimah na nan zaune a qasa tana numfarfashi tunani takeyi yanzu da tana gidanta abinci dai se wanda ranta ya raya zataci ko basu da abu duk inda yake Khalil ze tafi ya nemo mata danye ko dafaffe muddin tace tana so amma yanzu a cikin gidan ubanta yunwa na neman ta halakata.

Dakya ta iya tashi tabi bayan Maman, tayi tsuru tana sauraron Abban da yake cewa
"Mamarki ta nema miki afuwa akan abinci naji kuma nayi amma akan sharadi se kin biyani kudin abinda kika lalata sannan karki kuskura ki zubar ki san dai yanda zakiyi dashi"
"Na yarda wlh Abba zan biyaka" ta fada cikin rawar murya se yayi murmushi kawai yaci gaba da cewa
"Sannan abubuwan da kikeyi na ganin dama inaso kisan cewar dolenki ne kiyi bawai kamar yanda kike dauka ba karki kuskura na sake maimaita miki maganar nan a cikin gidan nan" ya zaro dubu biyu ya miqa mata yace
"Ki bayar a siyo miki Cefane Miyar Taushe zakiyi da dare idan na fita zan aiko da Qashi a qara da Nama" seta tsaya ta kasa karba ya watsa mata kudin baki na rawa tace

"Abba ai yau girkin Anty ne bana Mama ba"
"Dana tashi baki Umarni kinji nace girkin uwarki kadai zaki ringayi? In kinga dama kiyi idan kuma kinga akasin haka karkiyi ita Saratun ma bata nan Uwarki da sauran yan uwanki su zauna da yunwar dan ban yarda wani ya girka abinci cikin gidan nan ba idanba ita ba kuma ki hado lissafin kudina ki kawo mun yanzu ina jiranki" Abban ya fada a fusace kan ta na qasa tana Hawaye ta tabbata dai ta zama boyi boyi kawai a gidan bata da hutu daga girki se shara da wanke wanke. Cikin kuka ta kalleshi tace
"Toh dan girman Allah Abba bada itace ba wlh har cikin kwakwalwata nake jin hayaqinga idona duk ciwo sukeyi ka barni na ringa Amfani da Gas din"
"Ban yarda ba sedai idanda kudinki zaki ringa zuba Gas din" ya bata amsa kai tsaye har tana zabura kuwa tace
"Na yarda sannan Abba Shara ma zan samo Almajirai zan ringa biyansu sunayi "
"Ai shikenan kiyi duk yanda yayi miki" ya sake fada yana wani murmushi tareda girgiza kai, su zubasu gani ai duniya tafi bagaruwa iya jima daga haka ya sallameta ta fita tana jinta sakayau ko babu komai an rabata da wahala tunda ya yarda ta samu mataya.

Indomie ta debo a store ta samo Almajiri ya siyo mata sardine ta dafa abarta taci tayi nak har wani sabon qarfi takeji saboda sassaucin data samu a wautarta. Ta dumama Dafadukanta tsaf ta bawa Almajirin tace ya fita da ita ya rabar sannan ta ce masa ya ringa zuwa kullum safe da yamma ze ringayin shara da wanke wanke suka tsadance yanda zata ringa biyansa ya zama girki kadai ne aikinta. Cike da kuzari ranar ta ringa aikinta tayi musu Dafaduka da rana amma ba irin waccen ba tana saukewa ta mayar da Ruwan Tuwo haka ta tuqa musu shi sama sama duk dan kar hannunta yayi kanta danma shinkafar me laushi ce kuma tasha ruwa zata kwashe a kula Mama tace mata karta kuskura, dole ta dakko Leda ta malmala shi yanda akeyi ita dai Maman kallonta kawai takeyi dan gaba daya rayuwar Umaiman tausayi take bata. A maimakon ta roqi Mahaifinta ta bashi haquri yayi mata afuwa saboda shedan na mata kururuwa tana ganin ta tara Abin duniya ai shikenan yau da gobe dai tafi qarfin wasa ko nawa take ganin tana dasu wata rana zasu qare.

Haka rayuwa taci gaba da gangarawa Umaimah, Yasir tasa ya kira mata Me POS din qofar gidansu tunda an hanata Fita ta bashi ATM dinta ya duba mata balance tunda babu waya, dubu dari uku da Hamsin da biyar take dasu a cikin account dinta na UBA, dayan first bank dinta bata da ATM tunda yayi expire bata sake wani ba ta san ma kuma ba wasu kudine a ciki ba sunyi yawa sukai dubu Hamsin dan a nan take Saving kudi kuma su ta tattara ta biyewa Safina suka ringa rabawa Malaman qarya gashi yanzu bata ga tsuntsu bata ga tarko. Tas tace ya cire kudin ya bata ta ajiye su, ta debo akwatunanta na dakin Mama a cikin kayan ma ta samu kudade irin wadanda take ajiye wa cikin drawer kaf suka hado mata komai nata Mayukan shafawarta da yawa se zubar dasu tayi dan sun lalace ta debi abubuwan da zatayi amfani dasu yauda kullum ragowar ta hadesu ta rufe tunda ba fita takeyi ba.

Kwanci tashi Asarar me rai se gashi tun ba'aje ko ina ba Al'amura sun fara yi mata tsanani, kudin da take gani a hannunta suka sa ta sake miqe qafa tana yanda taso suka tasamma qarewa dan a cikinsu take hidimar komai da wadda ta zamar mata dole da wanda ta dorawa kanta ta siyan Gas da biyan Almajirin da yake mata wanke wanke da shara ga ciye ciyen banza da wofi baki ya saba da dadi kullum tana hanyar aiken Yasir siyan shawarma da Icream ko Kaza gashin Inji wadda ta sabaci a gidan Khalil a zahiri idan ka ganta zaka dauka bata da wata damuwa amma a badini ba haka bane, a sannu rashin Khalil yake dukanta kullum cikin zuba idon ganinsa takeyi yazo da niyyar maidata se gashi babu wata alama da take nuna faruwar hakan dan daga shi har yayanta babu wanda ya sake tako qafarsa gidan har gara takan ji a bakin Nuratu ko Maman Asad an kai musu yaran Musamman Nuratu da take nacin su abin ya qara bata mata rai wato ana kaisu gidan yan uwanta se ita da take uwarsu ce ba za'a kai mata su ba duk tsiya dai ba'a isa a canzawa Tuwo suna ba suna nan a matsayin yayanta kuma ko bajima ko ba dade zasu nemeta idan ba'a kawo su ba.

Ba'a cika wata shida data kama ayyukan gida ba kudi suka qare Almajiri ya gudu saboda daman ba abinci ake bashi ba kudi take biyansa yaci wata biyu bata biyashi ba sedai ta hadashi kanzon tukunya tace yayi haquri in ta samu zata biyashi daya gaji ya fece shikenanta sake shiga ukun data fi tada dan yanzu ga aiki ya mata karo ga qangin talauci dan kudin da zata siyi sabulun wanka ma Wahala yake mata a da kuwa duk wata Khalil yana sako mata Shower gel din da take amfani dasu tunda Iman ta bar hannunta kuwa ya janye tallafi a farko bata damu ba dan gani take kamar tana da abinda ze ci gaba da riqeta se yanzu ta gane karin maganar da Hausawa suke cewa Zara bata barin dami tunda gashi sake dawowa square zero.
Chapter 228 · 0% Book details